< Anden Kongebog 10 >
1 Og Akab havde halvfjerdsindstyve Sønner i Samaria; og Jehu skrev Breve og sendte til Samaria, til de øverste i Jisreel, de Ældste, og til de af Akab indsatte Fosterfædre og lod sige:
To, akwai’ya’ya maza saba’in na gidan Ahab a Samariya. Saboda haka Yehu ya rubuta wasiƙu, ya aika su Samariya, zuwa ga shugabannin Yezireyel, da kuma ga masu lura da’ya’yan Ahab. Ya ce,
2 Og nu, naar dette Brev kommer til eder — efterdi eders Herres Sønner ere hos eder, og Vognene ere hos eder og Hestene, samt en fast Stad og Vaabnene —
“Da zarar wasiƙan nan ta sadu da ku, da yake’ya’yan maigidanku suna tare da ku, kuna kuma da kekunan yaƙi da dawakai, da birni mai katanga da makamai,
3 saa ser, hvem der er den bedste og den rette af eders Herres Sønner, og sætter ham paa hans Faders Trone og strider for eders Herres Hus!
sai ku zaɓi mafi cancanta a cikin’ya’yan maigidanku ku sa shi a kan kursiyin mahaifinsa. Sa’an nan ku yi yaƙi don gidan maigidanku.”
4 Men de frygtede saare meget og sagde: se, de to Konger kunde ikke staa sig for hans Ansigt, hvorledes ville vi da kunne staa os?
Amma suka razana suka ce, “Idan sarakuna biyu ba su iya yin tsayayya da shi ba, wane mu?”
5 Og den, som var over Huset og den, som var over Staden, og de Ældste og Fosterfædrene sendte til Jehu og lode sige: Vi ere dine Tjenere, vi ville gøre alt det, som du siger til os, vi ville ingen gøre til Konge; gør det, som dig synes godt.
Saboda haka sarkin fada, da gwamnan birnin, da dattawa, da kuma masu lura da’ya’yan suka aika da saƙo ga Yehu, cewa, “Mu bayinka ne, za mu kuma yi duk abin da ka ce. Ba za mu naɗa kowa sarki ba; sai ka yi abin da ka ga ya fi kyau.”
6 Da skrev han et andet Brev til dem og lod sige: Dersom I ere mine og høre min Røst, saa tager Hovederne af Mændene, eders Herres Sønner, og kommer til mig i Morgen ved denne Tid til Jisreel. Men Kongens Sønner, halvfjerdsindstyve Mænd, vare hos de store i Staden, som fødte dem op.
Sai Yehu ya sāke rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “In a gefena kuke, to, sai ku yi biyayya da ni, ku fille kawunan’ya’yan maigidanku, ku kawo mini a Yezireyel war haka gobe.” To,’ya’yan sarki, su saba’in, suna tare da manyan birni waɗanda suke lura da su.
7 Og det skete, der Brevet kom til dem, da toge de Kongens Sønner og slagtede dem, halvfjerdsindstyve Mænd, og lagde deres Hoveder i Kurve og sendte dem til ham i Jisreel.
Sa’ad da wasiƙar ta iso, sai mutanen nan suka ɗauki dukan’ya’yan sarkin nan saba’in, suka kashe su, suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezireyel.
8 Og der Budet kom og gav ham det til Kende og sagde: De have bragt Kongens Sønners Hoveder hid, da sagde han: Lægger dem i to Hobe ved Indgangen til Porten indtil i Morgen!
Da ɗan saƙon ya iso, sai aka ce wa Yehu, “Sun kawo kawunan’ya’yan sarki.” Sai Yehu ya ce, “Ku ajiye su kashi biyu a ƙofar gari har safiya.”
9 Og det skete om Morgenen, der han gik ud og stod der, da sagde han til alt Folket: I ere retfærdige! se, jeg har gjort et Forbund imod min Herre og slaaet ham ihjel; men hvo har slaget alle disse?
Da gari ya waye, sai Yehu ya fita ya tsaya a gaban dukan jama’a ya ce, “Ba ku da laifi. Ni ne na ƙulla wa maigidana maƙarƙashiya, na kuma kashe shi, amma wa ya karkashe dukan waɗannan?
10 Vider nu, at der er ikke eet af Herrens Ord, som Herren har talt over Akabs Hus, faldet til Jorden; thi Herren har gjort, som han talte ved sin Tjener Elias.
Ku sani fa, ba kalmar da Ubangiji ya faɗa game da gidan Ahab da ba za tă cika ba. Ubangiji ya yi abin da ya alkawarta ta bakin bawansa Iliya.”
11 Saa ihjelslog Jehu alle, som vare overblevne af Akabs Hus i Jisreel og alle hans store Mænd og hans Kyndinger og hans Præster, indtil han ikke levnede ham een tilovers.
Saboda haka Yehu ya kashe duk waɗanda suka rage na iyalin Ahab a Yezireyel, tare da dukan fadawansa da aminansa da firistocinsa, ba a bar masa kowa ba.
12 Og han gjorde sig rede og drog hen og kom til Samaria. Og der han var ved Hyrdernes Beth-Eked paa Vejen,
Sa’an nan Yehu ya nufi Samariya. Da ya kai Bet-Eked na Makiyaya,
13 da traf Jehu paa Ahasias, Judas Konges, Brødre og sagde: Hvem ere I? og de sagde: Vi ere Ahasias Brødre og fare ned for at hilse paa Kongens Børn og Dronningens Børn.
sai ya gamu da waɗansu daga dangin Ahaziya sarkin Yahuda, sai ya tambaye su, ya ce, “Ku, su wane ne?” Suka ce, “Mu dangin Ahaziya ne, mun kuma zo ne mu gai da iyalan sarki da kuma mahaifiyar sarauniya.”
14 Da sagde han: Griber dem levende, og de grebe dem levende; og de slagtede dem ved Grøften ved Beth-Eked, to og fyrretyve Mænd, og man lod ikke een Mand blive tilovers af dem.
Sai ya umarta ya ce, “A kama su da rai!” Aka kuwa kama su aka yayyanka kusa da rijiyar Bet-Eked, su arba’in da biyu. Ba a bar wani da rai ba.
15 Og der han drog derfra, da traf han Jonadab, Rekabs Søn, som mødte ham og velsignede ham, og han sagde til ham: Mon dit Hjerte er oprigtigt, som mit Hjerte imod dit Hjerte? og Jonadab sagde: Det er. Er det saa, da giv mig din Haand; og han gav ham sin Haand, og han lod ham stige op til sig i Vognen.
Bayan ya bar wurin, sai ya gamu da Yehonadab ɗan Rekab wanda yake kan hanyarsa don yă sadu da shi. Sai Yehu ya gaishe shi, ya ce, “Ka amince da ni yadda na amince da kai?” Yehonadab ya ce, “I.” Yehu ya ce, “To, in haka ne ka ba ni hannunka.” Sai ya miƙa masa, Yehu kuwa ya ja shi cikin keken yaƙin.
16 Og han sagde: Gak med mig, og se paa min Nidkærhed for Herren; og de kørte ham paa hans Vogn.
Yehu ya ce, “Zo tare da ni ka ga himmata saboda Ubangiji.” Sa’an nan ya sa suka tafi tare cikin keken yaƙinsa.
17 Og der han kom til Samaria, da slog han alle ihjel, som vare overblevne af Akabs i Samaria, indtil han havde ødelagt ham, efter Herrens Ord, som han talte til Elias.
Da Yehu ya isa Samariya, sai ya karkashe dukan sauran iyalin Ahab, ya hallaka su, bisa ga maganar da Ubangiji ya faɗa ta bakin Iliya.
18 Og Jehu samlede alt Folket og sagde til dem: Akab tjente Baal lidet; Jehu vil tjene ham meget.
Sa’an nan Yehu ya tattara dukan jama’a ya ce musu, “Ahab ya bauta wa Ba’al kaɗan ne kawai; amma Yehu zai bauta masa sosai.
19 Saa kalder nu alle Baals Profeter, alle hans Tjenere og alle hans Præster til mig, at ingen savnes, thi jeg har et stort Slagtoffer for til Baal, hvo som savnes, skal ikke leve; men Jehu gjorde det med Svig, at han kunde ødelægge Baals Tjenere.
Yanzu sai ku kira dukan annabawan Ba’al, dukan masu yin masa hidima da kuma dukan firistocinsa. Ku tabbata ba a manta da wani ba, gama zan yi wa Ba’al babbar hadaya. Duk wanda bai zo ba, a bakin ransa.” Amma Yehu yana wayo ne domin yă hallaka masu yi wa Ba’al sujada.
20 Og Jehu sagde: Helliger Baal en Højtidsdag; og de udraabte den.
Yehu ya ce, “Ku kira jama’a don a girmama Ba’al.” Saboda haka suka yi shela.
21 Og Jehu sendte til hele Israel, og alle Baals Tjenere kom, og ingen blev tilbage, som ej kom; og de kom i Baals Hus, at Baals Hus blev fuldt her og der.
Sa’an nan ya aika saƙo ko’ina a Isra’ila, dukan masu yi wa Ba’al hidima kuwa suka tattaru, ba mutumin da bai zo ba. Suka yi cincirindo a haikalin Ba’al har sai da ya cika makil.
22 Da sagde han til dem, som vare over Klædekammeret: Bærer Klæder ud til alle Baals Tjenere; og man bar Klæderne ud til dem.
Sai Yehu ya ce wa mai ajiyar tufafi, “Ka kawo riguna domin dukan masu yi wa Ba’al hidima.” Sai ya fito musu da riguna.
23 Og Jehu og Jonadab, Rekabs Søn, gik ind i Baals Hus; og han sagde til Baals Tjenere: Ransager og ser til, at her ikke er nogen af Herrens Tjenere iblandt eder, men alene Baals Tjenere.
Sa’an nan Yehu da Yehonadab ɗan Rekab, suka shiga haikalin Ba’al. Yehu ya ce wa masu yi wa Ba’al sujada, “Ku dudduba ku tabbatar cewa babu wani bawan Ubangiji a nan tare da ku, sai masu hidimar Ba’al kawai.”
24 Og der de gik ind til at gøre Slagtofre og Brændofre, da beskikkede Jehu sig firsindstyve Mænd udenfor og sagde: Dersom nogen af de Mænd skulde undkomme, som jeg har ført hid under eders Hænder, da skal der bødes med Liv for Liv.
Saboda haka suka shiga don su miƙa hadayu da kuma hadaya ta ƙonawa. To, Yehu ya riga ya ba wa mutane takwas wannan kashedi a waje cewa, “In waninku ya bar ɗaya daga cikin mutanen nan da nake danƙa a hannunku ya tsere, to, a bakin ransa.”
25 Og det skete, der man var færdig med at bringe Brændofferet, da sagde Jehu til Drabanterne og Høvedsmændene: Gaar ind, slaar dem, ingen maa komme ud; og de sloge dem med skarpe Sværd, og Drabanterne og Høvedsmændene kastede dem hen, og de gik til Baals Hus's Stad.
Nan da nan sa’ad da Yehu ya gama yin hadayar, sai ya umarci masu gadin da hafsoshi, “Ku shiga ku karkashe su; kada ku bar wani yă tsere.” Saboda haka suka karkashe su da takobi. Masu gadin da hafsoshin suka wuwwurga gawawwakinsu waje, suka kuma shiga ciki cikin haikalin Ba’al ɗin,
26 Og de bare Støtterne af Baals Hus ud og opbrændte dem.
suka fitar da dutsen tsafi daga haikalin Ba’al, suka kuma ƙone shi.
27 Og de nedbrøde Baals Støtte og nedbrøde Baals Hus og gjorde et hemmeligt Mag deraf indtil denne Dag.
Suka farfasa dutsen tsafin Ba’al, suka kuma rushe haikalin, mutane suka mai da wurin salga har yă zuwa yau.
28 Saa ødelagde Jehu Baal af Israel.
Ta haka Yehu ya hallaka butar Ba’al a Isra’ila.
29 Dog fra Jeroboams, Nebats Søns, Synder, som kom Israel til at synde, dem veg Jehu ikke fra, nemlig fra de Guldkalve, den som var i Bethel, og den som var i Dan.
Duk da haka, bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata ba, wato, yin sujada ga siffofin maruƙa na zinariya a Betel da kuma Dan.
30 Og Herren sagde til Jehu: Fordi du fuldkommelig har gjort det, som er ret for mine Øjne, og har gjort imod Akabs Hus efter alt det, som var i mit Hjerte, da skulle dine Sønner i fjerde Led sidde paa Israels Trone.
Ubangiji ya ce wa Yehu, “Tun da yake ka aikata abin da yake mai kyau a idanuna, ka kuma yi wa gidan Ahab dukan abin da yake a zuciyata, ina yin maka alkawari cewa zuriyarka za su yi mulkin Isra’ila har tsara ta huɗu.”
31 Dog tog Jehu ikke Vare paa at vandre i Herrens, Israels Guds, Lov af sit ganske Hjerte; han veg ikke fra Jeroboams Synder, med hvilke han kom Israel til at synde.
Duk da haka, Yehu bai mai da hankali ya kiyaye dokokin Ubangiji, Allah na Isra’ila da dukan zuciyarsa ba. Bai rabu da zunubin Yerobowam, wanda ya sa Isra’ila ta aikata ba.
32 I de samme Dage begyndte Herren at tage Stykker bort af Israel; thi Hasael slog dem i hele Israels Landemærke,
A kwanakin sai Ubangiji ya fara rage girman Isra’ila, Hazayel ya yi nasara a bisa Isra’ila a ko’ina a yankinsu
33 fra Jordan af, imod Solens Opgang, det hele Gileads Land, Gaditerne og Rubeniterne og Manassiterne, fra Aroer, som er ved Arnons Bæk, baade Gilead og Basan.
gabas da Urdun, cikin dukan ƙasar Gileyad (yankin Gad, da na Ruben, da na Manasse), daga Arower wajen Kwarin Arnon ya ratsa Gileyad zuwa Bashan.
34 Men det øvrige af Jehus Handeler, og alt det, han har gjort, og al hans Vælde, ere de Ting ikke skrevne i Israels Kongers Krønikers Bog?
Game da sauran ayyukan mulkin Yehu, da dukan abin da ya yi, a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
35 Og Jehu laa med sine Fædre, og de begravede ham i Samaria, og Joahas, hans Søn, blev Konge i hans Sted.
Yehu ya huta tare da kakanninsa, aka binne shi a Samariya. Yehoyahaz kuma ya ci sarauta bayansa.
36 Og de Aar, som Jehu regerede over Israel i Samaria, vare otte og tyve Aar.
Yehu ya yi sarautar Isra’ila a Samariya shekara ashirin da takwas.