< Isaiah 62 >
1 For Zion’s sake will I not hold my peace, and for Jerusalem’s sake I will not rest, until her righteousness go forth as brightness, and her salvation as a lamp that burneth.
Saboda Sihiyona ba zan yi shiru ba, saboda Urushalima ba zan huta ba, sai adalcinta ya haskaka kamar hasken safiya, cetonta kuma ya haskaka kamar fitila mai haske.
2 And the nations shall see thy righteousness, and all kings thy glory, and thou shalt be called by a new name, which the mouth of Jehovah shall name.
Al’ummai za su ga adalcinki, sarakuna kuma za su ga ɗaukakarki; za a kira ki da sabon suna sunan da bakin Ubangiji zai ambata.
3 Thou shalt also be a crown of beauty in the hand of Jehovah, and a royal diadem in the hand of thy God.
Za ki zama rawanin daraja a hannun Ubangiji, rawanin sarauta a hannun Allahnki.
4 Thou shalt no more be termed Forsaken; neither shall thy land any more be termed Desolate: but thou shalt be called Hephzi-bah, and thy land Beulah; for Jehovah delighteth in thee, and thy land shall be married.
Ba za a ƙara ce da ke Yasasshiya ba, ko a kira ƙasarki Kango. Amma za a ce da ke Hefziba ƙasarki kuma Bewula; gama Ubangiji zai ji daɗinki, ƙasarki kuma za tă yi aure.
5 For as a young man marrieth a virgin, so shall thy sons marry thee; and as the bridegroom rejoiceth over the bride, so shall thy God rejoice over thee.
Kamar yadda saurayi kan auri yarinya, haka’ya’yanki maza za su aure ki; kamar kuma yadda ango yakan yi farin ciki da amaryarsa, haka Allahnki zai yi farin ciki da ke.
6 I have set watchmen upon thy walls, O Jerusalem; they shall never hold their peace day nor night: ye that are Jehovah’s remembrancers, take ye no rest,
Na sa matsara a kan katangarki, ya Urushalima; ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Ku da kuke kira bisa sunan Ubangiji, kada ku ba kanku hutu,
7 and give him no rest, till he establish, and till he make Jerusalem a praise in the earth.
kuma kada ku ba shi hutu sai ya kafa Urushalima ya kuma mai da ita yabon duniya.
8 Jehovah hath sworn by his right hand, and by the arm of his strength, Surely I will no more give thy grain to be food for thine enemies; and foreigners shall not drink thy new wine, for which thou hast labored:
Ubangiji ya rantse da hannunsa na dama ta hannunsa kuma mai iko cewa, “Ba zan ƙara ba da hatsinki ya zama abinci ga abokan gābanki ba, baƙi kuma ba za su ƙara shan ruwan inabin wanda kika sha wahala samu ba;
9 but they that have garnered it shall eat it, and praise Jehovah; and they that have gathered it shall drink it in the courts of my sanctuary.
amma waɗanda suka girbe shi za su ci shi su kuma yabi Ubangiji, waɗanda kuma suka tattara’ya’yan inabi za su sha shi a filayen wurina mai tsarki.”
10 Go through, go through the gates; prepare ye the way of the people; cast up, cast up the highway; gather out the stones; lift up an ensign for the peoples.
Ku wuce, ku wuce ƙofofi! Ku shirya hanya saboda mutane. Ku gina, ku gina babbar hanya! Ku kawar da duwatsu. Ku ɗaga tuta saboda al’ummai.
11 Behold, Jehovah hath proclaimed unto the end of the earth, Say ye to the daughter of Zion, Behold, thy salvation cometh; behold, his reward is with him, and his recompense before him.
Ubangiji ya yi shela ga iyakokin duniya cewa, “Faɗa wa Diyar Sihiyona, ‘Ga Mai Cetonki yana zuwa! Ga ladarsa tana tare da shi, sakamakonsa yana raka shi.’”
12 And they shall call them The holy people, The redeemed of Jehovah: and thou shalt be called Sought out, A city not forsaken.
Za a ce da shi Tsattsarkar Mutane, Fansassu na Ubangiji; za a kuma ce da ke Wadda Aka Nema Birnin da Ba Za a Ƙara Yashe ta ba.