< Esajas 47 >

1 Stig ned, sid i Støvet, du Jomfru, Babels Datter, sid uden Trone paa Jorden, Kaldæernes Datter! Thi ikke mer skal du kaldes den fine, forvænte!
“Ki gangara, ki zauna a ƙura, Budurwa Diyar Babilon; ki zauna a ƙasa ba tare da rawani ba, Diyar Babiloniyawa. Ba za a ƙara kira ke marar ƙarfi’yar gata ba.
2 Tag fat paa Kværnen, mal Mel, læg Sløret bort, løft Slæbet, blot dine Ben og vad over Strømmen!
Ɗauki dutsen niƙa ki niƙa gari; ki kware lulluɓinki. Ki ɗaga fatarinki ki bar ƙafafunki tsirara, ki kuma yi ta ratsa cikin rafuffuka.
3 Din Blusel skal blottes, din Skam skal ses. Hævn tager jeg uden Skaansel, siger vor Genløser,
Tsirararki zai bayyana za a kuma buɗe kunyarki. Zan ɗauki fansa; ba zan bar wani ba.”
4 hvis Navn er Hærskarers HERRE, Israels Hellige.
Mai Fansarmu, Ubangiji Maɗaukaki shi ne sunansa, shi ne Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
5 Sid tavs og gaa ind i Mørke, Kaldæernes Datter, thi ikke mer skal du kaldes Rigernes Dronning!
“Zauna shiru, tafi cikin duhu, Diyar Babiloniya; ba za a ƙara kira ke sarauniyar masarautai.
6 Jeg vrededes paa mit Folk, vanæred min Arv, gav dem hen i din Haand; du viste dem ingen Medynk, du lagde dit tunge Aag paa Oldingens Nakke.
Na yi fushi da mutanena na ƙazantar da gādona; na ba su ga hannunki, ba ki kuwa nuna musu jinƙai ba. Har ma da tsofaffi kin jibga musu kaya masu nauyi sosai.
7 Du sagde: »Jeg bliver evindelig Evigheds Dronning.« Du tog dig det ikke til Hjerte, brød dig ikke om Enden.
Kika ce, ‘Zan ci gaba har abada, madawwamiyar sarauniya!’ Amma ba ki lura da waɗannan abubuwa ko ki yi la’akari a kan abin da zai faru ba.
8 Saa hør nu, du yppige, du, som sidder i Tryghed, som siger i Hjertet: »Kun jeg, og ellers ingen! Aldrig skal jeg sidde Enke, ej kende til Barnløshed.«
“To, yanzu fa, ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi, mai zama da rai kwance kina kuma ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni. Ba zan taɓa zama gwauruwa ko in sha wahalar rashin’ya’ya ba.’
9 Begge Dele skal ramme dig brat samme Dag, Barnløshed og Enkestand ramme dig i fuldeste Maal, dine mange Trylleord, din megen Trolddom til Trods,
Duk waɗannan za su sha kanki cikin farat ɗaya, a rana guda, rashin’ya’ya da gwauranci. Za su zo a kanki da cikakken minzani, duk da yawan masu dubanki da kuma dukan sihirinki.
10 skønt du tryg i din Ondskab sagde: »ingen ser mig.« Din Visdom og Viden var det, der ledte dig vild, saa du sagde i Hjertet: »Kun jeg, og ellers ingen!«
Kin dogara a muguntarki kika kuma ce, ‘Babu wanda ya gan ni.’ Hikimarki da saninki sun ɓad da ke sa’ad da kika ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni.’
11 Dig rammer et Onde, du ikke kan købe bort, over dig falder et Vanheld, du ikke kan sone, Undergang rammer dig brat, naar mindst du aner det.
Bala’i zai fāɗo a kanki, kuma ba za ki san yadda za ki rinjaye shi yă janye ba. Masifa za tă fāɗo a kanki da ba za ki iya tsai da ita da kuɗin fansa ba; lalacewar da ba ki taɓa mafarkinta ba za tă auko miki nan da nan.
12 Kom med din Trolddom og med dine mange Trylleord, med hvilke du umaged dig fra din Ungdom, om du kan bøde derpaa og skræmme det bort.
“Ki dai ci gaba, da sihirinki da kuma makarunki masu yawa, waɗanda kika yi ta wahala tun kina jaririya. Mai yiwuwa ki yi nasara, mai yiwuwa ki jawo fargaba.
13 Med Raadgiverhoben sled du dig træt, lad dem møde, lad Himmelgranskerne frelse dig, Stjernekigerne, som Maaned for Maaned kundgør, hvad dig skal ske!
Dukan shawarwarin da kika samu sun dai gajiyar da ke ne kawai! Bari masananki na taurari su zo gaba, waɗannan masu zāna taswirar sammai suna kuma faɗa miki dukan abin da zai faru da ke wata-wata, bari su cece ki daga abin da zai faru da ke.
14 Se, de er blevet som Straa, de fortæres af Ild, de frelser ikke deres Liv fra Luens Magt. »Ingen Glød til Varme, ej Baal at sidde ved!«
Tabbas suna kama da bunnu; wuta za tă cinye su ƙaf. Ba za su ma iya ceton kansu daga ikon wutar ba. Ba wutar da wani zai ji ɗumi; ba wutar da za a zauna kusa da ita.
15 Sligt faar du af dem, du umaged dig med, dine Troldmænd fra Ungdommen af; de raver hver til sin Side, dig frelser ingen.
Abin da za su iya yi miki ke nan kawai, waɗannan da kika yi ta fama da su kika kuma yi ciniki da su tun kina jaririya. Kowannensu zai tafi cikin kuskurensa; babu ko ɗayan da zai cece ki.

< Esajas 47 >