< 1 Tesalonickým 4 >

1 Dále pak, bratří, prosíme vás, a napomínáme v Pánu Ježíši, jakož jste přijali od nás, kterak byste měli choditi a líbiti se Bohu, v tom abyste se rozhojnili více.
A ƙarshe,’yan’uwa, mun umarce ku yadda za ku yi rayuwa domin ku gamshi Allah, kamar yadda kuke yi. Yanzu muna roƙonku muna kuma gargaɗe ku a cikin Ubangiji Yesu ku yi haka sau da sau.
2 Víte zajisté, jaká přikázání vydali jsme vám skrze Pána Ježíše.
Gama kun san umarnan da muka ba ku ta wurin ikon Ubangiji Yesu.
3 Tať jest zajisté vůle Boží, totiž posvěcení vaše, abyste se zdržovali od smilstva,
Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci;
4 A aby uměl jeden každý z vás svým osudím vládnouti v svatosti a v uctivosti,
don kowannenku yă koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma,
5 Ne v libosti tělesných žádostí jako i pohané, kteříž Boha neznají;
ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba;
6 A aby žádný neutiskal ani oklamával v jakémkoli jednání bratra svého, protože mstitel jest Pán všeho toho, jakož i předpověděli jsme vám a osvědčili.
cikin wannan al’amari kuwa kada wani yă yi wa ɗan’uwansa laifi ko yă cuce shi. Ubangiji zai hukunta mutane saboda dukan irin waɗannan zunubai, kamar yadda muka riga muka gaya muku, muka kuma yi muku gargaɗi.
7 Nebo nepovolal nás Bůh k nečistotě, ale ku posvěcení.
Gama Allah bai kira mu ga zaman marasa tsarki ba, sai dai ga zaman tsarki.
8 A protož kdo by pohrdal tímto, ne člověkem pohrdá, ale Bohem, kterýž i dal Ducha svého svatého nám.
Saboda haka, duk wanda ya ƙi wannan umarni ba mutum ne ya ƙi ba sai ko Allah, wanda ya ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.
9 O lásce pak bratrské neníť potřebí psáti vám; nebo jste vy již tomu od Boha naučeni, abyste milovali jedni druhé.
Yanzu kuwa game da ƙaunar’yan’uwa, ba ma bukata mu rubuta muku, gama ku kanku Allah ya riga ya koya muku ku ƙaunaci juna.
10 A jistě činíte to ke všechněm bratřím ve vší Macedonii. Napomínámeť pak vás, bratří, abyste se v tom ještě více rozhojnili,
Gaskiyar kuwa ita ce, kuna ƙaunar dukan’yan’uwa ko’ina a Makidoniya. Duk da haka muna ƙara gargaɗe ku,’yan’uwa, ku yi haka sau da sau.
11 A snažili se pokojni býti a hleděti toho, což komu náleží, a pracovati rukama svýma vlastníma, jakož jsme přikázali vám,
Ku mai da wannan burinku na yi natsattsiyar rayuwa, kuna mai da hankali ga sha’anin da yake gabanku, kuna kuma yin aiki da hannuwanku, kamar dai yadda muka gaya muku,
12 Tak abyste slušně chodili před těmi, kteříž jsou vně, a v ničemž abyste neměli nedostatku.
don rayuwanku ta kullum ta zama da mutunci ga waɗanda suke na waje don kuma kada ku dogara a kan kowa.
13 Nechciť pak, abyste nevěděli, bratří, o těch, kteříž zesnuli, abyste se nermoutili, jako i jiní, kteříž naděje nemají.
’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege.
14 Nebo jakož věříme, že Ježíš umřel a z mrtvých vstal, takť Bůh i ty, kteříž by zesnuli v Ježíšovi, přivede s ním.
Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu.
15 Toto zajisté vám pravíme slovem Páně, že my, kteříž živi pozůstaneme do příchodu Páně, nepředejdeme těch, kteříž zesnuli.
Bisa ga maganar Ubangiji kansa, muna gaya muku cewa mu da muke raye har yanzu, waɗanda aka bari har dawowar Ubangiji, tabbatacce ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba.
16 Nebo Pán náš s zvukem ponoukajícím, s hlasem archanděla a s troubou Boží sstoupí s nebe, a mrtví, kteříž jsou v Kristu, vstanou nejprve.
Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko.
17 Potom my živí pozůstavení spolu s nimi zachváceni budeme do oblaků, vstříc Pánu v povětří, a tak vždycky se Pánem budeme.
Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada.
18 A protož potěšujtež jedni druhých těmito slovy.
Saboda haka ku ƙarfafa juna da waɗannan kalmomi.

< 1 Tesalonickým 4 >