< Jeremiah 11 >
1 The word that came to Jeremiah from Jehovah, saying,
Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji.
2 Hear ye the words of this covenant, and speak unto the men of Judah, and to the inhabitants of Jerusalem;
“Ka saurari zancen wannan alkawari ka kuma faɗe su ga mutanen Yahuda da kuma waɗanda suke zaune a Urushalima.
3 and say thou unto them, Thus saith Jehovah, the God of Israel: Cursed be the man that heareth not the words of this covenant,
Ka faɗa musu cewa ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa, ‘La’ananne ne wanda bai kula da zancen alkawarin nan ba,
4 which I commanded your fathers in the day that I brought them forth out of the land of Egypt, out of the iron furnace, saying, Obey my voice, and do them, according to all which I command you: so shall ye be my people, and I will be your God;
zancen da na umarci kakanni-kakanninku sa’ad da na fitar da su daga Masar, daga cikin tanderun narkewar ƙarfe.’ Na ce, ‘Ku yi mini biyayya ku kuma aikata kowane abin da na umarce ku, za ku kuwa zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnku.
5 that I may establish the oath which I sware unto your fathers, to give them a land flowing with milk and honey, as at this day. Then answered I, and said, Amen, O Jehovah.
Sa’an nan zan cika rantsuwar da na yi wa kakanni-kakanninku, da zan ba su ƙasa mai zub da madara da kuma zuma’ ƙasar da kuka mallaka a yau.” Sai na amsa na ce, “Amin, Ubangiji.”
6 And Jehovah said unto me, Proclaim all these words in the cities of Judah, and in the streets of Jerusalem, saying, Hear ye the words of this covenant, and do them.
Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka yi shelar dukan maganan nan a biranen Yahuda da titunan Urushalima duka cewa, ‘Su saurari zancen alkawarin nan, su aikata.
7 For I earnestly protested unto your fathers in the day that I brought them up out of the land of Egypt, even unto this day, rising early and protesting, saying, Obey my voice.
Daga lokacin da na fitar da kakanni-kakanninku daga Masar har yă zuwa yau, na gargaɗe su sau da sau, ina cewa, “Ku yi mini biyayya.”
8 Yet they obeyed not, nor inclined their ear, but walked every one in the stubbornness of their evil heart: therefore I brought upon them all the words of this covenant, which I commanded them to do, but they did them not.
Amma ba su kasa kunne ko su saurara ba, a maimako, sai suka bi taurinkai na mugayen zukatansu. Saboda haka na kawo musu dukan la’anonin alkawarin da na riga na umarce su, su bi amma ba su kiyaye ba.’”
9 And Jehovah said unto me, A conspiracy is found among the men of Judah, and among the inhabitants of Jerusalem.
Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Akwai maƙarƙashiya a cikin mutanen Yahuda da waɗanda suke zaune a Urushalima.
10 They are turned back to the iniquities of their forefathers, who refused to hear my words; and they are gone after other gods to serve them: the house of Israel and the house of Judah have broken my covenant which I made with their fathers.
Sun koma ga zunuban kakanni kakanninsu, waɗanda suka ƙi su saurari maganata. Suka bi waɗansu alloli don su bauta musu. Da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda duk sun take alkawarin da na yi da kakanni kakanninsu.
11 Therefore thus saith Jehovah, Behold, I will bring evil upon them, which they shall not be able to escape; and they shall cry unto me, but I will not hearken unto them.
Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan kawo masifa a kansu wadda ba za su iya tsere mata ba. Ko da yake suna kuka gare ni, ba zan saurare su ba.
12 Then shall the cities of Judah and the inhabitants of Jerusalem go and cry unto the gods unto which they offer incense: but they will not save them at all in the time of their trouble.
Garuruwan Yahuda da mutanen Urushalima za su tafi su yi kuka ga allolin da suke ƙona wa turare, amma ba za su taimake su ba sam sa’ad da masifar ta auku.
13 For according to the number of thy cities are thy gods, O Judah; and according to the number of the streets of Jerusalem have ye set up altars to the shameful thing, even altars to burn incense unto Baal.
Kuna da alloli masu yawa yadda kuke da garuruwa, ya Yahuda; kuma bagadan da kuka yi don ƙona turare wa allahn nan Ba’al abin kunya sun yi yawa kamar titunan Urushalima.’
14 Therefore pray not thou for this people, neither lift up cry nor prayer for them; for I will not hear them in the time that they cry unto me because of their trouble.
“Kada ka yi addu’a domin wannan mutane ko ka miƙa wani roƙo ko kuka dominsu, domin ba zan saurara ba sa’ad da suka kira gare ni a lokacin ƙuncinsu.
15 What hath my beloved to do in my house, seeing she hath wrought lewdness [with] many, and the holy flesh is passed from thee? when thou doest evil, then thou rejoicest.
“Mene ne ƙaunatacciyata take yi a haikali da yake ta yin ƙulle-ƙullen mugayen makircinta tare da mutane masu yawa? Tsarkakar nama zai iya kawar da hukuncinki? Sa’ad da kike yin muguntarki sa’an nan ki yi farin ciki.”
16 Jehovah called thy name, A green olive-tree, fair with goodly fruit: with the noise of a great tumult he hath kindled fire upon it, and the branches of it are broken.
Ubangiji ya kira ki itacen zaitun mai inuwa kyakkyawa mai’ya’ya masu kyau. Amma da ƙugin babbar hadari zai cinna masa wuta, rassansa za su kakkarye.
17 For Jehovah of hosts, who planted thee, hath pronounced evil against thee, because of the evil of the house of Israel and of the house of Judah, which they have wrought for themselves in provoking me to anger by offering incense unto Baal.
Ubangiji Maɗaukaki, wanda ya dasa ki, ya furta miki masifa, domin gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda sun aikata mugunta suka kuma tsokane ni in yi fushi ta wurin ƙona wa Ba’al turare.
18 And Jehovah gave me knowledge of it, and I knew it: then thou showedst me their doings.
Domin Ubangiji ya bayyana mini maƙarƙashiyarsu, na santa, gama a wannan lokaci ya nuna mini abin da suke yi.
19 But I was like a gentle lamb that is led to the slaughter; and I knew not that they had devised devices against me, [saying], Let us destroy the tree with the fruit thereof, and let us cut him off from the land of the living, that his name may be no more remembered.
Na kasance kamar ɗan rago marar faɗa wanda aka kai mayanka; ban gane cewa sun ƙulla mini maƙarƙashiya, suna cewa, “Bari mu lalatar da itacen duk da’ya’yansa; bari mu datse shi daga ƙasar masu rai, har da ba za a ƙara tunawa da sunansa ba.”
20 But, O Jehovah of hosts, who judgest righteously, who triest the heart and the mind, I shall see thy vengeance on them; for unto thee have I revealed my cause.
Amma, ya Ubangiji Maɗaukaki, kai da kake yin shari’a da adalci kake gwada zuciya da kuma tunani, ka sa in ga sakayyar da za ka yi musu, gama a gare ka na danƙa maganata.
21 Therefore thus saith Jehovah concerning the men of Anathoth, that seek thy life, saying, Thou shalt not prophesy in the name of Jehovah, that thou die not by our hand;
“Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da mutanen Anatot, waɗanda suke neman ranka suna kuma cewa, ‘Kada ka yi annabci da sunan Ubangiji in ba haka za ka mutu a hannunmu’
22 therefore thus saith Jehovah of hosts, Behold, I will punish them: the young men shall die by the sword; their sons and their daughters shall die by famine;
saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, ‘Zan hukunta su. Samarinsu za su mutu ta wurin takobi,’ya’yansu maza da mata kuwa ta wurin yunwa.
23 and there shall be no remnant unto them: for I will bring evil upon the men of Anathoth, even the year of their visitation.
Babu raguwar da za a bar musu, domin zan kawo masifa a kan mutanen Anatot a shekarar hukuncinsu.’”