< 2 Tesalonickým 2 >
1 Prosímeť pak vás, bratří, skrze příští Pána našeho Jezukrista a naše shromáždění v něj,
Game da dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi da game da tattara mu gare shi, muna roƙonku,’yan’uwa,
2 Abyste se nedali rychle vyrážeti z mysli, ani kormoutiti, buď skrze ducha, buďto skrze řeč, neb skrze list, jako od nás poslaný, jako by nastával den Kristův.
kada ku yi saurin jijjiguwa ko kuwa hankalinku yă tashi ta wurin wani annabci, rahoto ko wasiƙar da an ce daga wurinmu ne, cewa ranar Ubangiji ta riga ta zo.
3 Nesvodiž vás žádný nižádným obyčejem. Neboť nenastane den Páně, než až prve přijde odstoupení, a zjeven bude ten člověk hřícha, syn zatracení,
Kada ku bar wani yă ruɗe ku ko ta yaya, gama wannan rana ba za tă zo ba sai an yi tawayen nan an kuma bayyana mutumin tawayen nan, mutumin da aka ƙaddara ga hallaka.
4 Protivící a povyšující se nade všecko, což slove Bůh, anebo čemuž se děje Božská čest, takže se posadí v chrámě Božím, tak sobě počínaje, jako by byl Bůh.
Zai yi gāba yă kuma ɗaukaka kansa a bisa kome da ya shafe sunan Allah, ko kuma ake yi wa sujada, domin yă kafa kansa a haikalin Allah, yana shelar kansa a kan shi Allah ne.
5 Nepomníte-liž, že ještě byv u vás, o tom jsem vám pravil?
Ba ku tuna ba cewa sa’ad da nake tare da ku nakan gaya muku waɗannan abubuwa?
6 A nyní co mešká, víte, totiž aby on teprv zjeven byl časem svým.
Yanzu kuwa kun san abin da yake hana shi, wannan yana faruwa ne don a bayyana shi a daidai lokaci.
7 Nebo již tajemství nepravosti působí, toliko až by ten, jenž jej zdržuje nyní, z prostředku byl vyvržen.
Gama ikon asirin tawaye ya riga ya fara aiki; sai dai wannan da yake hana shi zai ci gaba da yin haka sai an kau da shi.
8 A tehdážť zjeven bude ten bezbožník, kteréhož Pán zabije duchem úst svých a zkazí zjevením jasné přítomnosti své,
Sa’an nan za a bayyana mai tawayen, Ubangiji Yesu kuwa zai hamɓare shi da numfashin bakinsa yă kuma hallaka shi da darajar dawowarsa.
9 Kteréhožto nešlechetníka příští jest podle mocného díla satanova, se vší mocí a divy i zázraky lživými,
Zuwan mai tawayen nan zai zama ta wurin aikin Shaiɗan da aka bayyana cikin kowane irin ayyukan banmamaki, alamu da abubuwan banmamaki na ƙarya,
10 A se všelikým podvodem nepravosti v těch, jenž hynou, protože lásky pravdy nepřijali, aby spaseni byli.
da kuma cikin kowace irin muguntar da take ruɗin waɗanda suke hallaka. Sun hallaka ne domin sun ƙi su ƙaunaci gaskiya don su sami ceto.
11 A protož pošle jim Bůh mocné dílo podvodů, aby věřili lži,
Saboda haka Allah zai aiko musu da babban ruɗu don su gaskata ƙarya
12 A aby odsouzeni byli všickni, kteříž neuvěřili pravdě, ale oblíbili sobě nepravost.
don kuma a hukunta dukan waɗanda ba su gaskata gaskiyar ba sai dai suke jin daɗin mugunta.
13 Myť pak jsme povinni děkovati Bohu vždycky z vás, bratří Pánu milí, že vyvolil vás Bůh od počátku k spasení, v posvěcení Ducha a u víře pravdy,
Amma dole kullum mu gode wa Allah dominku,’yan’uwa waɗanda Ubangiji ya ƙaunace, domin daga farko Allah ya zaɓe ku don a cece ku ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu da kuma ta wurin gaskatawa da gaskiya.
14 K čemuž povolal vás skrze evangelium naše, k dojití slávy Pána našeho Jezukrista.
Ya kira ku ga wannan ta wurin bishararmu, don ku sami rabo a cikin ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Kiristi.
15 A protož, bratří, stůjtež a držtež se učení vydaného, jemuž jste se naučili, buďto skrze řeč, buďto i skrze list náš.
Saboda haka fa,’yan’uwa, sai ku tsaya daram ku riƙe koyarwar da muka miƙa muku, ko ta wurin maganar baki ko kuma ta wurin wasiƙa.
16 On pak Pán náš Ježíš Kristus, a Bůh i Otec náš, kterýž zamiloval nás a dal nám potěšení věčné a naději dobrou z milosti, (aiōnios )
Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa yă ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege, (aiōnios )
17 Potěšujž srdcí vašich a utvrdiž vás v každém slovu i skutku dobrém.
yă ƙarfafa zukatanku yă kuma gina ku cikin kowane aikin nagari da kuma magana.