< Salme 62 >

1 (Til sangmesteren. Til Jedutun. En salme af David.) Min Sjæl er Stille for Gud alene, min Frelse kommer fra ham;
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zaburar Dawuda. Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai; cetona na zuwa daga gare shi.
2 ja, han er min Klippe, min Frelse, mit Værn, jeg skal ikke rokkes meget.
Shi kaɗai ne dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.
3 Hvor længe stormer I løs på en Mand, - alle slår I ham ned - som på en hældende Væg, en faldende Mur?
Har yaushe za ku tasar wa mutum guda? Dukanku ne za ku kā da shi wannan jinganannen bango, wannan rusasshen katanga?
4 Ja, de oplægger Råd om at styrte ham fra hans Højhed. De elsker Løgn, velsigner med Munden, men forbander i deres Indre. (Sela)
Sun kintsa sosai su tumɓuke shi daga matsayinsa mai martaba; suna jin daɗi yin ƙarairayi. Sukan sa wa mutum albarka da bakinsu, amma a zuciyarsu la’antawa suke yi. (Sela)
5 Vær stille hos Gud alene, min Sjæl, thi fra ham kommer mit Håb;
Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai; dogarata kan zo daga gare shi ne.
6 ja, han er min Klippe, min Frelse, mit Værn, jeg skal ikke rokkes.
Shi ne kaɗai dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.
7 Hos Gud er min Hjælp og min Ære, min stærke Klippe, min Tilflugt har jeg i Gud;
Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne, shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata.
8 stol på ham, al Folkets Forsamling, udøs for ham eders Hjerte, Gud er vor Tilflugt. (Sela)
Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane; ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi, gama Allah ne mafakarmu. (Sela)
9 Kun Tomhed er Mennesker, Mænd en Løgn, på Vægtskålen vipper de op, de er Tomhed til Hobe.
Talakawa dai kamar shaƙar iska suke, Attajirai dai kamar shirim suke; in aka auna a ma’auni, su ba wani abu ba ne; dukansu dai kamar shaƙar iska ne kawai.
10 Forlad eder ikke på vold, lad jer ikke blænde af Ran; om Rigdommen vokser, agt ikke derpå!
Kada ku dogara a kan ƙwace ko yin fariya a kayan sata; ko arzikinku ya ƙaru, kada ku sa zuciyarku a kansu.
11 Een Gang talede Gud, to Gange hørte jeg det: at Magten er Guds,
Abu guda Allah ya ce, abubuwa biyu na ji, “Cewa kai, ya Allah, kake mai ƙarfi,
12 Og Miskundhed er hos dig, o Herre. Thi enhver gengælder du efter hans Gerning.
kuma cewa kai, ya Ubangiji, mai ƙauna ne. Tabbatacce za ka sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya yi.”

< Salme 62 >