< Filipperne 3 >

1 I øvrigt, mine Brødre glæder eder i Herren! At skrive det samme til eder er ikke til Besvær for mig, men er betryggende for eder.
A karshe, 'yan'uwana, ku yi farin ciki cikin Ubangiji. In sake rubuta maku wadannan abubuwa ba wani abu mai nauyi ba ne a gare ni. Wadannan abubuwa zasu tsare ku.
2 Holder Øje med Hundene, holder Øje med de slette Arbejdere, holder Øje med Sønderskærelsen!
Ku yi hankali da karnuka. Ku yi hankali da miyagun ma'aikata. Ku yi hankali da masu yanke-yanke.
3 Thi vi ere Omskærelsen, vi, som tjene i Guds Ånd og rose os i Kristus Jesus og ikke forlade os på Kødet",
Gama mune kaciyar. Don mune muke sujada ta wurin Ruhun Allah. Mune masu fahariya chikin Almasihu Yesu, kuma ba mu da gabagadi cikin jiki.
4 endskønt også jeg har det, jeg kunde forlade mig på også i Kødet, Dersom nogen anden synes, han kan forlade sig på Kødet, kan jeg det mere.
Ko da shike, ni kaina ina gabagadi ga jiki. Idan wani zai iya tunanin gabagadi ga jiki, ni na fi shi.
5 Jeg er omskåren på den ottende Dag, af Israels Slægt, Benjamins Stamme, en Hebræer af Hebræere, over for Loven en Farisæer,
An yi mani kaciya a rana ta takwas, daga mutanen Israila, na kabilar Biliyaminu, Bayahuden Yahudawa; ga zancen shari'a Bafarisiye nake.
6 i Nidkærhed en Forfølger af Menigheden, i Retfærdigheden efter Loven udadlelig.
Wajen himma na tsanantawa ikilisiya. Ga zancen adalci cikin sharia, na zama mara abin zargi.
7 Men hvad der var mig Vinding, det har jeg for Kristi Skyld agtet for Tab;
Amma duk wadannan abubuwan da suka zama riba a gare ni, na dauke su asara ne saboda Almasihu.
8 ja sandelig, jeg agter endog alt for at være Tab imod det langt højere, at kende Kristus Jesus, min Herre, for hvis Skyld jeg har lidt Tab på alt og agter det for Skarn, for at jeg kan vinde Kristus
I, lallai ina lisafta dukan wadannan abubuwa asara saboda mafificin sanin Almasihu Yesu Ubangijina. Saboda shine na yi asarar dukan abubuwa. Na maishe su marasa amfani domin in ribato Almasihu,
9 og findes i ham, så jeg ikke har min Retfærdighed, den af Loven, men den ved Tro på Kristus, Retfærdigheden fra Gud på Grundlag af Troen,
a iske ni cikinsa. Ba ni da wani adalcin kaina ta wurin shari'a. Maimakon haka, ina da adalci ta wurin bangaskiya cikin Almasihu, adalcin dake daga wurin Allah ta wurin Bangaskiya.
10 for at jeg må kende ham og hans Opstandelses Kraft og hans Lidelsers Samfund, idet jeg bliver ligedannet med hans Død,
Yanzu ina so in san shi da ikon tashinsa, da tarayya cikin shan wuyarsa. In kuma zama kamarsa wajen mutuwarsa,
11 om jeg dog kunde nå til Opstandelsen fra de døde.
domin ta ko kaka in kai ga tashi daga cikin matattu.
12 Ikke at jeg allerede har grebet det eller allerede er fuldkommen; men jeg jager derefter, om jeg dog kunde gribe det, efterdi jeg også er greben af Kristus Jesus.
Ba wai na rigaya na sami wadannan abubuwa bane, ko kuma na riga na zama cikakke. Amma ina nace bi domin in cafki wannan da Almasihu Yesu ya cafko ni dominsa.
13 Brødre! jeg mener ikke om mig selv, at jeg har grebet det.
'Yan'uwa, ban dauka cewa na riga na cafka ba tukuna. Amma akwai abu daya da nake yi: ina mantawa da abin da ke baya, ina kutsawa zuwa ga abin da ke gaba.
14 Men eet gør jeg: glemmende, hvad der er bagved, men rækkende efter det, som er foran, jager jeg imod Målet, til den Sejrspris, hvortil Gud fra det høje kaldte os i Kristus Jesus.
Ina nacewa zuwa ga manufar nan in kai ga samun ladar nasara na madaukakin kiran Allah cikin Almasihu Yesu.
15 Lader da os, så mange som ere fuldkomne, have dette Sindelag; og er der noget, hvori I ere anderledes sindede, da skal Gud åbenbare eder også dette.
Dukan mu wadanda muke kammalallu, sai mu yi tunani ta wannan hanyar, idan kuwa kun yi tunanin wani abu daban, to Allah zai bayyana maku wannan kuma.
16 Kun at vi, så vidt vi ere komne, vandre i samme Retning.
Sai dai, in da muka rigaya muka kai, bari mu rike shi haka.
17 Vorder mine Efterlignere, Brødre! og agter på dem, der vandre således, som I have os til Forbillede.
Ku zama masu koyi da ni, 'yan'uwa. Ku duba da kyau wadannan da suke tafiya yadda muka zama abin koyi a gare ku.
18 Thi mange vandre, som jeg ofte har sagt eder, men nu også siger med Tårer, som Kristi Kors's Fjender,
Mutane da dama suna tafiya -sune wadanda na ba ku labarin su, yanzu kuma ina fada maku har da hawaye - kamar makiyan gicciyen Almasihu ne.
19 hvis Ende er Fortabelse, hvis Gud er Bugen, og hvis Ære er i deres Skændsel, de, som tragte efter de jordiske Ting.
Karshen su hallaka ne. Domin allahn su ciki ne, fahariyar su kuma tana cikin kunyar su. Tunanin su na kan al'amuran duniya.
20 Thi vort Borgerskab er i Himlene, hvorfra vi også forvente som Frelser den Herre Jesus Kristus,
Amma mu 'yangarincin mu a sama yake, daga inda muke sauraron mai ceto, Ubangiji Yesu Almasihu.
21 der skal forvandle vort Fornedrelses-Legeme til at blive ligedannet med hans Herligheds-Legeme, efter den Kraft, ved hvilken han også kan underlægge sig alle Ting.
Za ya sake jikinmu na kaskanci ya siffanta shi kamar jikin darajarsa, siffantacce ta karfin ikonsa inda ya sarayar da dukan abubuwa a gare shi.

< Filipperne 3 >