< 1 Chronicles 10 >

1 Now the Philistines fought against Israel. And the men of Israel fled from before the Philistines, and fell down slain in mount Gilboa.
To, fa, Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra’ilawa; Isra’ilawa kuwa suka gudu a gabansu, da yawa kuma suka mutu a kan Dutsen Gilbowa.
2 And the Philistines followed hard after Saul and after his sons. And the Philistines killed Jonathan, and Abinadab, and Malchi-shua, the sons of Saul.
Filistiyawa suka matsa sosai suna bin Shawulu da’ya’yansa maza, suka kuma kashe’ya’yansa maza Yonatan, Abinadab da Malki-Shuwa.
3 And the battle went hard against Saul, and the archers overtook him. And he was wounded because of the archers.
Yaƙin ya yi tsanani kewaye da Shawulu, kuma sa’ad da maharba suka rutsa shi, sai suka ji masa rauni.
4 Then Saul said to his armor bearer, Draw thy sword, and thrust me through therewith, lest these uncircumcised come and abuse me. But his armor bearer would not, for he was very afraid. Therefore Saul took his sword, and fell upon it.
Sai Shawulu ya ce wa mai riƙe masa kayan yaƙi, “Zare takobinka ka soke ni, in ba haka ba waɗannan marasa kaciya za su zo su yi mini ba’a.” Amma mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ji tsoro bai kuwa yi haka ba; saboda haka Shawulu ya zāre takobinsa ya fāɗi a kansa.
5 And when his armor bearer saw that Saul was dead, he likewise fell upon his sword, and died.
Da mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ga Shawulu ya mutu, sai shi ma ya fāɗi a kan takobinsa ya mutu.
6 So Saul died, and his three sons. And all his house died together.
Ta haka Shawulu da’ya’yansa maza uku suka mutu, dukan gidansa kuwa suka mutu tare.
7 And when all the men of Israel who were in the valley saw that they fled, and that Saul and his sons were dead, they forsook their cities, and fled. And the Philistines came and dwelt in them.
Sa’ad da dukan Isra’ilawa a cikin kwari suka ga cewa mayaƙansu suna gudu, kuma cewa Shawulu da’ya’yansa maza sun mutu, sai suka bar garuruwansu suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu.
8 And it came to pass on the morrow, when the Philistines came to strip the slain, that they found Saul and his sons fallen in mount Gilboa.
Kashegari, da Filistiyawa suka zo don su tuttuɓe waɗanda suka mutu, sai suka sami Shawulu da’ya’yansa maza sun mutu a Dutsen Gilbowa.
9 And they stripped him, and took his head, and his armor, and sent into the land of the Philistines round about to carry the news to their idols, and to the people.
Suka tuttuɓe shi suka yanke kansa suka ɗauka duk da kayan yaƙinsa, suka kuma aika’yan aika ko’ina a ƙasar Filistiyawa, a yi shela labarin a cikin gumakansu da kuma mutanensu.
10 And they put his armor in the house of their gods, and fastened his head in the house of Dagon.
Suka sa kayan yaƙinsa a haikalin allahnsu suka kuma rataye kansa a haikalin Dagon.
11 And when all Jabesh-gilead heard all that the Philistines had done to Saul,
Sa’ad da mazaunan Yabesh Gileyad suka ji dukan abin da Filistiyawa suka yi wa Shawulu,
12 all the valiant men arose, and took away the body of Saul, and the bodies of his sons, and brought them to Jabesh, and buried their bones under the oak in Jabesh, and fasted seven days.
sai dukan jarumawa suka tafi suka ɗauki jikunan Shawulu da na’ya’yansa maza suka kawo Yabesh. Sa’an nan suka binne ƙasusuwan a ƙarƙashin babban itace oak a Yabesh, suka kuma yi azumi kwana bakwai.
13 So Saul died for his trespass which he committed against Jehovah, because of the word of Jehovah, which he did not keep, and also because he asked counsel of a spiritist, to inquire thereby,
Shawulu ya mutu domin rashin aminci ga Ubangiji; bai kiyaye maganar Ubangiji ba, ya ma nemi shawarar mace mai duba,
14 and did not inquire of Jehovah. Therefore he killed him, and turned the kingdom to David the son of Jesse.
bai kuwa nemi nufin Ubangiji ba. Saboda haka Ubangiji ya kashe shi, ya miƙa mulkin ga Dawuda ɗan Yesse.

< 1 Chronicles 10 >