< 1 Tessalonikerne 5 >

1 Men om Tid og Time, Brødre! have I ikke nødig, at der skrives til eder;
Yanzu fa game da zancen lokatai da zamanai 'yan'uwa, ba ku da bukatar a rubuta maku wani abu.
2 thi I vide selv grant, at Herrens Dag kommer som en Tyv om Natten.
Domin ku da kanku kun sani kwarai cewa ranar zuwan Ubangiji kamar barawo take da dare.
3 Når de sige: "Fred og ingen Fare!" da kommer Undergang pludselig, over dem ligesom Veerne over den frugtsommelige, og de skulle ingenlunde undfly.
Da suna zancen “zaman lafiya da kwanciyar rai,” sai hallaka ta zo masu ba zato ba tsammani. Zai zama kamar nakudar haihuwa ce da ke kama mace mai ciki. Ba su kwa da wata hanyar kubuta.
4 Men I, Brødre! I ere ikke i Mørke, så at Dagen skulde overraske eder som en Tyv.
Amma ku, 'yan'uwa, ai ba cikin duhu kuke ba har da wannan rana zata mamaye ku kamar barawo.
5 Thi I ere alle Lysets Børn og Dagens Børn, vi ere ikke Nattens eller Mørkets Børn.
Domin dukkan ku 'ya'yan haske ne 'ya'yan rana kuwa. Mu ba 'ya'yan dare ba ne ko na duhu,
6 Så lader os da ikke sove ligesom de andre, men lader os våge og være ædrue!
Don haka, kada muyi barci kamar yadda sauran ke yi. Maimakon haka, bari mu kasance muna zaman tsaro kuma muna a fadake.
7 Thi de, som sove, sove om Natten, og de, som beruse sig, ere berusede om Natten.
Don masu yin barci da dare suke yin barci, haka kuma masu sha su bugu ma da dare suke yi.
8 Men da vi høre Dagen til, så lader os være ædrue, iførte Troens og Kærlighedens Panser og Frelsens Håb som Hjelm!
Tunda shike mu 'ya'yan rana ne, bari mu zauna a natse. Bari musa sulke na bangaskiya da kauna, mu kuma sa kwalkwali don ceton mu dake gaba.
9 Thi Gud bestemte os ikke til Vrede, men til at vinde Frelse ved vor Herre Jesus Kristus,
Domin Allah bai kaddara mu ga fushinsa ba, sai dai ga samun ceto ta wurin Ubangijin mu Yesu Almasihu.
10 som døde for os, for at vi, hvad enten vi våge eller sove, skulle leve sammen med ham.
Shi ne wanda ya mutu domin mu, don ko da muna raye ko muna mace, mu iya rayuwa tare da shi,
11 Formaner derfor hverandre og opbygger den ene den anden, ligesom I også gøre.
Domin haka ku ta'azantar da juna ku kuma inganta juna, kamar yadda kuke yi.
12 Men vi bede eder, Brødre! at I skønne på dem, som arbejde iblandt eder og ere eders Forstandere i Herren og påminde eder,
Muna rokon ku, 'yan'uwa, ku bada daraja ga wadanda suke aiki a tsakaninku wadanda kuma suke shugabanci a kan ku cikin Ubangiji, wadanda kuma suke horonku.
13 og agte dem højlig i Kærlighed for deres Gernings Skyld. Holder Fred med hverandre!
Muna kuma rokon ku, da ku kula dasu ku kuma kaunacesu sabili da irin ayyukansu. Ku kuma yi zaman lafiya da junan ku.
14 Og vi formane eder, Brødre! påminder de uskikkelige, trøster de modfaldne, tager eder af de skrøbelige, værer langmodige imod alle!
Muna yi maku gargadi 'yan'uwa; ku jawa marassa ji kunne, ku karfafa marassa karfin zuciya, ku taimaki gajiyayyu, kuyi zaman hakuri da kowa.
15 Ser til, at ingen gengælder nogen ondt med ondt; men stræber altid efter det gode, både imod hverandre og imod alle.
Ku lura kada wani ya rama mugunta da mugunta, Maimakon haka ma, Ku cigaba da abinda ke mai kyau ga juna da kowa duka.
16 Værer altid glade,
Kuyi farin ciki koyaushe.
17 beder uafladelig,
Kuyi addu'a ba fasawa.
18 takker i alle Forhold; thi dette er Guds Villie med eder i Kristus Jesus.
A cikin kome kuyi godiya. Domin wannan ne nufin Allah a cikin Yesu Almasihu game daku.
19 Udslukker ikke Ånden,
Kada ku hana Ruhun Allah aiki a cikin ku.
20 ringeagter ikke Profetier,
Kada ku raina anabce anabce.
21 prøver alt, beholder det gode!
Ku gwada komai. Ku rike abinda ke mai kyau.
22 Holder eder fra det onde under alle Skikkelser!
Ku kaucewa duk wani abinda yayi kama da mugunta.
23 Men han selv, Fredens Gud, helliggøre eder ganske og aldeles, og gid eders Ånd og Sjæl og Legeme må bevares helt og holdent, uden Dadel i vor Herres Jesu Kristi Tilkommelse!
Bari Allah na salama ya mai da ku cikakun tsarkaka. Bari dukkan ruhun ku, da zuciyar ku, da jikin ku su zama adanannu marassa zargi domin zuwan Ubangijin mu Yesu Almasihu.
24 Trofast er han, som kaldte eder, han skal også gøre det.
Wanda ya kira ku mai aminci ne, wanda kuma zai aikata.
25 Brødre! beder for os!
Yan'uwa, kuyi addu'a domin mu.
26 Hilser alle Brødrene med et helligt Kys!
Ku gaida dukkan yan'uwa da tsattsarkar sumba.
27 Jeg besværger eder ved Herren, at dette Brev må blive oplæst for alle de hellige Brødre.
Ina rokon ku saboda Ubangiji ku karanta wasikar nan ga dukkan 'yan'uwa.
28 Vor Herres Jesu Kristi Nåde være med eder!
Bari alherin Ubangijin mu Yesu Almasihu shi kasance tareda ku.

< 1 Tessalonikerne 5 >