< Galatians 2 >
1 Then after fourteen years I went up again to Jerusalem with Barnabas, having taken along Titus also.
Daga nan, bayan shekara goma sha hudu na koma Urushalima tare da Barnaba. Na kuma dauki Titus tare da ni.
2 And I went up according to revelation, and I declared to them the good news that I preach among the Gentiles, but privately to those who were of repute, lest somehow I might be running or ran in vain.
Na koma ne domin Allah ya nuna mani in koma. Sai na gabatar masu shelar bisharan da nake yi a cikin al'ummai. (Amma a kebe na yi magana da wadanda aka dauka muhimman shugabanni). Na yi haka ne domin in tabbatar da cewa ba gudun banza nake yi ba, ko kuma na yi gudun banza.
3 But not even Titus with me, being a Greek, was compelled to be circumcised.
Amma ko Titus wanda yake tare da ni, Baheline, ba wanda ya tilasta masa ya yi kaciya.
4 But that issue was because of those false brothers smuggled in, who sneaked in to spy out our liberty that we have in Christ Jesus, so that they might enslave us,
Wannan maganar ta taso ne daga 'yan'uwan karya da suka zo cikinmu a boye su ga 'yancin mu a cikin Yesu Almsihu. Sun yi marmarin su maishe mu bayi ga doka.
5 to whom we yielded in subjection not even for an hour, so that the truth of the good news might continue with you.
Ba mu mika kanmu biyayya gare su ba ko da na sa'a daya, domin gaskiyar bishara ta kasance babu canzawa domin ku.
6 But from those who were reputed to be something (what kind they were formerly, it makes no difference to me, God does not accept a personage of man), for those who were of repute added nothing to me,
Amma su wadanda a ke ganin su da muhimmanci ba su taimaka mani da komai ba. Ko su wanene su bai dame ni ba. Allah ba ya karbar wanda mutane suka fi so.
7 but to the contrary, when they saw that I was entrusted with the good news for men of uncircumcision, as Peter for men of circumcision
Maimakon haka, suka ga an danka mani shelar bishara ga wadanda ba su da kaciya. Kamar yadda aka ba Bitrus shelar bishara ga masu kaciya.
8 (for he who was working in Peter for the apostleship for men of circumcision was also working in me for the Gentiles),
Gama Allah wanda yake yin aiki a cikin Bitrus domin manzanci zuwa ga masu kaciya, haka kuma yake aiki ciki na zuwa ga al'ummai.
9 and James and Cephas and John, those who were reputed to be pillars, when they understood the grace that was given to me, they gave to me and Barnabas the right hands of fellowship. So that we were for the Gentiles, and they for men of circumcision,
Da Yakubu, Kefas, da Yahaya, wadanda a ke gani masu gina ikilisiya, suka fahimci alherin da aka ba ni, suka bamu hannun dama na zumunci ni da Barnaba, Sun yi haka ne kawai domin mu mu tafi zuwa wurin al'ummai, su kuma su je wurin masu kaciya.
10 only that we should remember the poor, which this same thing I also was eager to do.
Suna kuma so mu tuna da matalauta. Ni ma ina da aniyar yin haka.
11 But when Peter came to Antioch I opposed him to the face, because he was blameworthy.
Da Kefas ya kai Antakiya, na yi tsayayya da shi a gabansa domin shine ke da kuskure.
12 For before certain men came from James he ate together with the Gentiles, but when they came, he withdrew and separated himself, fearing men of circumcision.
Da ma Kefas yana cin abinci tare da al'ummai kafin zuwan wasu mutane daga wurin Yakubu. Amma da wadannan mutane suka iso, sai ya dena kuma ya ware kansa daga al'umman. Yana jin tsoron wadannan mutanen da ke bukatar kaciya.
13 And the other Jews also joined in hypocrisy with him, so that even Barnabas went along with their hypocrisy.
Hakannan ma sauran Yahudawa da suke tare da shi sun bi munafurcin sa. A sakamakon haka Barnaba ma ya bi munafurcin su.
14 But when I saw that they did not walk uprightly toward the truth of the good news, I said to Peter before all, If thou being a Jew, live as a Gentile and not as a Jew, why do thou compel the Gentiles to live as Jews?
Da na ga basu bin gaskiyar da take cikin bisharar, na gaya wa Kefas a gaban su duka, “Idan kai Bayahude ne kana rayuwar ka ta al'ummai a maimakon rayuwar Yahudawa, to ta yaya za ka tilasta wa al'ummai su yi zaman Yahudawa? “
15 We are Jews by nature and not sinful men of the Gentiles,
Mu da muke Yahudawa daga haihuwa, ba ''Al'ummai masu zunubi ba.''
16 knowing that a man is not made righteous from works of law, instead through faith of Jesus Christ. And we believed in Christ Jesus, so that we might be made righteous from faith of Christ, and not from works of law, because no flesh will be made righteous from works of law.
Ku sani fa, babu wanda za a baratar ta ayyukan shari'a. A maimakon haka an baratar da su ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu. Mun zo ga cikin Almasihu Yesu domin mu samu baratarwa ta bangaskiya cikin Almasihu, kuma ba ta ayyukan shari'a ba. Domin ta ayyukan shari'a babu wanda zai samu baratarwa.
17 But if, while seeking to be made righteous in Christ, we ourselves were also found sinful, then is Christ an aide of sin? May it not happen!
Amma idan mun nemi Allah ya baratar da mu cikin Almasihu, mun samu kanmu masu zunubi kenan, Almasihu ya zama bawan zunubi ne? Ko kadan!
18 For if I build again these things that I tore down, I demonstrate myself a transgressor.
Idan na sake gina dogara ta a kan shari'a, dogarar da na juya wa baya, na nuna kai na mai karya shari'a kenan.
19 For I, through law, died to law, so that I might live to God.
Ta wurin shari'a na mutu ga shari'a, domin in yi rayuwa irin ta Allah.
20 I have been crucified with Christ, and I no longer live, but Christ lives in me. And what I now live in flesh I live by the faith of the Son of God who loved me and gave himself up for me.
An giciye ni tare da Almasihu, ba nine ke rayuwa ba kuma, amma Almasihu ke rayuwa a cikina. Rayuwar da nake yi a yanzu a cikin jiki, ina yin ta ne, ta wurin bangaskiya ga dan Allah, wanda ya kaunace ni ya ba da kansa domina.
21 I do not disregard the grace of God, for if righteousness is through law, then Christ died in vain.
Ban yi watsi da alherin Allah ba, domin idan adalci ya wanzu ta wurin shari'a, ashe Almasihu ya mutu a banza kenan.