< 2 Korinterne 8 >
1 Men vi kundgøre eder, Brødre! den Guds Naade, som er given i Makedoniens Menigheder,
Muna so ku sani, 'yan'uwa, game da alherin Allah da aka bayar ga Ikkilisiyoyin Makidoniya.
2 at under megen Trængsels Prøvelse har deres overstrømmende Glæde og deres dybe Fattigdom strømmet over i deres Gavmildheds Rigdom.
A lokacin babban gwajin wahala, yalwar farincikinsu da tsananin talaucinsu ya haifar da yalwar bayarwa hannu sake.
3 Thi efter Evne (det vidner jeg) gave de, ja, over Evne, af egen Drift,
Domin ina shaida, sun yi bayarwa iya kokarinsu, fiye da abinda ma suke iyawa. Cikin yaddar ransu
4 idet de med megen Overtalelse bade os om den Naade at maatte tage Del i Hjælpen til de hellige,
da roko mai yawa suka nace da a ba su zarafi su yi tarayya a wannan hidima ga masu bi.
5 og ikke alene som vi havde haabet, men sig selv gav de først og fremmest til Herren og saa til os, ved Guds Villie,
Haka ya auku ba kamar yadda muka yi zato ba. A Maimakon haka, sai da suka fara bada kansu ga Ubangiji. Kuma suka bada kansu gare mu bisa ga nufin Allah.
6 saa at vi opfordrede Titus til, ligesom han forhen havde begyndt, saaledes ogsaa at tilendebringe hos eder ogsaa denne Gave.
Sai muka karfafa Titus, wanda ya rigaya ya fara wannan aiki, domin ya kammala wannan aiki na bayarwa ta fannin ku.
7 Men ligesom I ere rige i alt, i Tro og Tale og Erkendelse og al Iver og i eders Kærlighed til os: Maatte I da være rige ogsaa i denne Gave!
Amma kun habaka cikin komai-cikin bangaskiya, cikin magana, cikin sani, cikin aiki tukuru, cikin kaunarku dominmu. Don haka, ku tabbata kun habaka a wannan aiki na bayarwa.
8 Jeg siger det ikke som en Befaling, men for ved andres Iver at prøve ogsaa eders Kærligheds Ægthed.
Na fadi haka ne ba kamar ina umurtar ku ba. A maimakon haka, na fadi haka ne in gwada sahihancin kaunarku ta wurin kwatanta ta da himmar sauran mutane.
9 I kende jo vor Herres Jesu Kristi Naade, at han for eders Skyld blev fattig, da han var rig, for at I ved hans Fattigdom skulde blive rige.
Domin kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu. Kodashike shi mai arziki ne, amma ya zama matalauci, domin ta wurin talaucinsa ku yi arziki.
10 Og jeg giver min Mening herom til Kende; thi dette er eder gavnligt, I, som jo i Fjor vare de første til at begynde, ikke alene med Gerningen, men endogsaa med Villien dertil.
A wannan al'amari zan ba ku shawarar da za ta taimake ku. Shekarar da ta wuce, ba fara wani abu kawai kuka yi ba, amma kun yi marmarin ku yi shi.
11 Men fuldbringer da nu ogsaa Gerningen, for at, ligesom I vare redebonne til at ville, I ogsaa maa fuldbringe det efter eders Evne.
Yanzu ku kammala shi. Kamar yadda kuke da niyya da marmarin yin haka a lokacin, bari ku yi kokari ku kawo shi ga kammalawa iyakar iyawar ku.
12 Thi naar Redebonheden er til Stede, da er den velbehagelig efter, hvad den evner, ikke efter, hvad den ikke evner.
Idan kuna niyya ku yi wannan aiki, abu mai kyau ne karbabbe kuma. Tabbas ya zama dai-dai da abinda mutum ke da shi, ba abinda ba ya da shi ba.
13 Det er nemlig ikke Meningen, at andre skulle have Lettelse og I Trængsel; nej, det skal være ligeligt. Nu for Tiden maa eders Overflod komme hines Trang til Hjælp,
Domin wannan aiki ba domin a nawaita maku sannan wadansu su samu sauki ba ne. A maimakon haka, ya kamata a sami daidaituwa.
14 for at ogsaa hines Overflod kan komme eders Trang til Hjælp, for at der kan blive Ligelighed,
Yalwar ku a wannan lokaci za ta zama abin biyan bukatarsu. Haka nan kuma domin yalwar su ta iya biyan bukatarku, domin a sami daidaituwa.
15 som der er skrevet: „Den, som sankede meget, fik ikke for meget, og den, som sankede lidet, fik ikke for lidt.‟
Yana nan kamar yadda aka rubuta: “Wanda ke da shi dayawa bai samu raguwar komai ba, kuma wanda yake da kadan bai rasa komai ba.”
16 Men Gud ske Tak, som giver den samme Iver for eder i Titus's Hjerte!
Amma godiya ga Allah, da yasa a zuciyar Titus marmarin kulawa da ku kamar wadda nake da ita domin ku.
17 Thi vel har han modtaget min Opfordring; men da han er saa ivrig, saa er det af egen Drift, at han rejser til eder.
Gama ba rokon mu kadai ya karba ba, amma ya yi da gaske akan haka. Ya zo gare ku ne da yardar kan sa.
18 Og sammen med ham sende vi den Broder, hvis Ros i Evangeliet gaar igennem alle Menighederne,
Mun aiko tare da shi dan'uwa da ake yaba masa a tsakanin dukan Ikkilisiyoyi domin ayyukansa a cikin shelar bishara.
19 og ikke det alene, men han er ogsaa udvalgt af Menederne til at rejse med os med denne Gave, som besørges af os, for at fremme selve Herrens Ære og vor Redebonhed,
Ba domin wannan kadai ba, amma Ikkilisiyoyi ne suka zabe shi ya tafi tare da mu a cikin yin wannan hidima ta alheri. Wannan domin girmama Ubangiji ne kansa da kuma domin aniyarmu ta taimakawa.
20 idet vi undgaa dette, at nogen skulde kunne laste os i Anledning af denne rige Hjælp, som besørges af os;
Muna gudun kada kowa ya sa mana laifi game da wannan alheri da muke dauke da shi.
21 thi vi lægge Vind paa, hvad der er godt ikke alene i Herrens, men ogsaa i Menneskers Øjne.
Niyyar mu ce mu yi kyakkyawan abu, ba a gaban Ubangiji kadai ba, amma a gaban mutane ma.
22 Men sammen med dem sende vi vor Broder, hvis Iver vi ofte i mange Maader have prøvet, men som nu er langt ivrigere paa Grund af sin store Tillid til eder.
Mun kuma aiki wani dan'uwan tare da su. Mun sha gwada shi, kuma mun same shi da himma wajen ayyuka da dama. Yanzu kuma ya kara himma, saboda amincewa mai girma da yake da ita gare ku.
23 Hvad Titus angaar, da er han min Fælle og Medarbejder hos eder, og hvad vore Brødre angaar, da ere de Menighedsudsendinge, Kristi Ære.
Game da Titus, shi abokin tafiyata ne, kuma abokin aikina domin ku. Game da yan'uwanmu, an aiko su ne daga Ikkilisiyoyi. Su kuwa daraja ne ga Almasihu.
24 Saa giver dem da for Menighedernes Aasyn Beviset paa eders Kærlighed og for det, vi have rost eder for.
Don haka, ku nuna masu kaunarku, ku kuma nuna wa Ikilisiyoyi dalilin fahariyarmu game da ku.