< Numbers 12 >
1 And Miriam and Aaron spoke against Moses because of the Cushite woman whom he had married, for he had married a Cushite woman.
Miriyam da Haruna suka fara zargin Musa saboda matarsa’yar ƙasar Kush da ya aura.
2 And they said, Has Jehovah indeed spoken only with Moses? Has he not spoken also with us? And Jehovah heard it.
Suka ce, “Ubangiji ya yi magana ta wurin Musa ne kaɗai? Ashe, bai yi magana ta wurinmu mu ma ba?” Ubangiji kuwa ya ji wannan.
3 Now the man Moses was very meek, above all the men who were upon the face of the earth.
(Musa kuwa mutum ne mai tawali’u ƙwarai, mafi tawali’u fiye da kowane mutum a duniya.)
4 And Jehovah spoke suddenly to Moses, and to Aaron, and to Miriam, Come out ye three to the tent of meeting. And the three came out.
Nan da nan Ubangiji ya ce wa Musa, da Haruna da kuma Miriyam, “Ku fita ku tafi Tentin Sujada, dukanku uku.” Sai dukansu uku suka tafi.
5 And Jehovah came down in a pillar of cloud, and stood at the door of the tent, and called Aaron and Miriam. And they both came forth.
Sai Ubangiji ya sauko a cikin ginshiƙin girgije; ya tsaya a bakin ƙofar Tenti, ya kira Haruna da Miriyam. Sa’ad da su biyu suka gusa gaba,
6 And he said, Hear now my words. If there be a prophet among you, I Jehovah will make myself known to him in a vision. I will speak with him in a dream.
sai ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa, “Duk lokacin da akwai annabin Ubangiji a cikinku, nakan bayyana kaina gare shi cikin wahayi, in yi magana da shi cikin mafarkai.
7 My servant Moses is not so. He is faithful in all my house.
Amma ba haka nake magana da Musa bawana ba; na sa shi yă lura da dukan jama’ata Isra’ila.
8 With him I will speak mouth to mouth, even manifestly, and not in dark speeches, and he has beheld the form of Jehovah. Why then were ye not afraid to speak against my servant, against Moses?
Da shi nake magana fuska da fuska, a fili kuma, ba a kacici-kacici ba; yakan ga siffar Ubangiji. To, me ya sa ba ku ji tsoro ku yi magana a kan bawana Musa ba?”
9 And the anger of Jehovah was kindled against them, and he departed.
Sai fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kansu, ya kuma rabu da su.
10 And the cloud removed from over the tent. And, behold, Miriam was leprous, as snow. And Aaron looked upon Miriam, and, behold, she was leprous.
Da girgijen ya tashi daga bisa Tentin, sai ga Miriyam tsaye, kuturwa, fari fat. Haruna kuwa ya juya wajenta ya ga ta kuturce;
11 And Aaron said to Moses, Oh, my lord, lay not, I pray thee, sin upon us, in which we have done foolishly, and in which we have sinned.
sai Haruna ya ce wa Musa, “Ranka yă daɗe, ina roƙonka kada ka hukunta mu, gama zunubin da muka yi, mun yi ne cikin wauta.
12 Let her not, I pray, be as one dead, of whom the flesh is half consumed when he comes out of his mother's womb.
Kada ka sa ta zama kamar haifaffen mataccen jariri daga cikin mahaifiya wanda rabin jikin ruɓaɓɓe ne.”
13 And Moses cried to Jehovah, saying, Heal her, O God, I beseech thee.
Saboda haka sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Allah, ina roƙonka ka warkar da ita!”
14 And Jehovah said to Moses, If her father had but spit in her face, should she not be ashamed seven days? Let her be shut up outside the camp seven days, and after that she shall be brought in again.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Da a ce mahaifinta ne ya tofa mata miyau a fuskarta, ashe, ba za tă ji kunya har kwana bakwai ba? A fitar da ita bayan sansani kwana bakwai; bayan haka za a iya dawo da ita.”
15 And Miriam was shut up outside the camp seven days. And the people journeyed not till Miriam was brought in again.
Haka aka fitar da Miriyam bayan sansani kwana bakwai, mutane kuwa ba su ci gaba da tafiya ba sai da aka dawo da ita.
16 And afterward the people journeyed from Hazeroth, and encamped in the wilderness of Paran.
Bayan haka sai mutane suka bar Hazerot suka sauka a Hamadan Faran.