< Romerne 9 >
1 Sandhed siger jeg i Kristus, jeg lyver ikke, min Samvittighed vidner med mig i den Helligaand,
Gaskiya ne nake gaskiya nake fada cikin Almasihu. Ba karya nake yi ba. Lamirina, na shaida a cikin Ruhu Mai Tsarki.
2 at jeg har en stor Sorg og en uafladelig Kummer i mit Hjerte.
cewa ina da matukar bakin-ciki da takaici marar karewa a zuciyata.
3 Thi jeg kunde ønske selv at være bandlyst fra Kristus til Bedste for mine Brødre, mine Frænder efter Kødet,
Dama ace, a la'anta ni, in rabu da Almasihu saboda 'yan'uwana, wato dangina da suke zuriyata bisa ga jiki.
4 de, som jo ere Israeliter, hvem Sønneudkaarelsen og Herligheden og Pagterne og Lovgivningen og Gudstjenesten og Forjættelserne tilhøre,
Sune Isra'ilawa, sun sami karbuwa, da daukaka, da baiwar shari'a, da yi wa Allah sujada, da alkawarai.
5 hvem Fædrene tilhøre, og af hvem Kristus er efter Kødet, han, som er Gud over alle Ting, højlovet i Evighed! Amen. (aiōn )
Dukkan ubanni nasu ne daga cikinsu Almasihu ya fito bisa ga jiki- wanda shi ke Allah bisa kowa. Yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin. (aiōn )
6 Ikke dog som om Guds Ord har glippet; thi ikke alle, som stamme fra Israel, ere Israel;
Amma ba wai alkawarin Allah ya kasa ba ne, ba dukkan Isra'ilawa ne suke Isra'ilawa na gaskiya ba.
7 ej heller ere alle Børn, fordi de ere Abrahams Sæd, men: „I Isak skal en Sæd faa Navn efter dig.‟
Haka nan, ba dukkan zuriyar Ibrahim ne 'ya'yansa ba. Amma ''ta wurin Ishiyaku ne za'a kira zuriyarka.''
8 Det vil sige: Ikke Kødets Børn ere Guds Børn, men Forjættelsens Børn regnes for Sæd.
Yana nuna mana cewa ba 'ya'yan jiki su ne 'ya'yan Allah ba. Amma 'ya'yan alkawari ne ake kirga su, kuma aka kebe su.
9 Thi et Forjættelsesord er dette: „Ved denne Tid vil jeg komme, saa skal Sara have en Søn.‟
Wanna ce kalmar alkawari, ''badi warhaka zan dawo, Saratu kuwa zata sami da.''
10 Men saaledes skete det ikke alene dengang, men ogsaa med Rebekka, da hun var frugtsommelig ved een, Isak, vor Fader.
Amma ba wannan kadai ba, bayan Rifkatu ta dauki ciki daga gun mijinta, ubammu Ishiyaku.
11 Thi da de endnu ikke vare fødte og ikke havde gjort noget godt eller ondt, blev der, for at Guds Udvælgelses Beslutning skulde staa fast, ikke i Kraft af Gerninger, men i Kraft af ham, der kalder,
Yaran nan kafin ma a haife su, balle ma a ce sun yi wani abu mai kyau ko laifi, saboda zaben da Allah yayi, bai danganta da abin da suka yi ba, ko don aiki ba, amma don shine mai kira—
12 sagt til hende: „Den ældste skal tjene den yngste, ‟
kamar yadda Ya ce, mata, “babban zaya yiwa karamin bauta,'' haka nassi yace,
13 som der er skrevet: „Jakob elskede jeg, men Esau hadede jeg.‟
''Kamar yadda aka rubuta: “Yakubu na ke kauna, amma Isuwa na ki shi.”
14 Hvad skulle vi da sige? mon der er Uretfærdighed hos Gud? Det være langt fra!
To me zamu ce kenan? Allah ya yi rashin adalci kenan? Ko kadan.
15 Thi han siger til Moses: „Jeg vil være barmhjertig imod den, hvem jeg er barmhjertig imod, og forbarme mig over den, hvem jeg forbarmer mig over.‟
Gama ya ce wa Musa, ''Ina nuna jinkai ga wanda zan yi wa jinkai, zan ji tausayi ga wanda zan tausaya masa.''
16 Altsaa staar det ikke til den, som vil, ej heller til den, som løber, men til Gud, som er barmhjertig.
Saboda haka, ba don wanda ke da aniya ba ne, ko kuwa wanda yake kokari ba, amma saboda Allah mai nuna jinkai.
17 Thi Skriften siger til Farao: „Netop derfor lod jeg dig fremstaa, for at jeg kunde vise min Magt paa dig, og for at mit Navn skulde forkyndes paa hele Jorden.‟
Gama nassi ya ce da Fir'auna, '' Saboda wannan dalilin ne, na tada kai, don in nuna ikona mai karfi a kanka, don sunana ya yadu ga dukkan duniya.''
18 Saa forbarmer han sig da over den, som han vil, men forhærder den, som han vil.
Ta haka Allah ya nuna jinkansa ga wanda ya so, ya taurarar da zuciyar wanda ya ga dama.
19 Du vil nu sige til mig: Hvad klager han da over endnu? thi hvem staar hans Villie imod?
Za kuce mani, to don me, ''Yake kama mu da llaifi? Wa ya taba yin jayayya da nufinsa?''
20 Ja, men, hvem er dog du, o Menneske! som gaar i Rette med Gud? mon noget, som blev dannet, kan sige til den, som dannede det: Hvorfor gjorde du mig saaledes?
In ma mun duba, kai mutum wanene kai da zaka ja da Allah? Ko abin da aka gina zai ce wa magininsa, ''Don me yasa ka ginani haka?''
21 Eller har Pottemageren ikke Raadighed over Leret til af den samme Masse at gøre et Kar til Ære, et andet til Vanære?
Ko maginin ba shi da iko akan yimbu daya da zai gina tukunya mai daraja, wata kuma tukunyar don kowanne irin aiki?
22 Men hvad om nu Gud, skønt han vilde vise sin Vrede og kundgøre sin Magt, dog med stor Langmodighed taalte Vredes-Kar, som vare beredte til Fortabelse,
In ace Allah, dake niyyar nuna fushinsa da ikonsa, ya sanu, sai ya jure da matukar hakuri mai yawa da tukwanen fushi da ya shirya don hallakarwar fa?
23 ogsaa for at kundgøre sin Herligheds Rigdom over Barmhjertigheds-Kar, som han forud havde beredt til Herlighed?
To ko ma ya yi haka don ya nuna yalwar daukakarsa da take dauke da alheri, wanda ya shirya don daukakarsa tun farko?
24 Og hertil kaldte han ogsaa os, ikke alene af Jøder, men ogsaa af Hedninger,
Zai yiwu ma ya yi haka ne domin mu, mu da ya kira, ba ma daga cikin Yahudawa kadai ba, amma har ma daga cikin al'ummai?
25 som han ogsaa siger hos Hoseas: „Det, som ikke var mit Folk, vil jeg kalde mit Folk, og hende, som ikke var den elskede, den elskede;
Kamar yadda ya ce a cikin littafin Yusha'u: ''zan kira wadanda ba mutanena ba mutanena, da kuma kaunatattunta wadanda ba kaunatattu ba.
26 og det skal ske, at paa det Sted, hvor der blev sagt til dem: I ere ikke mit Folk, der skulle de kaldes den levende Guds Børn.‟
Zai zama kuma a inda aka ce da su, “ku ba mutanena bane, za a kisa su 'ya'yan Allah mai rai.”'
27 Men Esajas udraaber over Israel: „Om end Israels Børns Tal var som Havets Sand, saa skal kun Levningen frelses.
Ishaya ya yi kira game da Isra'ila, ''in a ce yawan 'ya'yan Isra'ila zasu zama kamar yashi a bakin teku, ragowarsu ne kawai za su sami ceto.
28 Thi idet Herren opgør Regnskab og afslutter det i Hast, vil han fuldbyrde det paa Jorden.‟
Ubangiji zai tabbatar da cikar kalmarsa a duniya, ba kuwa da dadewa ba.
29 Og som Esajas forud har sagt: „Dersom den Herre Zebaoth ikke havde levnet os en Sæd, da vare vi blevne som Sodoma og gjorte lige med Gomorra.‟
Yadda Ishaya ya rubuta ada, ''In da ba Ubangiji mai runduna bai bar mana zuriya ba, da zamu zama kamar Saduma, da kuma an maida mu kamar Gomarata.
30 Hvad skulle vi da sige? At Hedninger, som ikke jagede efter Retfærdighed, fik Retfærdighed, nemlig Retfærdigheden af Tro;
To me za mu ce kenan? Ko al'ummai, da ba sa neman adalci, sun samu adalci ta wurin bangaskiya.
31 men Israel, som jagede efter en Retfærdigheds Lov, naaede ikke til en saadan Lov.
Amma Isra'ila, wadanda suka nemi adalcinsu ta wurin shari'a, ba su kai ga gaci ba.
32 Hvorfor? fordi de ikke søgte den af Tro, men som af Gerninger. De stødte an paa Anstødsstenen,
To don me? don ba su neme shi da bangaskiya ba, amma ta ayyuka. Sun yi tuntube a kan dutse da zai sa laifi.
33 som der er skrevet: „Se, jeg sætter i Zion en Anstødssten og en Forargelses Klippe; og den, som tror paa ham, skal ikke blive til Skamme.‟
Kamar yadda aka rubuta, “Ga, shi na ajiye dutse a kan Sihiyona dutsen tuntube mai sa laifi. Ga wanda ya bada gaskiya gare shi ba zai ji kunya ba.”