< Efezským 2 >

1 I vás obživil mrtvé v vinách a hříších,
Amma da ku matattu ne cikin zunubanku da laifofinku.
2 V nichž jste někdy chodili podlé obyčeje světa tohoto, a podlé knížete mocného v povětří, ducha toho, kterýž nyní dělá v synech zpoury. (aiōn g165)
A cikinsu kuka yi rayuwa bisa ga al'amuran duniyan nan. Kuka biye wa mai sarautar ikokin sararin sama, wannan ruhun ne da ke aiki cikin kangararrun 'ya'ya. (aiōn g165)
3 Mezi nimiž i my všickni obcovali jsme někdy v žádostech těla svého, činivše to, což se líbilo tělu a mysli, a byli jsme z přirození synové hněvu jako i jiní.
Da can dukanmu muna cikin wadannan marasa bada gaskiya. Muka biye wa mugun burin jikinmu. Muna aikata halin mutuntaka da na tunaninmu. Bisa ga dabi'a 'ya'ya ne wadanda sun cancanci fushin Allah, kamar wadansu.
4 Ale Bůh, bohatý jsa v milosrdenství pro velikou lásku svou, kterouž zamiloval nás,
Amma Allah mai yalwar jinkai ne, sabili da matukar kauna da ya kaunace mu.
5 Také i nás, když jsme mrtví byli v hříších, obživil spolu s Kristem, (milostí spaseni jste, )
Sa'anda muke matattu cikin zunubai, ya kawo mu cikin sabon rai tare da Almasihu. Ta wurin alheri aka cece mu.
6 A spolu s ním vzkřísil, i posadil na nebesích v Kristu Ježíši,
Allah ya tashe mu tare ya kuma sa muka zauna tare a matsayi guda cikin Almasihu Yesu.
7 Aby ukázal v věku budoucím nepřevýšené bohatství milosti své, z dobroty své k nám v Kristu Ježíši. (aiōn g165)
Ya yi wannan domin a zamanai masu zuwa ya nuna mana matukar yalwar arzikin alherinsa ta wurin Yesu. Yana nuna mana wannan ta wurin alherinsa. (aiōn g165)
8 Nebo milostí spaseni jste skrze víru, (a to ne sami z sebe, darť jest to Boží, )
Domin ta wurin alheri aka cece ku ta wurin bangaskiya, wannan ba daga gare ku ba ne, kyauta ce ta Allah.
9 Ne z skutků, aby se někdo nechlubil.
Ba daga ayyuka ba, Saboda wannan dalili kada kowa ya yi fahariya.
10 Jsme zajisté jeho dílo, jsouce stvořeni v Kristu Ježíši k skutkům dobrým, kteréž Bůh připravil, abychom v nich chodili.
Gama mu aikin hannuwansa ne, halitattu cikin Almasihu Yesu domin mu yi kyawawan ayyuka, wadanda tun da Allah ya tanada, mu yi rayuwa a cikinsu.
11 Protož pamatujte, že vy někdy pohané podlé těla, kteříž jste slouli neobřízka od těch, kteříž slouli obřízka na těle, kteráž se působí rukama,
Saboda haka ku tuna da ku al'ummai ne a dabi'ar jiki. Ana kiranku “marasa kaciya”, abin da ake kira kaciya cikin jiki wadda hannayen mutane ke yi.
12 Vy jste byli onoho času bez Krista, odcizení od společnosti Izraele, a cizí od úmluv zaslíbení, naděje nemající, a bez Boha na světě.
Gama a lokacin nan a rabe kuke da Almasihu. Ku bare ne ga mutanen Isra'ila. Ku baki ne ga wa'adodi na al'kawarai. Ba ku da tabbaci a kan gobe. Ba ku da Allah a cikin duniya.
13 Ale nyní v Kristu Ježíši vy, kteříž jste někdy byli dalecí, blízcí učiněni jste skrze krev Kristovu.
Amma yanzu a cikin Almasihu Yesu ku da da kuke nesa da Allah, an kawo ku kusa da shi ta wurin jinin Almasihu.
14 Nebo onť jest pokoj náš, kterýž učinil oboje jedno, zbořiv hradbu dělící na různo,
Gama shine salamar mu. Domin ya mai da biyun daya. Cikin jikinsa ne ya rushe katangar gaba da ta raba mu da juna.
15 A nepřátelství, totiž zákon přikázaní v ustanoveních, vyprázdniv skrze tělo své, aby ty oboje vzdělal v samém sobě v jednoho nového člověka, tak čině pokoj,
Wato ya kawar da shari'a mai umarnai da sharudda, domin ya halitta sabon mutum daya a cikinsa. Yin haka ya kawo salama.
16 A v mír uvodě oboje v jenom těle Bohu skrze kříž, vyhladiv nepřátelství skrze něj.
Ya yi haka domin ya sulhunta mutum biyu cikin jiki daya ga Allah ta wurin gicciye. Ta wurin gicciye ya kashe gabar da ke tsakaninsu.
17 A přišed, zvěstoval pokoj vám, dalekým i blízkým.
Yesu ya zo ya yi maku shelar salama ku da kuke nesa da ku na kusa.
18 Neboť skrze něho obojí máme přístup v jednom Duchu k Otci.
Domin ta wurin Yesu dukanmu biyu cikin Ruhu daya muna da hanya zuwa wurin Uba.
19 Aj, již tedy nejste hosté a příchozí, ale spoluměšťané svatých a domácí Boží,
Sabo da haka yanzu ku al'ummai, ko daya, ba bare ba ne. Maimakon haka ku abokai ne tare da kebabbun Allah, abokan aiki.
20 Vzdělaní na základ apoštolský a prorocký, kdež jest gruntovní úhelný kámen sám Ježíš Kristus,
Wadanda an gina su bisa tushen manzanni da annabawa. Almasihu Yesu da kansa shine mafificin dutsen ginin.
21 Na němž všecko stavení příslušně vzdělané roste v chrám svatý v Pánu.
A cikinsa dukan ginin ya hade tare, suna kuma girma kamar haikali cikin Ubangiji.
22 Na kterémž i vy spolu vzděláváte se v příbytek Boží, v Duchu svatém.
A cikinsa ne kuma ake gina ku gaba daya kun zama mazaunin Allah a cikin Ruhu.

< Efezským 2 >