< Efezským 5 >
1 Buďtež tedy následovníci Boží, jakožto synové milí.
Saboda haka ku zama masu koyi da Allah, kamar kaunatattun 'ya'yansa.
2 A choďtež v lásce, jakož i Kristus miloval nás, a vydal sebe samého za nás, dar a obět Bohu u vůni rozkošnou.
Ku yi zama cikin kauna kamar yadda Almasihu ya kaunace mu, ya kuma mika kansa sadaka da hadaya ga Allah dominmu, hadaya mai kanshi abin karba ga Allah.
3 Smilstvo pak a všeliká nečistota, neb lakomství, aniž jmenováno buď mezi vámi, jakož sluší na svaté,
Fasikanci ko kowacce irin kazamta, ko kazamar lalata kada a ambace su a tsakaninku, don haka ya dace ga masu bi.
4 A tolikéž mrzkost, ani bláznové mluvení, ani šprýmování, kteréžto věci jsou nenáležité, ale raději ať jest díků činění.
Kada a ambaci batsa, maganar wauta ko alfasha wadanda ba su dace ba. Maimakon haka, mu zama masu godiya.
5 Víte zajisté o tom, že žádný smilník aneb nečistý, ani lakomec, (jenž jest modloslužebník, ) nemá dědictví v království Kristově a Božím.
Domin wannan kun sani cewa ba fasiki, ko mara tsarki, ko mai hadama wato mai bautar gumaka zai sami gado cikin mulkin Almasihu da Allah.
6 Žádný vás nesvoď marnými řečmi; nebo pro takové věci přichází hněv Boží na syny nepoddané.
Kada kowa ya rude ku da maganganun wofi. Saboda wadannan abubuwa ne fushin Allah ke zuwa kan kangararrun 'ya'ya.
7 Nebývejtež tedy účastníci jejich.
Kada ku yi tarayya tare da su.
8 Byli jste zajisté někdy temnosti, ale již nyní jste světlo v Pánu. Jakožto synové světla choďte,
Domin da ku duhu ne, amma yanzu ku haske ne cikin Ubangiji. Sai ku yi tafiya kamar 'ya'yan haske.
9 (Nebo ovoce Ducha záleží ve vší dobrotě, a spravedlnosti, a v pravdě, )
Saboda amfanin haske shine dukan alheri, adalci da gaskiya.
10 O to stojíce, což by se dobře líbilo Pánu.
Kuna bidar abin da Ubangiji ke murna da shi.
11 A neobcujte s skutky neužitečnými tmy, ale raději je trescete.
Kada ku sa hannu ga ayyuka marasa amfani da ayyukan duhu amma gara a tone su.
12 Nebo což se tajně děje od nich, mrzko jest o tom i mluviti.
Don abubuwan da suke yi a boye abin kunya ne a bayyana su.
13 Všecko pak, což bývá trestáno, od světla bývá zjeveno; nebo to, což všecko zjevuje, světlo jest.
Dukan abu, idan haske ya bayyana su, za a gan su.
14 Protož praví: Probuď se ty, jenž spíš, a vstaň z mrtvých, a zasvítíť se tobě Kristus.
Domin duk abin da aka bayyana ya zama haske. Saboda haka aka ce, “Ka farka, kai mai barci, ka tashi daga cikin matattu; Almasihu kuwa zai haskaka bisanka”.
15 Viztež tedy, kterak byste opatrně chodili, ne jako nemoudří, ale jako moudří,
Saboda haka, ku maida hankali yadda kuke rayuwar ku, ba kamar mutane marasa hikima ba amma kamar masu hikima.
16 Vykupujíce čas; nebo dnové zlí jsou.
Ku yi lura yadda kuke amfani da lokaci don kwanakin miyagu ne.
17 Protož nebývejte neopatrní, ale rozumějící, která by byla vůle Páně.
Kada ku zama wawaye. Maimakon haka, ku fahimci ko menene nufin Ubangiji.
18 A neopíjejte se vínem, v němžto jest prostopášnost, ale naplněni buďte Duchem svatým,
Kuma Kada ku bugu da ruwan inabi, don yana iya lalata rayuwa. Maimakon haka, ku cika da Ruhu Mai Tsarki.
19 Mluvíce sobě vespolek v žalmích, a v chvalách, a v písničkách duchovních, zpívajíce a plésajíce v srdcích vašich Pánu,
Kuna magana da junanku cikin zabura da wakoki da wakokin ruhaniya, kuna rairawa da yabo da zuciyarku ga Ubangiji.
20 Díky činíce vždycky ze všeho ve jménu Pána našeho Jezukrista Bohu a Otci,
Kullum kuna ba da gaskiya domin dukan abubuwa cikin sunan Ubangiji Yesu ga Allah Uba.
21 Poddáni jsouce jedni druhým v bázni Boží.
Kuna sarayadda kanku ga juna cikin girmama Almasihu.
22 Ženy mužům svým poddány buďte jako Pánu.
Mata, ku yi biyayya ga mazan ku kamar ga Ubangiji.
23 Nebo muž jest hlava ženy, jako i Kristus jest hlava církve, a onť jest Spasitel těla.
Domin miji shine shugaban matarsa kamar yadda Almasihu yake shugaban ikilisiya. Shine kuma mai ceton jiki.
24 A tak jakož církev poddána jest Kristu, tak i ženy mužům svým ať jsou poddány ve všem.
Amma kamar yadda ikilisiya take biyayya ga Almasihu, haka kuma dole mata suyi ga mazajen su cikin kowanne abu.
25 Muži milujte ženy své, jako i Kristus miloval církev, a vydal sebe samého za ni,
Mazaje, ku kaunaci matanku kamar yadda Almasihu ya kaunaci ikilisiya har ya ba da kansa dominta,
26 Aby ji posvětil, očistiv ji obmytím vody v slovu,
Ya yi wannan domin ya tsarkake ta. Ya wanke mu da ruwan wanki ta wurin kalma.
27 Aby ji sobě postavil slavnou církev, nemající poskvrny, ani vrásky, neb cokoli takového, ale aby byla svatá a bez úhony.
Ya yi wannan domin ya mika ma kansa ikilisiya mai daraja, ba tare da tabo ko cikas ko wani abu kamar wadannan, amma ta zama da tsarki da kuma mara aibi.
28 Takť jsou povinni muži milovati ženy své jako svá vlastní těla. Kdo miluje ženu svou, sebeť samého miluje.
Hakannan kuma, mazaje su kaunaci matansu kamar jikunnansu. Wanda yake kaunar matarsa yana kaunar kansa.
29 Žádný zajisté nikdy těla svého neměl v nenávisti, ale krmí a chová je, jakožto i Pán církev.
Ba wanda ya taba kin jikinsa. Amma, yakan ciyadda shi yana kaunarsa, kamar yadda Almasihu ya kaunaci ikilisiya.
30 Neboť jsme údové těla jeho, z masa jeho a z kostí jeho.
Domin mu gabobin jikinsa ne.
31 A protoť opustí člověk otce i matku, a připojí se k manželce své, i budouť dva jedno tělo.
“Domin wannan mutum zai rabu da ubansa da uwarsa ya manne wa matarsa, su biyu su zama nama daya”.
32 Tajemství toto veliké jest, ale já pravím o Kristu a o církvi.
Wannan asirin gaskiyar, da girma yake, amma ina magana ne game da Almasihu da ikilisiyarsa.
33 Avšak i vy, jeden každý z vás, manželku svou tak jako sám sebe miluj. Žena pak ať se bojí muže svého.
Duk da haka, kowannenku dole ya kaunaci matarsa kamar kansa, matar kuma dole ta girmama mijinta.