< Mattheüs 9 >
1 En Hij steeg in de boot, voer over, en kwam in zijn woonplaats aan.
Yesu ya shiga jirgi ya haye ya je birninsa.
2 En zie, men bracht Hem een lamme, die op een bed was gelegd. Toen Jesus hun geloof zag, sprak Hij tot den lamme: Wees welgemoed, mijn zoon; uw zonden zijn u vergeven.
Sai gashi, sun kawo masa wani mutum shanyayye kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, ''Da, ka yi farin ciki. An gafarta maka zunuban ka.''
3 En zie, enige schriftgeleerden zeiden bij zichzelf: Hij lastert God.
Sai wadansu marubuta suka ce a tsakaninsu, ''Wannan mutum sabo yake yi.''
4 Maar Jesus kende hun gedachten, en sprak: Waarom denkt gij kwaad in uw harten?
Yesu kuwa da yake ya san tunaninsu, yace, ''Don me kuke mugun tunani a zuciyarku?
5 Wat is gemakkelijker te zeggen: De zonden zijn u vergeven; of: Sta op en wandel?
Wanne ya fi sauki, a ce, 'An gafarta maka zunubanka,' ko kuwa a ce, 'Tashi ka yi tafiya'?
6 Welnu, opdat gij moogt weten, dat de Mensenzoon macht heeft op aarde, om zonde te vergeven, (hier sprak Hij tot den lamme: ) sta op, neem uw bed, en ga naar huis.
Amma domin ku sani Dan mutum yana da ikon gafarta zunubai a duniya...'' Sai ya ce wa shanyayyen, ''Tashi, ka dauki shimfidarka ka tafi gida.''
7 En hij stond op, en ging naar huis.
Mutumin kuwa ya tashi ya tafi gida.
8 De menigte, die het zag, werd door vrees bevangen, en verheerlijkte God, die zulk een macht aan de mensen gaf.
Da taron suka ga haka sai suka yi mamaki, suka daukaka Allah, wanda ya ba mutane irin wannan iko.
9 Toen Jesus vandaar verder ging, zag Hij een man, Matteüs genaamd, bij het tolhuis zitten. Hij zeide tot hem: Volg Mij. En hij stond op, en volgde Hem.
Da Yesu ya yi gaba, ya ga wani mutum mai suna Matiyu a zaune, yana aiki a wurin karbar haraji. Yace masa, ''Ka biyo ni.'' Ya tashi ya bi shi.
10 En zie, terwijl Jesus in het huis aan tafel aanlag, kwamen vele tollenaars en zondaars met Hem en zijn leerlingen aanliggen.
Sa'adda kuma Yesu yake cin abinci a gida, sai ga masu karbar haraji da masu zunubi da yawa sun zo, sun zauna tare da shi da almajiransa.
11 Toen de farizeën dit zagen, zeiden ze tot zijn leerlingen: Waarom eet uw Meester met tollenaars en zondaars?
Da Farisawa suka ga haka, sai suka ce wa almajiransa, ''Don me malamin ku ya ke ci tare da masu karbar haraji da masu zunubi?''
12 Jesus hoorde het, en sprak: De gezonden hebben geen geneesheer nodig, wel de zieken.
Amma da Yesu ya ji haka ya ce, ''Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya.
13 Gaat, en leert wat het zeggen wil: "Barmhartigheid wil Ik, en geen offerande." Ik ben niet gekomen, om de rechtvaardigen, maar om de zondaars te roepen.
Sai ku fahimci ma'anar wannan tukuna, 'Ni kam, ina bukatar jinkai ba hadaya ba.' Ba domin in kira masu adalci su tuba na zo ba, sai dai masu zunubi.
14 Nu kwamen de leerlingen van Johannes naar Hem toe, en zeiden: Waarom vasten wij en de farizeën, en vasten uw leerlingen niet?
Sai almajiran Yahaya suka zo wurinsa, suka ce, ''Don me mu da Farisawa mu kan yi azumi a kai a kai, amma naka almajiran ba su yi?''
15 Jesus sprak tot hen: Kunnen de bruiloftsgasten treuren, zolang de bruidegom bij hen is? Maar de dagen zullen komen, dat de bruidegom van hen wordt weggenomen; dan zullen ze vasten.
Sai Yesu ya ce masu, ''Masu hidimar buki za su yi bakin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a dauke masu angon. A sa'annan ne fa za su yi azumi.''
16 Niemand zet een lap nieuw laken op een oud kleed; want de opgezette lap trekt het kleed uiteen, en er ontstaat nog groter scheur.
Babu mutumin da zai sa sabon kyalle a kan tsohuwar tufa, domin kyallen zai yage daga tufar, har ma yagewar ta fi ta da.
17 Ook doet men geen nieuwe wijn in oude zakken; anders bersten de zakken, de wijn loopt weg, en de zakken gaan verloren. Maar nieuwe wijn doet men in nieuwe zakken; dan blijven beide behouden.
Mutane kuma ba su dura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. Idan sun yi haka, sai salkunan kuma su fashe inabin ya tsiyaye, sai salkunan su lalace. A maimakon haka, ana sa sabon inabi cikin sababbin salkuna, ta haka an tsirar da duka biyun kenan.''
18 Terwijl Hij zo tot hen sprak, zie, daar kwam een overste naar Hem toe, wierp zich voor Hem neer, en zeide: Heer, zo juist is mijn dochter gestorven; maar kom, leg haar de hand op, en ze zal leven.
Yesu kuwa yana cikin yi masu magana sai ga wani shugaban jama'a ya zo ya yi masa sujada, ya ce, ''Yanzun nan 'yata ta rasu, amma ka zo ka dora mata hannu, za ta rayu.''
19 Jesus stond op, en volgde hem met zijn leerlingen.
Sai Yesu ya tashi ya bi shi tare da almajiransa.
20 En zie, een vrouw, die twaalf jaar lang aan een bloedvloeiing leed, trad achter Hem aan, en raakte de zoom van zijn kleed aan.
Sai ga kuma wata mace wadda ta yi shakaru goma sha biyu tana zubar da jini sosai, ta rabo ta bayan Yesu, ta taba gezar mayafinsa.
21 Want ze zei bij zichzelf: Als ik alleen maar zijn kleed aanraak, ben ik genezen.
Domin ta ce a ran ta, ''Ko da mayafinsa ma na taba, sai in warke.''
22 Jesus keerde Zich om, zag haar, en sprak: Wees welgemoed, mijn dochter; uw geloof heeft u gered. Van dat ogenblik af was de vrouw genezen.
Sai Yesu ya juya, ya gan ta ya ce, '''Yata, ki karfafa. Bangaskiyarki ta warkar da ke.'' Nan take matar ta warke.
23 En toen Jesus in het huis van den overste kwam, en de fluitspelers zag en het luidruchtige volk, zeide Hij:
Da Yesu ya isa gidan shugaban jama'ar, ya kuma ga masu busar sarewa da taro suna ta hayaniya sosai.
24 Gaat heen; want het meisje is niet dood, maar het slaapt. Men lachte Hem uit.
Sai ya ce, ''Ku ba da wuri, ai, yarinyar ba matacciya take ba, barci ta ke yi.'' Sai suka yi masa dariyar raini.
25 Nadat de menigte verwijderd was. trad Hij binnen, en vatte haar bij de hand. En het meisje stond op.
Sa'adda aka fitar da taron waje, ya shiga ya kama hannunta, sai kuwa yarinyar ta shi.
26 De roep hierover verspreidde zich door heel die streek.
Labarin kuwa ya bazu a duk yankin.
27 Toen Jesus vandaar verder ging, volgden Hem twee blinden, die riepen: Heb medelijden met ons, Zoon van David.
Da Yesu ya yi gaba daga nan, sai wadansu makafi biyu suka bi shi, suna daga murya suna cewa, ''Ya Dan Dauda, ka ji tausayinmu.''
28 En toen Hij thuis was gekomen, kwamen de blinden naar Hem toe, en Jesus sprak tot hen: Gelooft gij, dat Ik het doen kan? Ze zeiden: Ja, Heer.
Da Yesu ya shiga wani gida sai makafin suka zo gareshi. Yesu ya ce masu, “Kun gaskata ina da ikon yin haka?'' Sai suka ce masa. ''I, ya Ubangiji.''
29 Nu raakte Hij hun ogen aan, en sprak: U geschiede naar uw geloof.
Sai Yesu ya taba idanunsu, ya ce, ''Ya zama maku gwargwadon bangaskiyarku.''
30 En hun ogen werden geopend. Jesus gebood hun ten strengste: Let er op, dat niemand het te weten komt.
Sai idanunsu suka bude. Amma Yesu ya umarce su kwarai, ya ce, ''Kada fa kowa ya ji labarin nan.''
31 Maar zodra ze waren heengegaan, maakten ze Hem bekend in heel die streek.
Amma suka tafi suka yi ta baza labarinsa a duk yankin.
32 Terwijl ze weggingen, zie, daar bracht men Hem een stomme, die bezeten was.
Da makafin biyu suka tafi, sai aka kawo wa Yesu wani bebe mai aljani.
33 En toen de duivel was uitgedreven, begon de stomme te spreken. De menigte stond verbaasd, en zeide: Zo iets is nog nooit in Israël gezien.
Bayan da an fitar da aljanin, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki, su ka ce, ''Kai, ba a taba ganin irin wannan a cikin Isra'ila ba!''
34 Maar de farizeën zeiden: Door den vorst der duivels drijft Hij de duivels uit.
Amma sai Farisawa suka ce, ''Ai, da ikon sarkin aljanu ya ke fitar da aljanu.''
35 Nu trok Jesus alle steden en dorpen rond, leerde in hun synagogen, preekte het Evangelie van het rijk, en genas alle ziekten en kwalen.
Sai Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da kauyuka, yana koyarwa a majami'unsu, yana yin bisharar mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
36 Bij het zien van de scharen had Hij medelijden met hen; want ze waren uitgeput, en lagen daar als schapen zonder herder.
Amma da ya ga taro masu yawa sai ya ji tausayinsu, domin suna shan wahala kuma sun karaya. Suna nan kamar tumaki da babu makiyayi.
37 Toen zei Hij tot zijn leerlingen: De oogst is groot, maar werklieden zijn er weinig.
Sai ya ce wa almajiransa, ''Girbin yana da yawa, amma ma'aikatan kadan ne.
38 Vraagt dus den Heer van de oogst, dat Hij werklieden zendt in zijn oogst.
Saboda haka sai ku yi sauri ku roki Ubangijin girbin ya turo ma'aikata cikin girbinsa.''