< 1 Corinthians 2 >
1 And I, brothers, when I came to you, came not in eminence of speech or of wisdom proclaiming the testimony of God to you.
Da na zo wurinku’yan’uwa, ban zo da iya magana ko wani mafificin hikima yayinda na yi muku shelar shaida game da Allah ba.
2 For I determined not to know anything among you except Jesus Christ, even this crucified man.
Don na ƙudura a raina sa’ad da nake tare da ku cewa ba zan mai da hankali ga kome ba sai dai Yesu Kiristi wanda aka gicciye.
3 And I was with you in weakness, and in fear, and in much trembling.
Na zo wurinku cikin rashin ƙarfi da tsoro, da rawan jiki ƙwarai.
4 And my speech and my preaching were not in persuasive words of human wisdom, but in demonstration of the Spirit and of power,
Saƙona da wa’azina ba su zo cikin hikima da kalmomin lallashi ba, sai dai da nuna ikon Ruhu,
5 so that your faith would not be in wisdom of men, but in the power of God.
domin kada bangaskiyarku ta dogara a kan hikimar mutane, sai dai a kan ikon Allah.
6 But we speak wisdom among the fully developed, but not a wisdom of this age, nor of the rulers of this age who come to nothing. (aiōn )
Duk da haka, muna sanar da saƙon hikima cikin waɗanda suka balaga, amma ba hikima irin ta wannan zamani ba ne, ko kuwa irin ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda za su shuɗe ba. (aiōn )
7 But we speak a wisdom of God in a hidden mystery, which God predestined before the ages for our glory, (aiōn )
A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai. (aiōn )
8 which none of the rulers of this age have known. For if they had known, they would not have crucified the Lord of glory. (aiōn )
Ba ko ɗaya daga cikin masu mulkin wannan zamani da ya fahimce ta, gama da a ce sun fahimce ta, da ba su gicciye Ubangiji mai ɗaukaka ba. (aiōn )
9 But as it is written, What an eye has not seen, and an ear has not heard, and have not arisen in a heart of a man, are things that God prepared for those who love him.
Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ba idon da ya taɓa gani, ba kunnen da ya taɓa ji, ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.”
10 But God disclosed it to us through his Spirit, for the Spirit searches all things, even the deep things of God.
Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa. Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah.
11 For what man knows the things of the man, except the spirit of the man in him? And so nobody knows the things of God except the Spirit of God.
Wane ne a cikin mutane ya san tunanin mutum, in ba ruhun mutumin da yake cikinsa ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah.
12 But we did not receive the spirit of the world, but the Spirit from God, so that we might know the things graciously given to us by God.
Ba mu karɓi ruhun duniya ba, sai dai Ruhun da yake daga Allah, domin mu fahimci abin da Allah ya ba mu hannu sake.
13 Which things also we speak, not in things learned from mankind, in words of wisdom, but in things learned from the Holy Spirit, comparing spiritual things with spiritual things.
Wannan shi ne abin da muke sanarwa, ba da kalmomin da muka koya ta wurin hikimar mutum ba, amma da kalmomin da Ruhu yake koyarwa, muna faɗin gaskiya ta ruhaniya da kalmomin ruhaniya.
14 Now the natural man does not accept the things of the Spirit of God, for they are foolishness to him, and he is unable to understand because they are evaluated spiritually.
Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu.
15 But truly the spiritual man evaluates all things, but he himself is evaluated by none.
Mutumin ruhaniya yakan gwada dukan abubuwa, amma shi kansa ba ya ƙarƙashin shari’ar mutum.
16 For who has known the mind of the Lord that he will stand with him? But we have the mind of Christ.
“Wa ya taɓa sanin hankalin Ubangiji, har da zai koya masa?” Amma muna da tunani iri na Kiristi ne.