< 1 Korintským 8 >
1 O těch pak věcech, kteréž modlám obětovány bývají, víme, že všickni známost máme. A známost nadýmá, ale láska vzdělává.
Game da abinci da ake yiwa gumakai hadaya: Mun sani cewa, “Dukanmu muna da ilimi.” Ilimi ya kan kawo takama, amma kauna tana ginawa.
2 Zdá-li se pak komu, že něco umí, ještě nic nepoznal, tak jakž by měl znáti.
Idan wani yana tunanin ya san wani abu, wannan mutumin bai rigaya ya san abinda ya kamata ya sani ba.
3 Ale jestliže kdo miluje Boha, tenť jest vyučen od něho.
Amma idan wani yana kaunar Allah, to ya san da wannan mutum.
4 A protož o pokrmích, kteříž se modlám obětují, toto dím: Víme, že modla na světě nic není a že není jiného žádného Boha nežli jeden.
Game da abincin da aka yiwa gumakai hadaya: Mun san cewa, “Gunki a duniyan nan ba wani abu bane,” kuma cewa” Babu wani Allah sai guda daya.”
5 Nebo ačkoli jsou někteří, ješto slovou bohové, i na nebi i na zemi, (jakož jsou mnozí bohové a páni mnozí, )
To wata kila ma a ce wadanda ake kira alloli sun kasance, ko a cikin sama ko duniya, kamar yadda akwai wadanda ake ce dasu “alloli dabam dabam a duniya ko a sama,” kamar yadda akwai “alloli da iyayengiji” da yawa.
6 Ale my máme jediného Boha Otce, z něhož všecko, a my v něm, a jednoho Pána Ježíše Krista, skrze něhož všecko, i my skrze něho.
“Amma a wurin mu, Allah daya ne, Uban dukan duniya, daga wurinsa aka halita dukan abu, domin sa muke rayuwa, Ubangiji Yesu Almasihu daya, wanda ta wurin sa kome ya kasance, mu kuma daga wurinsa muke.”
7 Ale ne ve všechť jest to umění. Nebo někteří se zlým svědomím pro modlu až dosavad jako modlám obětované jedí, a svědomí jejich, jsuci mdlé, poskvrňuje se.
Amma ba kowa ke da wannan ilimi ba. Shi ya sa tun da, wadan su na bauta wa gunki, kuma suna cin wannan abincin kamar abin da aka mika wa gunki. Lamirin su ya kazantu sabo da yana da rauni.
8 Nečiníť pak nás pokrm vzácných Bohu. Nebo budeme-li jísti, nic tím lepší nebudeme, a nebudeme-li jísti, nic horší nebudeme.
Amma ba abinci ke bamu tagomashi a wurin Allah ba. Ko mun ci, bamu kara karbuwan mu ba, ko ba mu ci ba, ba mu rage karbuwan mu ba.
9 Ale vizte, ať by snad ta vaše moc nebyla k urážce mdlým.
Amma, ka yi hatara kada 'yancin ka ya zama sanadiyar tuntuben wani mai rarraunar bangaskiya.
10 Nebo uzří-li kdo tebe, majícího známost, a ty sedíš při pokrmu modlám obětovaném, zdaliž svědomí toho, kterýž jest mdlý, nebude přivedeno k tomu, aby také jedl modlám obětované?
Anar misali, idan wani mai rarraunar lamiri ya hango ka mai ilimi, kana cin abincin da aka mika wa gunki, ai ba ka bashi kwarin gwiwa kenan yaci abincin da aka mika wa gunki ba?
11 I zahyneť bratr mdlý, (pro tvé to vědění), za kteréhož Kristus umřel.
Sabili da ganewar ka akan yanayin gumaka, dan'uwa rarrauna wanda Yesu ya mutu domin sa ya hallaka.
12 A tak hřešíce proti bratřím, a urážejíce svědomí jejich mdlé, proti Kristu hřešíte.
Saboda haka, idan ka saba wa 'yan'uwa masu raunin a lamiri, ka yi zunubi a gaban Almasihu.
13 A protož jestližeť pohoršuje pokrm bližního mého, nebudu jísti masa na věky, abych nezhoršil bratra svého. (aiōn )
Idan abinci zai sa dan'uwa na yayi tuntube, zan huta cin nama, domin kada in jawo wa 'yan'uwana faduwa. (aiōn )