< Matthæus 5 >

1 Men da han saa Skarerne, steg han op paa Bjerget; og da han havde sat sig, gik hans Disciple hen til ham,
Da Yesu ya ga taron jama'ar, sai ya hau saman dutse. Sa'adda ya zauna, almajiransa suka zo wurinsa.
2 og han oplod sin Mund, lærte dem og sagde:
Ya bude bakinsa kuma ya koyar da su, yana cewa,
3 „Salige ere de fattige i Aanden, thi Himmeriges Rige er deres.
“Albarka ta tabbata ga masu talauci a ruhu, domin mulkin sama nasu ne.
4 Salige ere de, som sørge, thi de skulle husvales.
Albarka ta tabbata ga masu makoki, domin za a ta'azantar da su.
5 Salige ere de sagtmodige, thi de skulle arve Jorden.
Albarka ta tabbata ga masu tawali'u, domin za su gaji duniya.
6 Salige ere de, som hungre og tørste efter Retfærdigheden, thi de skulle mættes.
Albarka ta tabbata ga masu yunwa da kishin adalci, domin za a kosar da su.
7 Salige ere de barmhjertige, thi dem skal vises Barmhjertighed.
Albarka ta tabbata ga masu jinkai, domin za su samu jinkai.
8 Salige ere de rene af Hjertet, thi de skulle se Gud.
Albarka ta tabbata ga masu tsabtar zuciya, domin za su ga Allah.
9 Salige ere de, som stifte Fred, thi de skulle kaldes Guds Børn.
Albarka ta tabbata ga masu kawo salama, domin za a ce da su 'ya'yan Allah.
10 Salige ere de, som ere forfulgte for Retfærdigheds Skyld, thi Himmeriges Rige er deres.
Albarka ta tabbata ga wadanda ake tsananta masu saboda adalci, domin mulkin sama nasu ne.
11 Salige ere I, naar man haaner og forfølger eder og lyver eder alle Haande ondt paa for min Skyld.
Masu albarka ne ku sa'adda mutane suka zage ku, suka kuma tsananta maku, ko kuwa suka zarge ku da dukan miyagun abubuwa iri iri na karya, saboda ni.
12 Glæder og fryder eder, thi eders Løn skal være stor i Himlene; thi saaledes have de forfulgt Profeterne, som vare før eder.
Ku yi murna da matukar farin ciki, domin sakamakonku mai yawan gaske ne a sama. Ta haka ne mutane suka tsananta wa annabawa da suka yi rayuwa kafin ku.
13 I ere Jordens Salt; men dersom Saltet mister sin Kraft, hvormed skal det da saltes? Det duer ikke til andet end at kastes ud og nedtrædes af Menneskene.
Ku ne gishirin duniya, amma idan gishiri ya sane yaya za a mai da dandanonsa? Ba zai kara anfani ga komai ba, sai ko a zubar da shi, a tattake a karkashin kafafun mutane.
14 I ere Verdens Lys; en Stad, som ligger paa et Bjerg, kan ikke skjules.
Ku ne hasken duniya, birnin da ke kan tudu ba shi boyuwa.
15 Man tænder heller ikke et Lys og sætter det under Skæppen, men paa Lysestagen; saa skinner det for alle dem, som ere i Huset.
Mutane ba za su kunna fitila su sa ta karkashin kwando ba, sai ko a dora ta a mazaunin ta, domin ta ba da haske ga kowa da ke gidan.
16 Lader saaledes eders Lys skinne for Menneskene, at de maa se eders gode Gerninger og ære eders Fader, som er i Himlene.
Bari hasken ku ya haskaka gaban mutane yadda za su ga kyawawan ayyukanku su kuma yabi Ubanku da ke cikin sama.
17 Mener ikke, at jeg er kommen for at nedbryde Loven eller Profeterne; jeg er ikke kommen for at nedbryde, men for at fuldkomme.
Kada ku yi tsammanin na zo ne domin in rushe shari'a ko annabawa. Ban zo domin in rushe su ba, amma domin in cika su.
18 Thi sandelig, siger jeg eder, indtil Himmelen og Jorden forgaar, skal end ikke det mindste Bogstav eller en Tøddel forgaa af Loven, indtil det er sket alt sammen.
Domin gaskiya ina gaya maku, har sama da kasa su shude, amma digo ko wasali daya ba za ya shude ba a cikin shari'ar, sai an cika dukan al'amura.
19 Derfor, den, som bryder et af de mindste af disse Bud og lærer Menneskene saaledes, han skal kaldes den mindste i Himmeriges Rige; men den, som gør dem og lærer dem, han skal kaldes stor i Himmeriges Rige.
Saboda haka duk wanda ya karya mafi kankanta daga cikin dokokin nan ko kuwa ya koya wa wasu su yi haka, za a kira shi mafi kankanta a cikin mulkin sama. Amma dukan wanda ya kiyaye su ko kuwa ya koyar da su, za a kira shi mafi girma a cikin mulkin sama.
20 Thi jeg siger eder: Uden eders Retfærdighed overgaar de skriftkloges og Farisæernes, komme I ingenlunde ind i Himmeriges Rige.
Gama ina gaya maku cewa idan adalcin ku bai zarce adalcin marubuta da Farisawa ba, babu yadda za ku shiga mulkin sama.
21 I have hørt, at der er sagt til de gamle: Du maa ikke slaa ihjel, men den, som slaar ihjel, skal være skyldig for Dommen.
Kun ji dai an ce wa mutanen da, 'Kada ka yi kisan kai,' kuma 'Duk wanda ya yi kisan kai yana cikin hatsarin hukunci.'
22 Men jeg siger eder, at hver den, som bliver vred paa sin Broder uden Aarsag, skal være skyldig for Dommen; og den, som siger til sin Broder: Raka! skal være skyldig for Raadet; og den, som siger: Du Daare! skal være skyldig til Helvedes Ild. (Geenna g1067)
Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da dan'uwansa, yana cikin hatsarin hukunci. Kuma duk wanda ya ce da dan'uwansa, 'Kai mutumin banza!' yana cikin hatsarin tsayawa gaban majalisa, kowa kuma ya ce da dan'uwan sa 'Kai wawa!' yana cikin hatsarin shiga wutar jahannama. (Geenna g1067)
23 Derfor, naar du ofrer din Gave paa Alteret og der kommer i Hu, at din Broder har noget imod dig,
Saboda haka idan za ka yi baiko a bagadi sai ka tuna cewa dan'uwanka yana da damuwa da kai,
24 saa lad din Gave blive der foran Alteret, og gaa hen, forlig dig først med din Broder, og kom da og offer din Gave!
ka bar baikon ka a gaban bagadin, ka yi tafiyarka. Da farko dai, ka sasanta da dan'uwanka kafin ka zo ka mika baikon.
25 Vær velvillig mod din Modpart uden Tøven, medens du er med ham paa Vejen, for at Modparten ikke skal overgive dig til Dommeren, og Dommeren til Tjeneren, og du skal kastes i Fængsel.
Ka yi sulhu da mai karar ka tun kana hanyar zuwa gaban shari'a, domin kada mai karar ka ya mika ka ga alkali, alkali kuwa ya mika ka ga dogarai, za a kuwa jefa ka a kurkuku.
26 Sandelig, siger jeg dig, du skal ingenlunde komme ud derfra, førend du faar betalt den sidste Hvid.
Gaskiya ina gaya maka, ba za ka taba fita daga can ba sai ko ka biya dukan kudin da ya ke binka.
27 I have hørt, at der er sagt: Du maa ikke bedrive Hor.
Kun dai ji an ce, 'Kada ka yi zina'.
28 Men jeg siger eder, at hver den, som ser paa en Kvinde for at begære hende, har allerede bedrevet Hor med hende i sit Hjerte.
Amma ina gaya maku, duk wanda ya dubi mace, da muguwar sha'awa, ya riga ya yi zina da ita a zuciyarsa.
29 Men dersom dit højre Øje forarger dig, saa riv det ud, og kast det fra dig; thi det er bedre for dig, at eet af dine Lemmer fordærves, end at hele dit Legeme bliver kastet i Helvede. (Geenna g1067)
Idan idonka na dama zai sa ka tuntube, kwakule shi ka jefar daga gareka. Don gara daya daga cikin gabobinka ya halaka, da a jefa dukan jikin ka a jahannama. (Geenna g1067)
30 Og om din højre Haand forarger dig, saa hug den af og kast den fra dig; thi det er bedre for dig, at eet af dine Lemmer fordærves, end at hele dit Legeme kommer i Helvede. (Geenna g1067)
Ko kuwa idan hannunka na dama zai sa ka tuntube, ka yanke shi ka jefar daga gare ka. Domin gara daya daga cikin gabobin ka ya halaka, da a jefa dukan jikinka a jahannama. (Geenna g1067)
31 Og der er sagt: Den, som skiller sig fra sin Hustru, skal give hende et Skilsmissebrev.
An sake fada, 'Duk wanda ya kori matarsa, sai ya ba ta takaddar saki.'
32 Men jeg siger eder, at enhver, som skiller sig fra sin Hustru, uden for Hors Skyld, gør, at hun bedriver Hor, og den, som tager en fraskilt Kvinde til Ægte, bedriver Hor.
Amma ina gaya maku ko wa ya saki matarsa, idan ba a kan laifin lalata ba, ya mai da ita mazinaciya kenan. Kuma duk wanda ya aure ta bayan sakin, ya yi zina kenan.
33 I have fremdeles hørt, at der er sagt til de gamle: Du maa ikke gøre nogen falsk Ed, men du skal holde Herren dine Eder.
Kun sake ji an ce wa wadan da suke a zamanin da, 'Kada ku yi rantsuwar karya, amma ku yi rantsuwar ku ga Ubangiji.'
34 Men jeg siger eder, at I maa aldeles ikke sværge, hverken ved Himmelen, thi den er Guds Trone,
Amma ina gaya maku, kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama domin kursuyin Allah ne;
35 ej heller ved Jorden, thi den er hans Fodskammel, ej heller ved Jerusalem, thi det er den store Konges Stad.
ko kuwa da duniya, domin mazaunin kafafunsa ne, ko da Urushalima, domin birnin babban sarki ne.
36 Du maa heller ikke sværge ved dit Hoved, thi du kan ikke gøre et eneste Haar hvidt eller sort.
Ko ma ace ku yi rantsuwa da kanku, domin ba za ku iya mai da gashin kanku baki ko fari ba.
37 Men eders Tale skal være ja, ja, nej, nej; hvad der er ud over dette, er af det onde.
Amma bari maganarku ta zama 'I, I', ko kuwa 'A'a, a'a.' Duk abin da ya wuce wannan, daga mugun yake.
38 I have hørt, at der er sagt: Øje for Øje, og Tand for Tand.
Kun dai ji an ce, “Ido a maimakon ido, hakori kuma a maimakon hakori.'
39 Men jeg siger eder, at I maa ikke sætte eder imod det onde; men dersom nogen giver dig et Slag paa din højre Kind, da vend ham ogsaa den anden til!
Amma ina gaya maku, kada ku yi jayayya da wanda ke mugu, a maimakon haka, ko wa ya mare ku a kuncin dama, ku juya masa dayan ma.
40 Og dersom nogen vil gaa i Rette med dig og tage din Kjortel, lad ham da ogsaa faa Kappen!
Idan wani yana da niyyar kai kararku gaban shari'a saboda ya karbi rigarku, ku ba wannan mutumin mayafinku ma.
41 Og dersom nogen tvinger dig til at gaa een Mil, da gaa to med ham!
Duk wanda ya tilasta ku ga tafiyar mil daya, ku je da shi biyu.
42 Giv den, som beder dig, og vend dig ikke fra den, som vil laane af dig.
Ku ba kowa da ya tambaye ku, kuma kada ku hana kowa da ke neman rance a wurinku.
43 I have hørt, at der er sagt: Du skal elske din Næste og hade din Fjende.
Kun ji abin da aka fada, 'Za ka kaunaci makwabcin ka ka ki magabcin ka.'
44 Men jeg siger eder: Elsker eders Fjender, velsigner dem, som forbande eder, gører dem godt, som hade eder, og beder for dem, som krænke eder og forfølge eder,
Amma ina gaya maku, ku kaunaci magabtan ku, ku yi addu'a domin masu tsananta maku, ku albarkaci wadanda suka la'ance ku, ku yi alheri ga wadanda suke kin ku,
45 for at I maa vorde eders Faders Børn, han, som er i Himlene; thi han lader sin Sol opgaa over onde og gode og lader det regne over retfærdige og uretfærdige.
domin ku zama 'ya'yan Ubanku da ke cikin sama. Domin yakan sa rana ta haskaka wa mugu da mutumin kirki, kuma yakan aiko da ruwan sama ga adali da azzalumi.
46 Thi dersom I elske dem, som elske eder, hvad Løn have I da? Gøre ikke ogsaa Tolderne det samme?
Domin idan kuna kaunar wadanda suke kaunarku, wanne lada kuka samu? Ba haka masu karban haraji ma suke yi ba?
47 Og dersom I hilse eders Brødre alene, hvad stort gøre I da? Gøre ikke ogsaa Hedningerne det samme?
Kuma in kun gaida 'yan'uwanku kadai, me kuke yi fiye da sauran? Ba hakanan al'ummai ma suke yi ba?
48 Værer da I fuldkomne, ligesom eders himmelske Fader er fuldkommen.
Saboda haka, lalle ne ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na sama yake cikakke.

< Matthæus 5 >