< 1 Johannes 5 >
1 Hver den, som tror, at Jesus er Kristus, er født af Gud; og hver den, som elsker Faderen, elsker også den, som er født af ham.
Duk Wanda ya gaskata Yesu shine Almasihu haifaffe na Allah ne. Kuma duk wanda ya kaunaci uba ya kaunaci dan da uban ya haifa.
2 Derpå kende vi, at vi elske Guds Børn, når vi elske Gud og gøre hans Bud.
Haka muka sani muna kaunar 'ya'yan Allah: yayin da muka kaunaci Allah, kuma muka aikata umarninsa.
3 Thi dette er Kærlighed til Gud, at vi holde hans Bud; og hans Bud ere ikke svære;
Wannan itace kaunar Allah, cewa mu kiyaye umarninsa. Domin umarninsa ba masu nawaitawa bane.
4 thi alt det, som er født af Gud, overvinder Verden; og dette er den Sejr, som har overvundet Verden, vor Tro.
Duk wanda yake haifaffe na Allah yakan yi nasara da duniya. Wannan itace nasarar da ta rinjayi duniya, wato bangaskiyarmu.
5 Hvem er den, som overvinder Verden, uden den, som tror, at Jesus er Guds Søn?
Wanene wannan mai nasara da duniya? Sai dai wanda ya gaskata Yesu Dan Allah ne.
6 Han er den, som kom med Vand og Blod, Jesus Kristus; ikke med Vandet alene, men med Vandet og med Blodet; og det er Ånden, som viduer, thi Ånden er Sandheden.
Wannan shine wanda yazo ta wurin ruwa da jini: Yesu Almasihu. Ya zo ba ta wurin ruwa kadai ba, amma ta wurin ruwa da jini.
7 Thi tre ere de, som vidne:
Domin akwai uku wadanda suke bada shaida:
8 Ånden og Vandet og Blodet; og disse tre forene sig til eet.
Ruhu, da ruwa, da kuma jini. Wadannan ukun kuwa manufarsu daya ce.
9 Dersom vi tage imod Menneskenes Vidnesbyrd, da er Guds Søn.
Idan mun karbi shaidar mutane, shaidar Allah ta fi girma. Wannan ita ce shaidar Allah, wato ya bada shaida akan Dansa.
10 Den, som tror på Guds Søn, har Vidnesbyrdet i sig selv; den, som ikke tror Gud, har gjort ham til en Løgner, fordi han ikke har troet på det Vidnesbyrd, som Gud har vidnet om sin Søn.
Wanda ya gaskata da Dan Allah shaidar tana nan tare da shi. Duk wanda bai bada gaskiya ga Allah ba, ya mai da shi makaryaci kenan, domin bai gaskata da shaidar da Allah ya bayar game da Dansa ba.
11 Og dette er Vidnesbyrdet, at Gud har givet os evigt Liv; og dette Liv er i hans Søn. (aiōnios )
Wannan ita ce shaida: Allah ya bamu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Dansa. (aiōnios )
12 Den, som har Sønnen, har Livet; den, som ikke har Guds Søn, har ikke Livet.
Duk wanda yake da Dan, yana da rai. Duk wanda ba shida Dan Allah kuwa bashi da rai.
13 Dette har jeg skrevet til eder, for at I skulle vide, at I have evigt Liv, I, som tro på Guds Søns Navn. (aiōnios )
Na rubuto maku wannan ne don ku tabbata kuna da rai madawwami—a gare ku wadanda suka gaskata da sunan Dan Allah. (aiōnios )
14 Og dette er den Frimodighed, som vi have over for ham, at dersom vi bede om noget efter hans Villie, hører han os.
Wannan shine gabagadin da muke da shi a gabansa, wato, in mun roki kome bisa ga nufinsa, zai ji mu.
15 Og dersom vi vide, at han hører os, hvad vi end bede om, da vide vi, at vi have de Ting, om hvilke vi have bedt ham.
Haka kuma, in mun san yana jinmu—Duk abin da mu ka rokeshi—mun sani muna da duk abin da muka roka daga gare shi.
16 Dersom nogen ser sin Broder begå Synd, som ikke er til Døden, han bede, og han skal give ham Liv, dem nemlig, som ikke synde til Døden. Der er Synd til Døden; for den siger jeg ikke, at han skal bede.
Idan wani ya ga dan'uwansa ya yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai yayi masa addu'a, Allah kuwa zai ba shi rai. Ina nufin wadanda suka yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yake kai wa ga mutuwa: Ban ce a yi addu'a domin wannan ba.
17 Al uretfærdighed er synd, men der er synd, som ikke er til døden.
Dukkan rashin adalci, zunubi ne, amma akwai zunubin da bai kai ga mutuwa ba.
18 Vi vide, at hver den, som er født af Gud, synder ikke; men den, som er født af Gud, bevarer sig selv, og den onde rører ham ikke.
Mun sani kowanne haiffafe daga wurin Allah ba ya yin zunubi. Amma wanda ke haifaffe daga wurin Allah, ya kan kare shi, mugun nan kuwa ba zai iya yi masa illa ba.
19 Vi vide, at vi ere af Gud, og hele Verden ligger i det onde.
Mun sani mu na Allah ne, mun kuma sani dukkan duniya tana hannun mugun nan.
20 Men vi vide, at Guds Søn er kommen, og han har givet os Forstand til at kende den sande; og vi ere i den sande, i hans Søn Jesus Kristus. Denne er den sande Gud og evigt Liv. (aiōnios )
Amma mun sani Dan Allah yazo, kuma ya bamu fahimta, domin mu san wanda yake shi ne mai gaskiya. Haka kuma muna cikin wannan wanda shine gaiskiya, kuma cikin Dansa Yesu Almasihu. Shine Allah na gaskiya, da kuma rai na har abada. (aiōnios )
21 Mine Børn, vogter eder for Afguderne!
'Ya'ya, ku tsare kanku daga bautar gumaka.