< Jeremias 27 >
1 I Josiass Søns, Kong Jojakim af Judas, første regeringstid kom dette Ord til Jeremias fra HERREN:
A farkon sarautar Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji.
2 Således sagde HERREN til mig: Gør dig Reb og Ågstænger og læg dem på din Hals
Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka yi karkiyar itace da maɗaurai ka ɗaura a wuyanka.
3 og send Edoms, Moabs, Ammoniternes, Tyruss og Zidons Konger Bud ved deres Sendemænd, som er kommet til Kong Zedekias af Juda i Jerusalem;
Sa’an nan ka aika da saƙo zuwa wurin sarakunan Edom, Mowab, Ammon, Taya da Sidon ta bakin jakadu waɗanda suka zo Urushalima wurin Zedekiya sarkin Yahuda.
4 byd dem at sige til deres Herrer: Så siger Hærskarers HERRE. Israels Gud: Sig til eders Herrer:
Ka ba su saƙo wa iyayengijinsu su ce, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Ku faɗa wa iyayengijinku wannan.
5 Jeg skabte Jorden og Menneskene og Kvæget på Jorden ved min vældige Styrke og min udrakte Hånd, og jeg giver den, til hvem jeg finder for godt.
Da ikon mai ƙarfi da kuma hannuna da na miƙa na yi duniya da mutanenta da kuma dabbobin da suke ciki, na ba da ita ga duk wanda na ga dama.
6 Og nu giver jeg alle disse Lande i min Tjener Kong Nebukadnezar af Babels Hånd, selv Markens Vildt giver jeg hen til at trælle for ham.
Yanzu zan ba da dukan ƙasashenku ga bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon; zan sa namun jeji ma su bauta masa.
7 Alle Folk skal trælle for ham, hans Søn og Sønnesøn, indtil også hans Lands Time slår og mange Folkeslag og store Konger gør ham til deres Træl.
Dukan al’ummai za su bauta masa da ɗansa da kuma jikansa har sai har lokacin ƙasarsa ya kai; sa’an nan al’ummai masu yawa da kuma manyan sarakuna za su kasance a ƙarƙashinsa.
8 Og det Folk og det Rige, som ikke vil trælle for ham, Kong Nebukadnezar af Babel, og bøje Hals under Babels Konges Åg, det vil jeg hjemsøge med Sværd, Hunger og Pest, lyder det fra HERREN, til det er tilintetgjort ved hans Hånd.
“‘“Amma fa, duk al’umma ko mulkin da bai bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon ba bai kuwa rusunar da wuyarsa ga karkiyarsa ba, zan hukunta wannan al’umma da takobi, yunwa da annoba, in ji Ubangiji, har sai na hallaka ta ta wurin hannunsa.
9 I skal ikke høre på eders Profeter og Spåmænd, eders Drømmere, Sandsigere og Troldmænd, som siger til eder: "I skal ikke komme til at trælle for Babels Konge;
Saboda haka kada ku saurari annabawanku, masu dubanku, masu fassarar mafarkanku, bokayenku ko masu maitancinku waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba.’
10 thi det er Løgn, de profeterer for eder for at få eder bort fra eders Jord, idet jeg da driver eder bort og I går til Grunde.
Suna muku annabcin ƙaryar ne kawai da za tă kau da ku daga ƙasarku; zan kore ku za ku kuwa hallaka.
11 Men det Folk, der bøjer Hals under Babels Konges Åg og træller for ham, vil jeg lade blive på sin Jord, lyder det fra HERREN, så det kan dyrke den og bo der.
Amma duk al’ummar da ta rusuna da wuyarta a ƙarƙashin karkiyar sarkin Babilon ta kuma bauta masa, zan bar al’ummar ta zauna a ƙasarta ta noma ta, ta kuma zauna a can, in ji Ubangiji.”’”
12 Og til Kong Zedekias af Juda talte jeg i Overensstemmelse med alle disse Ord: Bøj Hals under Babels Konges Åg og træl for ham og hans Folk, så skal I leve.
Na ba da wannan saƙo guda ga Zedekiya sarkin Yahuda. Na ce, “Ka rusunar da wuyanka a ƙarƙashin sarkin Babilon; ka bauta masa da kuma mutanensa, za ka kuwa rayu.
13 Hvorfor vil du og dit Folk dø ved Sværd, Hunger og Pest, således som HERREN truede det Folk, der ikke vil trælle for Babels Konge?
Me ya sa kai da mutanenka za ku mutu saboda takobi, yunwa da annoba waɗanda Ubangiji ya yi barazana wa duk al’ummar da ba za tă bauta wa sarkin Babilon ba?
14 Hør ikke på Profeternes Ord, når de siger til eder: "I skal ikke komme til at trælle for Babels Konge"; thi Løgn profeterer de eder.
Kada ku saurari maganganun annabawa waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba,’ gama annabcin ƙarya suke muku.
15 Jeg har ikke sendt dem, lyder det fra HERREN, og de profeterer Løgn i mit Navn, for at jeg skal bortstøde eder, så I går til Grunde sammen med Profeterne, der profeterer for eder.
‘Ban aike su ba,’ in ji Ubangiji. ‘Suna annabcin ƙarya ne da sunana. Saboda haka, zan kore ku za ku kuwa hallaka, da ku da kuma annabawan da suke muku annabci.’”
16 Og til Præsterne og alt dette Folk talte jeg således: Så siger HERREN: Hør ikke på eders Profeters Ord, når de profeterer for eder og siger: "Se, HERRENs Huss Kar skal nu snart føres hjem fra Babel." Thi Løgn profeterer de eder.
Sai na ce wa firistoci da dukan waɗannan mutane, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, kada ku saurari annabawan da suke cewa, ‘Ba daɗewa ba za a komo da kayan gidan Ubangiji daga Babilon.’ Suna muku annabcin ƙarya ne.
17 Hør dem ikke, men træl for Babels Konge, så skal I leve. Hvorfor skal denne By lægges øde?
Kada ku saurare su. Ku bauta wa sarkin Babilon, za ku kuwa rayu. Don me wannan birni zai zama kufai?
18 Er de Profeter og har HERRENs Ord, så lad dem gå i forbøn hos Hærskarers HERRE, at de Kar, der er tilbage i HERRENs Hus og Judas konges Palads, ikke også skal komme til Babel.
In su annabawa ne da gaske suna kuma da maganar Ubangiji, bari su roƙi Ubangiji Maɗaukaki ya sa kada a kwashe kayayyakin da suka ragu a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da kuma cikin Urushalima a kai Babilon.
19 Thi så siger Hærskarers HERRE om Søjlerne, Havet og Stellene og om de sidste Kar, der er tilbage i denne By,
Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da ginshiƙai, kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan,
20 dem, som Kong Nebukadnezar af Babel ikke tog med, da han bortførte Jojakims søn, Kong Jekonja af Juda, fra Jerusalem til Babel med alle de ypperste i Juda og Jerusalem,
waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwashe sa’ad da ya kame Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon tare da dukan manyan mutanen Yahuda da Urushalima,
21 ja, så siger Hærskarers HERRE, Israels Gud, om de kar, der er tilbage i HERRENs Hus og Judas Konges Palads og i Jerusalem:
I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa game da abubuwan da aka bari a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da Urushalima,
22 De skal føres til Babel, og der skal de blive, til den Dag jeg tager mig af dem og fører dem op og bringer dem tilbage hertil, lyder det fra HERREN.
‘Za a kwashe su zuwa Babilon a can kuwa za su kasance sai ranar da na neme su,’ in ji Ubangiji. ‘Sa’an nan zan komo da su in maido da su wannan wuri.’”