< 2 Tesalonickým 3 >
1 Dále pak, bratří, modlte se za nás, aby slovo Páně rozmáhalo se a slaveno bylo, jako i u vás,
A ƙarshe,’yan’uwa, ku yi mana addu’a domin saƙon Ubangiji yă yi saurin bazuwa a kuma girmama shi, kamar yadda yake a wurinku.
2 A abychom vysvobozeni byli od nezbedných a zlých lidí. Neboť ne všech jest víra.
Ku kuma yi addu’a yadda za a cece mu daga mugayen mutane masu mugunta, gama ba kowa ba ne yake da bangaskiya.
3 Ale věrnýť jest Pán, kterýž utvrdí vás a ostříhati bude od zlého.
Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan.
4 Doufámeť pak v Pánu o vás, že to, což vám předkládáme, činíte i činiti budete.
Muna da tabbaci cikin Ubangiji cewa kuna bin umarnai da muka yi muku, za ku kuma ci gaba da yin abubuwan da muka umarta.
5 Pán pak spravujž srdce vaše k lásce Boží a k trpělivému očekávání Krista.
Bari Ubangiji yă bi da zukatanku ga ƙaunan nan ta Allah da kuma jimirin nan na Kiristi.
6 Přikazujemeť pak vám, bratří, ve jménu Pána našeho Jezukrista, abyste se oddělovali od každého bratra, kterýž by se choval neřádně a ne podle naučení vydaného, kteréž přijal od nás.
A cikin sunan Ubangiji Yesu Kiristi, muna muku umarni,’yan’uwa, da ku kiyaye kanku daga kowane ɗan’uwa mai zaman banza da ba ya rayuwa bisa ga koyarwar da kuka karɓa daga wurinmu.
7 Nebo sami víte, kterak jest potřebí následovati nás, poněvadž jsme se nechovali mezi vámi neslušně.
Gama ku kanku kun san yadda ya kamata ku bi gurbinmu. Ba mu yi zaman banza sa’ad da muke tare da ku ba,
8 Aniž jsme darmo chleba jedli u koho, ale s prací a s těžkostí, ve dne i v noci dělajíce, abychom žádnému z vás nebyli k obtížení.
ba mu kuwa ci abincin kowa ba tare da ba mu biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki dare da rana, muna fama muna wahala kuma don kada mu nawaita wa waninku.
9 Ne jako bychom neměli k tomu práva, ale abychom se vám za příklad vydali, abyste nás následovali.
Mun yi wannan, ba don ba mu da’yancin karɓar irin taimakon nan ba ne, sai dai domin mu zama gurbin da za ku bi.
10 Nebo i když jsme byli u vás, to jsme vám předkládali: Kdož nechce dělati, aby také nejedl.
Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.”
11 Slyšímeť zajisté, že někteří mezi vámi chodí nezpůsobně, nic nedělajíce, ale v neužitečné věci se vydávajíce.
Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum.
12 Protož těm, kteříž takoví jsou, přikazujeme, a napomínáme jich skrze Pána našeho Jezukrista, aby pokojně pracujíce, svůj chléb jedli.
Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci.
13 Vy pak, bratří, neoblevujte dobře činíce.
Game da ku kuma’yan’uwa, kada ku gaji da yin abin da yake daidai.
14 Pakli kdo neuposlechne skrze psaní řeči naší, toho znamenejte, a nemějte s ním nic činiti, ať by se zastyděl.
In wani bai yi biyayya da umarninmu a wannan wasiƙa ba, sai fa ku lura da shi. Kada ku haɗa kai da shi, don yă ji kunya.
15 Avšak nemějte ho za nepřítele, ale napomínejte jako bratra.
Duk da haka kada ku mai da shi abokin gāba, sai dai ku gargaɗe shi a matsayin ɗan’uwa.
16 Sám pak Pán pokoje dejž vám vždycky pokoj všelijakým způsobem. Pán budiž se všemi vámi.
Yanzu, bari Ubangiji mai salama kansa yă ba ku salama a kowane lokaci da kuma a ta kowace hanya. Ubangiji yă kasance tare da ku duka.
17 Pozdravení mou vlastní rukou Pavlovou, což jest za znamení v každém listu. Takť obyčejně píši.
Ni, Bulus, nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna, wannan ce shaida a kowace wasiƙata, haka nake rubutu.
18 Milost Pána našeho Jezukrista budiž se všemi vámi. Amen. Druhý list k Tessalonicenským psán byl z Atén.
Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ku duka.