< Efeserne 3 >

1 Det er for denne Sags Skyld, at jeg, Paulus, Kristi Jesu Fange for eder, I Hedninger, —
Saboda haka, ni Bulus, dan sarka sabili da Almasihu dominku al'ummai.
2 om I da have hørt om Husholdningen med den Guds Naade, som blev given mig til eder,
Ina zaton kun ji a kan aiki mai girma na alherin Allah da ya ba ni dominku.
3 at ved Aabenbarelse blev Hemmeligheden kundgjort mig, saaledes som jeg foran kortelig har skrevet,
Ina rubuto maku bisa ga wahayin da aka sanashe ni. Wannan ita ce boyayyar gaskiya da na rubuta a takaice a cikin wata wasikar.
4 hvoraf I, naar I læse det, kunne skønne min Indsigt i Kristi Hemmelighed,
Sa'adda kuka karanta a kan wannan, za ku iya fahimtar basira ta cikin boyayyar gaskiya a kan Almasihu.
5 som i andre Slægter ikke blev kundgjort for Menneskenes Børn, saaledes som den nu er bleven aabenbaret hans hellige Apostle og Profeter ved Aanden:
Wanda a zamanun da ba a bayyana wa mutane ba. Amma yanzu an bayyana shi ga manzanni da annabawa kebabbu a cikin Ruhu.
6 Nemlig at Hedningerne ere Medarvinger og medindlemmede og meddelagtige i Forjættelsen i Kristus Jesus ved Evangeliet,
Wannan boyayyar bishara ita ce al'ummai ma abokan gado ne tare da mu, gabobi ne cikin jiki daya. Abokan tarayya ne kuma cikin alkawaran Almasihu Yesu ta wurin bishara.
7 hvis Tjener jeg er bleven ifølge den Guds Naades Gave, som blev given mig ved hans Magts Virkekraft.
Domin wannan na zama bawa ta wurin baiwar alherin Allah da ya bani ta wurin karfin ikonsa.
8 Mig, den allerringeste af alle hellige, blev denne Naade given at forkynde Hedningerne Evangeliet om Kristi uransagelige Rigdom
Allah ne ya ba ni wannan baiwa. Ko da shike nine mafi kankanta cikin kebabbun Allah, in yi shelar bishara ga al'ummai akan wadatar Almasihu marar matuka.
9 og at oplyse alle om, hvilken Husholdningen med den Hemmelighed er, som fra Evighed har været skjult i Gud, der skabte alle Ting, (aiōn g165)
In kuma fahimtar da dukan mutane a kan shirin Allah, wannan boyayyar gaskiya wadda tun zamanai da suka wuce Allah ya boye, shi da ke mahallicin dukan abubuwa. (aiōn g165)
10 for at Guds mangfoldige Visdom skulde nu ved Menigheden blive kundgjort for Magterne og Myndighederne i det himmelske,
Saboda haka, ta wurin ikilisiya, masu iko da masu mulkin sararin sama za su san hikimar Allah ta fuskoki daban daban.
11 efter det evige Forsæt, som han fuldbyrdede ved Kristus Jesus, vor Herre, (aiōn g165)
Wannan ya kasance bisa ga dawwamammen nufi da ya zartar cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu. (aiōn g165)
12 i hvem vi have Frimodigheden og Adgang med Tillid ved Troen paa ham.
Gama a cikin Almasihu muna da gabagadi, da dama, da amincewa sabili da gaskiyar mu a cikinsa.
13 Derfor beder jeg, at I ikke tabe Modet over mine Trængsler, som jeg lider for eder, hvilket er en Ære for eder. —
Saboda haka ina rokon ku kada ku karaya da wahalar da na sha domin ku wadda ta zama daukakar ku.
14 For denne Sags Skyld bøjer jeg mine Knæ for Faderen,
Saboda haka nake durkusawa da gwiwa ta a gaban Uba,
15 fra hvem enhver Faderlighed i Himle og paa Jord har sit Navn,
wanda ta wurinsa ake kiran kowanne iyali na sama da na kasa.
16 at han vil give eder efter sin Herligheds Rigdom mægtigt at styrkes ved hans Aand i det indvortes Menneske;
Ina addu'a ya amince maku bisa ga yalwar wadatar daukakarsa, ku karfafa matuka da iko ta wurin Ruhunsa, da yake cikinku.
17 at Kristus maa bo ved Troen i eders Hjerter,
Ina addu'a Almasihu ya zauna a cikin zuciyar ku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu'a ku kafu ku kuma ginu da zurfi kwarai cikin kaunarsa.
18 for at I, rodfæstede og grundfæstede i Kærlighed, kunne sammen med alle de hellige formaa at begribe, hvor stor Bredden og Længden og Dybden og Højden er,
Ku kasance cikin kaunarsa domin ku gane, tare da dukan masu bi, menene zurfi, da fadi, da tsawon kaunar Almasihu.
19 og at kende Kristi Kærlighed, som overgaar al Erkendelse, for at I kunne fyldes indtil hele Guds Fylde.
Ina addu'a domin ku san mafificiyar kaunar Almasihu da ta wuce sani. Ku yi wannan domin a cika ku da dukan cikar Allah.
20 Men ham, som formaar over alle Ting at gøre langt ud over det, som vi bede eller forstaa, efter den Magt, som er virksom i os,
Yanzu ga wanda yake da ikon aikata dukan abu fiye da abin da muke roko ko tunani, bisa ga ikonsa da ke aiki a cikinmu,
21 ham være Ære i Menigheden og i Kristus Jesus igennem alle Slægterne i Evighedernes Evighed! Amen. (aiōn g165)
daukaka ta tabbata a gare shi a cikin ikilisiya ta wurin Almasihu Yesu har ya zuwa zamanun zamanai har abada abadin. Amin. (aiōn g165)

< Efeserne 3 >