< Mikas 6 >

1 Hør, hvad HERREN taler: Kom fremfør din Trætte for Bjergene, lad Højene høre din Røst!
Ku saurari abin da Ubangiji ya ce, “Tashi ku gabatar da ƙararku a gaban duwatsu; bari tuddai su ji abin da kuke so ku faɗa.
2 I Bjerge, hør HERRENs Trætte, lyt til, I Jordens Grundvolde! Thi HERREN har Trætte med sit Folk, med Israel går han i Rette:
“Ku saurara, ya ku duwatsu game da tuhumar da Ubangiji yake muku, ku ji, ku daɗaɗɗun tushin duniya. Gama Ubangiji yana da ƙara a kan mutanensa; yana tuhumar Isra’ila.
3 Hvad har jeg gjort dig, mit Folk. med hvad har jeg plaget dig? Svar!
“Ya ku mutanena, me na yi muku? Ta yaya na nawaita muku? Ku amsa mini.
4 Jeg førte dig jo op fra Ægypten og udløste dig af Trællehuset, og jeg sendte for dit Ansigt Moses, Aron og Mirjam.
Na fito da ku daga ƙasar Masar na kuma’yantar da ku daga ƙasar bauta. Na aika da Musa yă jagorance ku, haka ma Haruna da Miriyam.
5 Mit Folk, kom i Hu, hvad Kong Balak af Moab havde i Sinde, og hvad Bileam, Beors Søn, svarede ham, fra Sjittim til Gilgal, for at du kan kende HERRENs Retfærdsgerninger.
Ya ku mutanena, ku tuna abin da Balak sarkin Mowab ya ƙulla da kuma amsar da Bala’am ɗan Beyor ya bayar. Ku tuna da tafiyarku daga Shittim zuwa Gilgal, don ku san ayyukan adalcin Ubangiji.”
6 "Med hvad skal jeg møde HERREN, bøje mig for Højhedens Gud? Skal jeg møde ham med Brændofre, møde med årgamle Kalve?
Da me zan zo a gaban Ubangiji in rusuna a gaban Maɗaukaki Allah? Shin, zan zo ne a gabansa da hadaya ta ƙonawa, da ɗan maraƙi bana ɗaya?
7 Har HERREN Behag i Tusinder af Vædre, Titusinder af Oliestrømme? Skal jeg give min førstefødte for min Synd, mit Livs Frugt som Bod for min Sjæl?"
Ubangiji zai ji daɗin hadayar raguna dubbai da kuma rafuffukan mai dubbai goma? Zan ba da ɗan farina ne don laifina, ko’ya’yan jikina domin zunubin raina?
8 Det er sagt dig, o Menneske, hvad der er godt, og hvad HERREN kræver af dig: hvad andet end at øve Ret, gerne vise Kærlighed og vandre ydmygt med din Gud.
Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau. Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.
9 Hør, HERREN råber til Byen (at frygte dit Navn er Visdom): Hør, Stamme og Byens Menighed!
Ku saurara! Ubangiji yana kira ga birni, a ji tsoron sunana kuwa hikima ce, “Ku kasa kunne ga sandan nan da kuma wannan wanda ya naɗa.
10 Skal jeg tåle Skattene i den gudløses Hus og den magre, forbandede Efa,
Har yanzu zan manta, ya muguwar gida da dukiyarki da kika samu a muguwar hanya zan kuma manta da bugaggen mudun awo wanda ake zargi?
11 tilgive Gudløsheds Vægt og Pungen med falske Lodder?
Zan kuɓutar da mutumin da yake da ma’auni na rashin gaskiya, da kuma buhun ma’aunan ƙarya?
12 Dens Rigmænd er fulde af Vold, dens Borgeres Tale er Løgn, og Tungen er falsk i deres Mund.
Attajiranta masu fitina ne; mutanenta kuma maƙaryata ne harsunansu kuwa suna yaudara.
13 Derfor tog jeg til at slå dig, ødelægge dig for dine Synder.
Saboda haka, zan hallaka ku in lalace ku saboda zunubanku.
14 Du skal spise, men ikke mættes, lige tomt skal dit Indre være; hvad du hengemmer, skal du ej bjærge, og hvad du bjærger, giver jeg Sværdet;
Za ku ci amma ba za ku ƙoshi ba, cikinku zai zama babu kome Za ku tattara amma ba za ku yi ajiyar kome ba, gama abin da kuka yi ajiya zan ba wa takobi.
15 du skal så, men ikke høste, perse Oliven, men ikke salve dig, perse Most, men ej drikke Vin.
Za ku yi shuki amma ba za ku girba ba; za ku matse zaitun amma ba za ku yi amfani da mai wa kanku ba, za ku tattaka’ya’yan inabi amma ba za ku sha ruwan inabin ba.
16 Du fulgte Omris Skikke, al Akabs Huses Færd; I vandrede efter deres Råd, så jeg må gøre dig til Ørk og Byens Borgere til Spot; Folkenes Hån skal I bære.
Kuna kiyaye ƙa’idodin Omri da dukan ayyukan gidan Ahab kun kuma bi al’adunsu. Saboda haka, zan maishe ku kufai in mai da ku abin dariya a cikin mutane, za ku sha reni a wurin al’ummai.”

< Mikas 6 >