< Zjevení Janovo 20 >
1 I viděl jsem anděla sstupujícího s nebe, majícího klíč od propasti a řetěz veliký v ruce své. (Abyssos )
Na kuma ga wani mala’ika yana saukowa daga sama, yana da mabuɗin Abis yana kuma riƙe da ƙaton sarƙa a hannunsa. (Abyssos )
2 I chopil draka, hada toho starého, jenž jest ďábel a satan, i svázal jej za tisíc let.
Ya kama macijin, wannan tsohon maciji, wanda yake shi ne Iblis, ko kuwa Shaiɗan, aka kuma ɗaura shi har shekara dubu.
3 A uvrhl ho do propasti, i zavřel jej tam a svrchu nad ním zapečetil, aby nesvodil více národů, až by se vyplnilo tisíc let; neboť potom musí býti propuštěn na malý čas. (Abyssos )
Ya jefa shi cikin Abis, ya kuma kulle ya sa hatimi a kansa, don a hana kada yă ƙara ruɗin al’ummai, sai shekarun nan dubu sun cika. Bayan wannan, dole a sake shi na ɗan lokaci. (Abyssos )
4 I viděl jsem stolice, a posadili se na nich, i dán jest jim soud, a viděl jsem duše stínaných pro svědectví Ježíšovo a pro slovo Boží, a kteříž se neklaněli šelmě, ani obrazu jejímu, a aniž přijali znamení jejího na čela svá, anebo na ruce své. A ožili a kralovali s Kristem tisíc let.
Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu.
5 Jiní pak mrtví neožili, dokudž by se nevyplnilo tisíc let. A toť jest první vzkříšení.
(Sauran matattu ba su sāke rayuwa ba, sai da shekaru dubun nan suka cika.) Wannan fa shi ne tashin matattu na farko.
6 Blahoslavený a svatý, kdož má díl v prvním vzkříšení. Nad těmiť ta druhá smrt nemá moci, ale budou kněží Boží a Kristovi, a kralovati s ním budou tisíc let.
Masu albarka da kuma tsarki ne waɗanda suke da rabo a tashin matattu na farko. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kansu, sai dai za su zama firistocin Allah da kuma na Kiristi za su kuma yi mulki tare da shi na shekaru dubu.
7 A když se vyplní tisíc let, propuštěn bude satanáš z žaláře svého.
Sa’ad da shekaru dubun nan suka cika, za a saki Shaiɗan daga kurkukun da yake,
8 I vyjde, aby svodil národy, kteříž jsou na čtyřech stranách země, Goga a Magoga, a aby je shromáždil k boji, kterýchžto počet jest jako písku mořského.
zai kuma fito don yă ruɗi al’ummai da suke a kursuyoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, yă tattara su don yaƙi. Yawansu kuwa ya yi kamar yashi a bakin teku.
9 I vstoupili na širokost země a obklíčili stany svatých, i to město milé, ale sstoupil oheň od Boha s nebe a spálil je.
Suka mamaye duk fāɗin duniya suka kuma kewaye sansanin mutanen Allah, birnin da yake ƙauna. Amma wuta ta fito daga sama ta cinye su.
10 A ďábel, kterýž je svodil, uvržen jest do jezera ohně a síry, kdež jest i šelma, i falešný prorok, a budouť mučeni dnem i nocí na věky věků. (aiōn , Limnē Pyr )
Aka jefa Iblis da ya ruɗe su cikin tafkin farar wuta, inda aka jefa dabban nan da annabin ƙaryan nan. Za a ba su azaba dare da rana har abada abadin. (aiōn , Limnē Pyr )
11 I viděl jsem trůn veliký bílý, a sedícího na něm, před jehož tváří utekla země i nebe, a místo jim není nalezeno.
Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu.
12 I viděl jsem mrtvé, malé i veliké, stojící před obličejem Božím, a knihy otevříny jsou. A jiné knihy také jsou otevříny, to jest knihy života, i souzeni jsou mrtví podle toho, jakž psáno bylo v knihách, totiž podle skutků svých.
Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai.
13 A vydalo moře mrtvé, kteříž byli v něm, tolikéž smrt i peklo vydali ty, kteříž v nich byli, i souzeni jsou jeden každý podle skutků svých. (Hadēs )
Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata. (Hadēs )
14 Smrt pak a peklo uvrženi jsou do jezera ohnivého, a toť jest smrt druhá. (Hadēs , Limnē Pyr )
Sa’an nan aka jefar da mutuwa da kuma Hades cikin tafkin wuta. Tafkin wutar nan kuwa shi ne mutuwa ta biyu. (Hadēs , Limnē Pyr )
15 I ten, kdož není nalezen v knihách života, uvržen jest do jezera ohnivého. (Limnē Pyr )
Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan. (Limnē Pyr )