< Filemonovi 1 >
1 Pavel, vězeň Krista Ježíše, a Timoteus bratr, Filemonovi milému, a pomocníku našemu,
Bulus, daurarren Yesu Almasihu, da kuma dan'uwa Timotawus zuwa ga Filimon, kaunataccen abokinmu da kuma abokin aikin mu,
2 A Apfie milé, a Archippovi spolurytíři našemu, i církvi, kteráž jest v domě tvém:
da Afiya yar'uwanmu da Arkifus abokin aikin mu a filin daga, da kuma Ikilisiyar da take taruwa a gidan ka:
3 Milost vám a pokoj od Boha Otce našeho a Pána Jezukrista.
Alheri da salama su kasance gare ka daga wurin Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Almasihu.
4 Díky činím Bohu svému, vždycky zmínku o tobě čině na svých modlitbách,
Kowane lokaci ina gode wa Allah. Ina ambaton ku cikin addu'oi na.
5 Slyše o lásce tvé, a víře, kterouž máš ku Pánu Ježíšovi, i ke všechněm svatým,
Na ji labarin kauna da bangaskiya da ka ke da ita a cikin Ubangiji Yesu da dukkan yan'uwa masu bi.
6 Aby společnost víry tvé mocná byla ku poznání všeho toho, cožkoli dobrého jest v vás skrze Krista Ježíše.
Ina addu'a zumuntar bangaskiyarka ta inganta ga kawo sanin kowane kyakkyawan abu dake cikin mu a cikin Almasihu.
7 Radost zajisté máme velikou, a potěšení z lásky tvé, že střeva svatých občerstvena jsou skrze tebe, bratře.
Na yi farinciki kwarai, na kuma ta'azantu saboda kaunarka, saboda zukatan masu bi sun kwanta ta wurin ka, dan'uwa.
8 Protož ačkoli mnohou smělost mám v Kristu rozkázati tobě, což by náleželo,
Saboda haka, ko da ya ke ina da gabagadi a cikin Almasihu domin in ba ka umarni ka yi abinda ya kamata ka yi,
9 Však pro lásku raději prosím, jsa takový, totiž Pavel starý, a nyní i vězeň Ježíše Krista.
duk da haka sabo da kauna, na fi so in roke ka- Ni, Bulus, dattijo, a yanzu kuma ga ni dan kurkuku domin Almasihu Yesu.
10 Prosímť pak tebe za syna svého, kteréhož jsem zplodil v vězení svém, Onezima,
Ina rokon ka saboda da na Onisimus, wanda na zama uba a gare shi sa'adda nake cikin sarkokina.
11 Kterýž byl někdy tobě neužitečný, ale nyní tobě i mně velmi užitečný, jehožť jsem odeslal.
Domin a da kam, ba shi da amfani a wurin ka, amma yanzu yana da amfani a gare ka da kuma a gare ni.
12 Protož ty jej, totiž střeva má, přijmi.
Na kuma aike shi wurinka, shi wanda ya ke a cikin zuciyata kwarai.
13 Kteréhož já chtěl jsem byl při sobě zdržeti, aby mi posluhoval místo tebe v vězení pro evangelium;
Na so da na rike shi a wuri na, domin ya rika yi mini hidima a madadin ka, a lokacin da ni ke cikin sarkoki saboda bishara.
14 Ale bez vědomí tvého nechtěl jsem nic učiniti, aby dobrý skutek tvůj nebyl bezděčný, ale dobrovolný.
Amma ba na so in yi wani abu ba tare da sanin ka ba. Ba ni so nagarin aikinka ya zama na dole amma daga kyakkyawar nufi.
15 Ano snad proto byl odšel na chvíli, abys jej věčného měl, (aiōnios )
Watakila dalilin da yasa ya rabu da kai na dan lokaci ke nan, domin ka karbe shi kuma har abada. (aiōnios )
16 Již ne jako služebníka, ale více než služebníka, totiž bratra milého, zvláště mně, a čím více tobě, i podlé těla, i v Pánu.
Daga yanzu ba za ya zama bawa ba kuma, amma fiye da bawa, wato kaunataccen dan'uwa. Shi kaunatacce ne musamman a gare ni, har fiye da haka ma a gare ka, a cikin jiki da kuma cikin Ubangiji.
17 Protož máš-li mne za tovaryše, přijmiž jej, jako mne.
Idan ka maishe ni abokin hidima, ka karbe shi kamar yadda za ka karbe ni.
18 Jestližeť pak v čem ublížil, aneb dlužen-liť co, to mně přičti.
Idan kuwa ya yi maka abinda ba daidai ba ko kuwa kana bin sa wani abu, ka dauka yana wurina.
19 Já Pavel psal jsem svou rukou, jáť zaplatím; ať nedím tobě, že ty i sám sebe jsi mi dlužen.
Ni, Bulus, na rubuta wannan da hannuna: zan biya ka. Ba kuwa cewa sai na gaya maka cewa ina bin ka bashin kanka ba.
20 Tak, bratře, ať já uživu tebe v Pánu; očerstviž střeva má v Pánu.
I, dan'uwa, ka yi mani alheri cikin Ubangiji; ka ba zuciyata hutu a cikin Almasihu.
21 Jist jsa tvým poslušenstvím, napsal jsem tobě, věda, že i více, než pravím, učiníš.
Saboda Ina da tabbaci game da biyayyarka, na rubuta maka. Na san za ka yi fiye da abinda na roka.
22 A mezi tím připrav mi také hospodu; neboť naději mám, že k modlitbám vašim budu vám navrácen.
Harwayau, ka shirya mani masauki. Domin ina fata ta wurin adu'oinku, nan ba da dadewa ba za a maida ni wurin ku.
23 Pozdravují tě Epafras, (spoluvězeň můj pro Krista Ježíše, )
Efafaras, abokina cikin Almasihu Yesu a kurkuku yana gaishe ka,
24 Marek, Aristarchus, Démas, a Lukáš, pomocníci moji.
haka ma Markus da Aristarkus, da Dimas, da Luka abokan aikina.
25 Milost Pána našeho Jezukrista s duchem vaším. Amen.
Bari Alherin Ubangiji Yesu Almasihu ya kasance da Ruhunka. Amin.