< Efezským 6 >
1 Dítky poslouchejte rodičů svých v Pánu; neboť jest to spravedlivé.
'Ya'ya, ku yi biyayya ga iyayenku chikin Ubangiji, domin wannan daidai ne.
2 Cti otce svého i matku, (toť jest přikázaní první s zaslíbením, )
“Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka” (Doka ta fari kenan da alkawari),
3 Aby dobře bylo tobě, a abys byl dlouhověký na zemi.
“ta haka za ku yi albarka, domin kwanakinku su yi tsawo a duniya”.
4 A vy otcové nepopouzejte k hněvu dítek svých, ale vychovávejte je v cvičení a v napomínání Páně.
Hakanan, ku ubanni kada ku cakuni 'ya'yan ku har su yi fushi, amma ku goye su cikin horon Ubangiji da gargadinsa.
5 Služebníci buďte poslušni pánů tělesných s bázní a s strachem, v sprostnosti srdce svého, jako Krista,
Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya tare da girmamawa da tsoro da zuciya mai gaskiya. Ku yi masu biyayya kamar ga Almasihu.
6 Ne na oko sloužíce, jako ti, kteříž se lidem líbiti usilují, ale jako služebníci Kristovi, činíce vůli Boží z té duše,
Ku yi masu biyayya ba don lallai suna kallonku ba domin ku faranta masu rai. Maimakon haka, ku yi biyayya kamar bayi ga Almasihu. Ku yi nufin Allah daga zuciya.
7 S dobrou myslí sloužíce, jakožto Pánu, a ne lidem,
Ku yi hidima da dukan zuciya, kamar kuna bautar Ubangiji ba mutane ba.
8 Vědouce, že, což by koli jeden každý učinil dobrého, za to odplatu vzíti má ode Pána, buďto služebník, buďto svobodný.
Sai ku sani cewa duk abinda mutum ya yi zai karbi sakamako daga wurin Ubangiji, ko shi bawa ne ko 'yantacce.
9 A vy páni též se tak mějte k nim, odpouštějíce pohrůžky, vědouce, že i vy také máte Pána svého v nebesích, a přijímání osob není u něho.
Ku kuma iyayengiji, ku yi irin wannan ga barorin ku. Kada ku razana su. Kun sani shi wanda ke Ubangijinsu da ku daya ne yana sama. Kun sani tare da shi baya nuna tara.
10 Dále pak, bratří moji, posilňte se v Pánu a v moci síly jeho.
A karshe, ku karfafa cikin Ubangiji da cikin karfin ikonsa.
11 Oblecte se v celé odění Boží, abyste mohli státi proti útokům ďábelským.
Ku dauki dukan makamai na Allah, domin ku iya dagewa gaba da dabarun shaidan.
12 Neboť není bojování naše proti tělu a krvi, ale proti knížatstvu, proti mocnostem, proti světa pánům temností věku tohoto, proti duchovním zlostem vysoko. (aiōn )
Gama yakinmu ba da nama da jini bane. Amma, da ikoki da mulkoki da mahukuntan wannan zamani mai duhu da rundunai masu duhu na mugunta cikin sammai. (aiōn )
13 A protož vezměte celé odění Boží, abyste mohli odolati v den zlý, a všecko vykonajíce, státi.
Don haka ku dauki dukan makamai na Allah, domin ku iya tsayawa da karfi cikin muguwar rana. Bayan kun yi komai za ku tsaya da karfi.
14 Stůjtež tedy, majíce podpásaná bedra svá pravdou, a oblečeni jsouce v pancíř spravedlnosti,
Saboda haka ku tsaya da karfi. Ku yi wannan bayan kun yi damara cikin gaskiya kuna yafa sulke na adalci.
15 A obuté majíce nohy v hotovost k evangelium pokoje,
Ku yi wannan bayan kun daure kafafunku da shirin kai bisharar salama.
16 A zvláště pak vezmouce štít víry, kterýmž byste mohli všecky šípy ohnivé nešlechetníka toho uhasiti.
Cikin dukan abu ku dauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku kashe dukan kibau masu wuta na mugun.
17 Lebku také spasení vezměte, i meč Ducha, jenž jest slovo Boží,
Ku dauki kwalkwalin ceto da takobin Ruhu, wanda shine maganar Allah.
18 Všelikou modlitbou a prosbou modléce se každého času v Duchu, a v tom bedliví jsouce se vší ustavičností a prošením za všecky svaté,
Tare da kowacce irin addu'a da roko kuna addu'a kullum cikin Ruhu. Da wannan lamiri, kuna tsare wannan da iyakacin kula da dukan juriya da roko saboda dukan masu bi.
19 I za mne, aby mi dána byla řeč k otevření úst mých s smělou doufanlivostí, abych oznamoval tajemství evangelium,
Ku yi mani addu'a, domin in karbi sako duk sa'adda na bude bakina. Ku yi addu'a in sami gabagadin bayyana boyayyar gaskiyar bishara.
20 Pro něž úřad konám v řetězu, abych v něm směle mluvil, jakž mně mluviti náleží.
Saboda bishara nake jakada cikin sarkoki, yadda a cikinta zan yi magana gabagadi yadda takamata.
21 Abyste pak věděli i vy, co se se mnou děje, a co činím, všecko vám to oznámí Tychikus, milý bratr a věrný služebník v Pánu,
Amma domin ku san rayuwa ta, da yadda nake, Tikikus, dan'uwa kaunatacce da amintaccen bawa cikin Ubangiji, zai sanar da ku dukan abu.
22 Jehož jsem pro to samo k vám poslal, abyste věděli o našich věcech, a aby potěšil srdcí vašich.
Saboda wannan dalili na aiko shi gare ku, domin ku san al'amuran mu, kuma domin ku sami ta'aziya a zukatan ku.
23 Pokoj bratřím, a láska s věrou od Boha Otce a Pána Jezukrista.
Bari salama ta kasance tare da 'yan'uwa, kauna da bangaskiya daga wurin Allah Uba da Ubangiji Yesu Almasihu.
24 Milost Boží se všechněmi milujícími Pána našeho Jezukrista k neporušitelnosti. Amen.
Alheri ya kasance tare da wadannan da suke kaunar Ubangijinmu Yesu Almasihu tare da kauna mara mutuwa.