< Acts 16 >
1 He came to Derbe and Lystra; and behold, a certain disciple was there, named Timothy, the son of a Jewess who believed, but his father was a Greek.
Bulus ya kai Derbe sa’an nan kuma zuwa Listira, inda wani almajiri mai suna Timoti yake da zama, wanda mahaifiyarsa mutuniyar Yahuda ce kuma mai bi ce, amma mahaifinsa mutumin Hellenawa ne.
2 The brothers who were at Lystra and Iconium gave a good testimony about him.
’Yan’uwa a Listira da Ikoniyum sun yi magana mai kyau ƙwarai a kansa.
3 Paul wanted to have him go out with him, and he took and circumcised him because of the Jews who were in those parts, for they all knew that his father was a Greek.
Bulus ya so ya ɗauke shi a tafiyar, saboda haka ya yi masa kaciya, domin Yahudawan da suke da zama a wurin, don duk sun san cewa mahaifinsa mutumin Hellenawa ne.
4 As they went on their way through the cities, they delivered the decrees to them to keep which had been ordained by the apostles and elders who were at Jerusalem.
Yayinda suke tafiya daga gari zuwa gari, suka dinga ba da shawarwarin da manzanni da dattawa a Urushalima suka zartar domin mutane su kiyaye.
5 So the assemblies were strengthened in the faith, and increased in number daily.
Saboda haka ikkilisiyoyi suka ginu cikin bangaskiya suka kuma yi girma suka yi ta ƙaruwa kowace rana.
6 When they had gone through the region of Phrygia and Galatia, they were forbidden by the Holy Spirit to speak the word in Asia.
Bulus da abokan tafiyarsa suka zazzaga dukan yankin Firjiya da Galatiya, don Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin wa’azi a lardin Asiya.
7 When they had come opposite Mysia, they tried to go into Bithynia, but the Spirit did not allow them.
Da suka isa kan iyakar Misiya, suka yi ƙoƙari su shiga Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai yarda musu ba.
8 Passing by Mysia, they came down to Troas.
Saboda haka suka ratsa Misiya suka zo Toruwas.
9 A vision appeared to Paul in the night. There was a man of Macedonia standing, begging him and saying, “Come over into Macedonia and help us.”
Da dare Bulus ya ga wahayin wani mutumin Makidoniya yana tsaye yana roƙonsa cewa, “Ka zo Makidoniya ka taimake mu.”
10 When he had seen the vision, immediately we sought to go out to Macedonia, concluding that the Lord had called us to preach the Good News to them.
Bayan Bulus ya ga wahayin, muka shirya nan take mu tashi zuwa Makidoniya, mun tabbata cewa, Allah ya kira mu mu yi musu wa’azin bishara.
11 Setting sail therefore from Troas, we made a straight course to Samothrace, and the day following to Neapolis;
Daga Toruwas muka tashi zuwa teku muka kuma shiga jirgin ruwa muka miƙe kai tsaye zuwa Samotiras, kashegari kuma muka nufi Neyafolis.
12 and from there to Philippi, which is a city of Macedonia, the foremost of the district, a Roman colony. We were staying some days in this city.
Daga can muka tafi Filibbi, wata babbar alkaryar Roma wadda kuma take babban birni a gundumar Makidoniya. Muka zauna a can kwanaki masu yawa.
13 On the Sabbath day we went outside of the city by a riverside, where we supposed there was a place of prayer, and we sat down and spoke to the women who had come together.
A Asabbaci, muka fita ƙofar birnin zuwa bakin kogi, inda muke tsammani za mu sami wurin yin addu’a. Muka zauna muka fara yin wa matan da suka taru a can magana.
14 A certain woman named Lydia, a seller of purple, of the city of Thyatira, one who worshiped God, heard us. The Lord opened her heart to listen to the things which were spoken by Paul.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka saurare mu mace ce mai suna Lidiya, mai sayar da yadunan jan garura masu tsada daga birnin Tiyatira, mai yi wa Allah sujada. Ubangiji ya buɗe zuciyarta har ta karɓi saƙon Bulus.
15 When she and her household were baptized, she begged us, saying, “If you have judged me to be faithful to the Lord, come into my house and stay.” So she persuaded us.
Da aka yi mata baftisma tare da iyalin gidanta, sai ta gayyace mu zuwa gidanta. Ta ce, “In kun amince ni mai bi ce cikin Ubangiji, sai ku zo ku sauka a gidana.” Sai ta kuwa rinjaye mu.
16 As we were going to prayer, a certain girl having a spirit of divination met us, who brought her masters much gain by fortune telling.
Wata rana muna tafiya zuwa wurin yin addu’a, sai muka sadu da wata baranya mai ruhun aljani mai duba. Takan samo wa mutanenta kuɗi da yawa, duban da take yi.
17 Following Paul and us, she cried out, “These men are servants of the Most High God, who proclaim to us a way of salvation!”
Wannan yarinya kuwa ta bi Bulus da kuma sauranmu, tana ihu tana cewa, “Waɗannan mutane bayin Allah Mafi Ɗaukaka ne, suna sanar da ku hanyar ceto.”
18 She was doing this for many days. But Paul, becoming greatly annoyed, turned and said to the spirit, “I command you in the name of Jesus Christ to come out of her!” It came out that very hour.
Ta yi ta faɗin haka har kwanaki masu yawa. A ƙarshe Bulus ya damu ƙwarai sai ya juya ya ce wa aljanin, “A cikin sunan Yesu Kiristi na umarce ka, ka rabu da ita!” Nan take aljanin ya rabu da ita.
19 But when her masters saw that the hope of their gain was gone, they seized Paul and Silas and dragged them into the marketplace before the rulers.
Da iyayengijin baranyar suka ga hanyar samun kuɗinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila suka ja su zuwa cikin kasuwa don su fuskanci hukuma.
20 When they had brought them to the magistrates, they said, “These men, being Jews, are agitating our city
Sai suka kawo su a gaban alƙalai suka ce, “Waɗannan Yahudawa ne, suna kuma birkitar mana da gari,
21 and advocate customs which it is not lawful for us to accept or to observe, being Romans.”
ta wurin koyar da al’adun da ba daidai ba ne mu Romawa mu karɓa ko mu aikata.”
22 The multitude rose up together against them and the magistrates tore their clothes from them, then commanded them to be beaten with rods.
Sai taron suka fāɗa wa Bulus da Sila gaba ɗaya, alƙalan kuwa suka yi umarni a tuɓe su a kuma yi musu dūka.
23 When they had laid many stripes on them, they threw them into prison, charging the jailer to keep them safely.
Bayan an yi musu bulala sosai, sai aka jefa su cikin kurkuku, aka umarci mai gadin kurkukun yă tsare su da kyau.
24 Having received such a command, he threw them into the inner prison and secured their feet in the stocks.
Da karɓan irin umarnan nan, sai ya sa su can cikin ɗakin kurkuku na ciki-ciki, kuma ya ɗaura ƙafafunsu a turu.
25 But about midnight Paul and Silas were praying and singing hymns to God, and the prisoners were listening to them.
Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran’yan kurkuku kuwa suna sauraronsu.
26 Suddenly there was a great earthquake, so that the foundations of the prison were shaken; and immediately all the doors were opened, and everyone’s bonds were loosened.
Ba zato ba tsammani sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa har tushen ginin kurkukun ya jijjiga. Nan da nan sai duk ƙofofin kurkukun suka bubbuɗe, sarƙoƙin kowa kuma suka ɓaɓɓalle.
27 The jailer, being roused out of sleep and seeing the prison doors open, drew his sword and was about to kill himself, supposing that the prisoners had escaped.
Mai gadin kurkukun ya farka daga barci, sa’ad da ya ga ƙofofin kurkukun a buɗe, sai ya zāre takobinsa yana shirin kashe kansa domin ya ɗauka’yan kurkukun sun gudu.
28 But Paul cried with a loud voice, saying, “Do not harm yourself, for we are all here!”
Amma Bulus ya yi ihu ya ce, “Kada ka yi wa kanka lahani! Dukanmu muna nan!”
29 He called for lights, sprang in, fell down trembling before Paul and Silas,
Mai gadin kurkukun ya kira a kawo fitilu, ya ruga ciki ya fāɗi yana rawan jiki a gaban Bulus da Sila.
30 brought them out, and said, “Sirs, what must I do to be saved?”
Sai ya fito da su waje ya kuma tambaye su ya ce, “Ranku yă daɗe, me zan yi domin in sami ceto?”
31 They said, “Believe in the Lord Jesus Christ, and you will be saved, you and your household.”
Suka amsa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka.”
32 They spoke the word of the Lord to him, and to all who were in his house.
Sa’an nan suka yi masa maganar Ubangiji shi da kuma dukan sauran da suke a gidansa.
33 He took them the same hour of the night and washed their stripes, and was immediately baptized, he and all his household.
A wannan sa’a na daren, mai gadin kurkukun ya ɗauke su ya wanke musu raunukansu; nan take aka yi masa baftisma da dukan iyalinsa.
34 He brought them up into his house and set food before them, and rejoiced greatly with all his household, having believed in God.
Sai mai gadin kurkukun ya kawo su cikin gidansa ya ba su abinci; ya kuwa cika da murna don yă gaskata da Allah, shi da dukan iyalinsa.
35 But when it was day, the magistrates sent the sergeants, saying, “Let those men go.”
Da gari ya waye, sai alƙalan suka aika ma’aikatansu wajen mai gadin kurkukun da umarni cewa, “Ka saki mutanen nan.”
36 The jailer reported these words to Paul, saying, “The magistrates have sent to let you go; now therefore come out and go in peace.”
Sai mai gadin kurkukun ya gaya wa Bulus cewa, “Alƙalai sun ba da umarni a sake ku kai da Sila. Yanzu sai ku tafi. Ku sauka lafiya.”
37 But Paul said to them, “They have beaten us publicly without a trial, men who are Romans, and have cast us into prison! Do they now release us secretly? No, most certainly, but let them come themselves and bring us out!”
Amma Bulus ya ce wa ma’aikatan, “Sun yi mana dūka a fili ba tare da shari’a ba, ko da yake mu’yan ƙasar Roma ne, suka kuma jefa mu cikin kurkuku. Yanzu suna so su fitar da mu a ɓoye? A’a! Sai dai su zo da kansu su rako mu waje.”
38 The sergeants reported these words to the magistrates, and they were afraid when they heard that they were Romans,
Sai ma’aikatan suka faɗa wa alƙalan wannan, da suka ji cewa Bulus da Sila Romawa ne, sai suka ji tsoro.
39 and they came and begged them. When they had brought them out, they asked them to depart from the city.
Sai suka zo don su roƙe su, suka yi musu rakiya daga kurkukun, suna roƙonsu su bar birnin.
40 They went out of the prison and entered into Lydia’s house. When they had seen the brothers, they encouraged them, then departed.
Bayan Bulus da Sila suka fita daga kurkukun, sai suka tafi gidan Lidiya, inda suka sadu da’yan’uwa suka kuma ƙarfafa su. Sa’an nan suka tafi.