< Skutky Apoštolů 10 >
1 Muž pak nějaký byl v Cesarii, jménem Kornelius, setník z zástupu, kterýž sloul Vlaský,
An yi wani Mutum a birnin Kaisariya, mai suna Karniliyas, shugaban sojoji ne na kungiyar da ake kira Italiya.
2 Nábožný a bohobojný se vším domem svým, čině almužny mnohé lidu.
Mutum ne mai ibada, wanda ya mika kansa da iyalinsa ga bautar Allah; ya kan bada taimakon kudi mai yawa ga Yahudawa, kuma yana addu'a ko yaushe ga Allah.
3 A modlívaje se vždycky Bohu, viděl u vidění zřetelně, jako v hodinu devátou na den, anděla Božího, an všel k němu, a řekl jemu: Kornéli.
Wajen sa'a ta tara ga yini, an bayyana masa cikin wahayi mala'kan Ubangiji na zuwa gare shi sai mala'ikan ya ce masa, ''Karniliyas!''
4 A on pilně popatřiv naň, a sstrašiv se, řekl: Co chceš, Pane? I řekl jemu: Modlitby tvé a almužny tvé vstoupily na pamět před tváří Boží.
Karniliyas ya zuba wa mala'ikan ido a tsorace ya ce ''Menene, mai gida?'' mala'ikan ya ce masa, ''Addu'ar ka da taimakon ka ga talakawa ya kai sama matsayin sadaka abin tunawa a gaban Allah,
5 Protož nyní pošli muže do Joppen, a povolej Šimona, kterýž má přijmí Petr.
''Yanzu ka aika mutane zuwa birnin Yafa su kawo mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus.
6 Tenť hospodu má u nějakého Šimona koželuha, kterýž má dům u moře. Onť poví tobě, co bys ty měl činiti.
Yana zama tare da Saminu majemi, wanda gidansa ke bakin teku.
7 A když odšel anděl, kterýž mluvil Korneliovi, zavolal dvou služebníků svých, a rytíře pobožného z těch, kteříž vždycky při něm byli.
Da mala'ikan da ya yi magana da shi ya tafi, Karniliyas ya kira biyu daga barorin gidansa, da kuma soja guda mai bautar Allah daga cikin sojojin da suke masa hidima.
8 A oznámiv jim všecko to, poslal je do Joppen.
Karniliyas ya fada masu dukan abin ya faru sai ya aike su Yafa.
9 Nazejtří pak, když oni šli, a přibližovali se k městu, všel Petr na horu, aby se modlil, okolo hodiny šesté.
Washe gari wajen sa'a ta shida (tsakar rana) suna cikin tafiya da suka yi kusa da birni, Bitrus ya hau kan bene don ya yi addu'a.
10 A potom velice zlačněv, chtěl pojísti. Když pak oni strojili, připadlo na něj mysli vytržení.
Sai ya ji yunwa kuma yana bukatar wani abinda da zai ci, amma a yayin da mutanen na dafa abinci, sai ya ga wahayi.
11 I uzřel nebe otevřené a sstupující k sobě nádobu jakous jako prostěradlo veliké, za čtyři rohy uvázanou, ana se spouští na zem,
Sai ya ga sararin sama ya bude kuma wani tasa na saukowa, wani abu kamar babban mayafi yana saukowa zuwa duniya, ana zuro shi ta kusuryoyinsa hudu.
12 Na níž byla všeliká zemská hovada čtvernohá, a zvířata, a zeměplazové, i ptactvo nebeské.
A cikinsu kuwa akwai dukan halitun dabbobi masu kafa hudu da kuma masu rarrafe a duniya da tsunstayen sama.
13 I stal se hlas k němu: Vstaň, Petře, bí a jez.
Sai murya ta yi magana da shi; “Tashi, Bitrus, yanka ka ci ''
14 I řekl Petr: Nikoli, Pane, neboť jsem nikdy nejedl nic obecného aneb nečistého.
Amma Bitrus ya ce ''Ba haka ba, Ubangiji, gama ban taba cin abu mara tsarki ko mai kazanta ba.”
15 Tedy opět podruhé stal se hlas k němu: Cožť Bůh očistil, neměj ty toho za nečisté.
Amma muryar ta sake zuwa masa karo na biyu kuma; “Abinda Allah ya tsarkake, kada ka kira shi kazantacce.”
16 A to se stalo potřikrát. I vzata jest zase ta nádoba do nebe.
Wannan ya faru sau uku; nan da nan sai aka dauki tasar zuwa sama.
17 A když Petr sám u sebe rozjímal, co by znamenalo vidění to, kteréž viděl, aj, muži ti, kteříž posláni byli od Kornelia, ptajíce se na dům Šimonův, stáli přede dveřmi.
A yayin da Bitrus na cikin rudani game da ma'anar wahayin da ya gani, sai ga mutanen da Karniliyas ya aika suna tsaye a bakin kofar gidan, bayan sun tambayi hanyar zuwa gidan,
18 A zavolavše, tázali se: Má-li zde hospodu Šimon, kterýž má přijmí Petr?
Kuma suka yi sallama suna tambaya ko Saminu wanda ake kira Bitrus ya sauka a nan.
19 A když Petr přemyšloval o tom vidění, řekl jemu Duch: Aj, muži tři hledají tebe.
A yayin da Bitrus yana kan tunani akan wahayin, Ruhu ya ce masa, “Duba, mutane uku na neman ka.”
20 Protož vstana, sejdi dolů, a jdi s nimi, nic se nerozpakuje; neboť jsem já je poslal.
Tashi ka sauka ka tafi tare da su. Kada ka yi jinkirin tafiya tare da su, domin Nine na aike su.”
21 Tedy sšed Petr k těm mužům, kteříž posláni byli k němu od Kornelia, řekl: Aj, jáť jsem ten, kteréhož hledáte. Jaká jest příčina, pro niž jste přišli?
Bitrus kuwa ya sauko wurin mutanen ya ce, “Ni ne wanda kuke nema. Me ya sa kuka zo?”
22 Oni pak řekli: Kornelius setník, muž spravedlivý a bohabojící, i svědectví dobré mající ode všeho národu Židovského, u vidění napomenut jest od anděla svatého, aby povolal tebe do domu svého, a slyšel řeč od tebe.
Suka ce, “Shugaban soja mai suna Karniliyas, adalin mutum kuma mai bautar Allah, yana da kyakkyawar shaida a dukan al'umman Yahudawa, shi ne wanda mala'ika mai tsarki na Allah ya aika domin ka zo gidansa, ya ji sako daga wurinka.”
23 Tedy zavolav jich do domu, přijal je do hospody. Druhého pak dne Petr šel s nimi, a někteří bratří z Joppen šli s ním.
Sai Bitrus ya gayyace su su zo ciki kuma su zauna tare da shi. Washegari sai ya tafi tare da su, kuma wadansu 'yan'uwa daga Yafa suka raka shi.
24 A nazejtří přišli do Cesaree. Kornelius pak očekával jich, svolav příbuzné své a přátely blízké.
Kashegari suka shiga Kaisariya, Karniliyas kuwa yana jiran su; har ma ya gayyaci 'yan'uwansa da kuma abokansa na kusa.
25 I stalo se, když vcházel Petr, vyšel proti němu Kornelius, a padna k nohám jeho, klaněl se mu.
Ya kasance sa'adda Bitrus ya shiga, Karniliyas ya sadu da shi kuma ya durkusa ya yi masa sujada.
26 Ale Petr pozdvihl ho, řka: Vstaň, i jáť také sám člověk jsem.
Amma Bitrus ya tashe shi yana cewa, “Tashi tsaye! Ni ma mutum ne.”
27 A rozmlouvaje s ním, všel, a nalezl mnoho těch, kteříž se byli sešli.
A lokacin da Bitrus yake magana da shi, ya shiga ciki sai ya tarar da mutane da yawa sun taru a wuri daya.
28 I řekl jim: Vy víte, že neslušné jest muži Židu připojiti se aneb přistoupiti k cizozemci, ale mně ukázal Bůh, abych žádného člověka nepravil obecným neb nečistým býti.
Ya ce masu, “Ku da kanku kun sani bai dace Bayahuden mutum ya yi ma'amulla ko ya ziyarci wani ko wata kabila ba. Amma Allah ya ce da ni kada in ce da kowa mara tsarki ko kazantacce.
29 Protož bez odporu přišel jsem, povolán jsa. I ptám se, pro kterou příčinu poslali jste pro mne?
Wannan shine yasa na zo ba tare da musu ba, a lokacin da kuka kira ni. Don haka na tambaye ku me ya sa kuka aika in zo.”
30 A Kornelius řekl: Před čtyřmi dny postil jsem se až do této hodiny, a v hodinu devátou modlil jsem se v domě svém. A aj, postavil se přede mnou muž v rouše bělostkvoucím.
Karniliyas ya ce “Kwanaki hudu da sun wuce a daidai wannan lokaci, ina addu'a da cikin sa'a na tara (karfe uku) a gidana, sai na ga mutum tsaye a gabana da tufafi mai haske.
31 A řekl: Kornéli, uslyšánať jest modlitba tvá, a almužny tvé jsouť v paměti před tváří Boží.
Ya ce, “Karniliyas, Allah ya ji addu'ar ka, kuma taimakon ka ga talakawa ya tuna ma Allah da kai.
32 Protož pošli do Joppen, a povolej Šimona, kterýž slove Petr. Tenť má hospodu v domě Šimona koželuha u moře; on přijda, bude mluviti tobě.
Saboda haka ka aika da wani Yafa, ya kira maka mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus. Yana zama a gidan Saminu majemi, da ke bakin teku.
33 Protož hned té chvíle jsem poslal k tobě, a ty jsi dobře učinil, žes přišel. Nyní tedy my všickni před oblíčejem Božím hotovi jsme slyšeti všecko, což jest koli přikázáno tobě od Boha.
[Idan ya zo, zai yi magana da kai.]
34 Tedy Petr otevřev ústa, řekl: V pravdě jsem shledal, že Bůh není přijimač osob.
Sai Bitrus ya bude bakinsa ya ce, “Gaskiya, na fahimci Allah baya nuna bambanci.
35 Ale v každém národu, kdož se ho bojí, a činí spravedlnost, příjemný jest jemu;
Maimakon haka, cikin kowace al'umma duk mai ibada kuma mai aikata adalci karbabbe ne a gare shi.
36 Jakž to oznámil synům Izraelským, zvěstuje pokoj skrze Ježíše Krista, kterýž jest Pánem všeho.
Ku kun san sakon da ya aika wa mutanen Isra'ila, a lokacin da ya sanar da labarin mai kyau na salama ta wurin Yesu Kristi, wanda shine Ubangiji na duka.
37 Vy sami víte, co se dálo po všem Židovstvu, počna od Galilee, po křtu, kterýž kázal Jan:
Ku da kanku kun san al'amuran da suka kasance, wanda ya faru cikin Yahudiya, farawa daga Galili, bayan sanarwar baftismar da Yahaya ya yi.
38 Kterak Ježíše od Nazaréta pomazal Bůh Duchem svatým a mocí. Kterýž chodil, dobře čině, a uzdravuje všecky posedlé od ďábla; nebo Bůh s ním byl.
Al'amura game da Yesu Banazare, yadda Allah ya kebe shi da Ruhu Mai Tsarki da iko kuma. Ya kuma ci gaba da aikin alheri da warkarwa ga dukan wadanda shaidan ya daure, domin Allah yana tare da shi.
39 A my jsme svědkové všeho toho, což činil v krajině Judské a v Jeruzalémě. Kteréhož zamordovali, pověsivše na dřevě.
Mu shaidu ne ga dukan abubuwan da ya yi a kasar Yahudawa da cikn Urushalima, wannan Yesu wanda suka kashe, ta wurin giciye shi a akan itace.
40 Toho Bůh vzkřísil třetího dne, a způsobil to, aby zjeven byl,
Wannan mutumin, Allah ya ta da shi rana ta uku ya kuma maishe shi sananne,
41 Ne všemu lidu, ale svědkům prvé k tomu zřízeným od Boha, nám, kteříž jsme s ním jedli a pili po jeho z mrtvých vstání.
ba ga dukan mutane ba, amma ga shaidun da Allah ya zaba tun da farko - mu kanmu, wadanda muka ci muka sha tare da shi bayan tashin sa daga matattu,
42 A přikázal nám kázati lidu a svědčiti, že on jest ten ustanovený od Boha soudce živých i mrtvých.
Ya umarce mu mu yi wa mutane wa'azi mu kuma tabbatar cewa shine wanda Allah ya zaba ya yi shariya bisa masu rai da matattu.
43 Jemuť všickni proroci svědectví vydávají, že odpuštění hříchů vezme skrze jméno jeho všeliký, kdožkoli uvěřil by v něho.
Gareshi ne dukan annabawa suka yi shaida, domin dukan wanda ya bada gaskiya gareshi ya sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.`
44 A když ještě Petr mluvil slova tato, sstoupil Duch svatý na všecky, kteříž poslouchali slova.
Sa'adda Bitrus yana kan magana game da wadannan abubuwa, Ruhu Mai Tsarki ya sauko a kan dukan wadanda suke sauraron wa'azin sa.
45 I užasli se ti, kteříž z obřezaných věřící byli, kteříž byli přišli s Petrem, že i na pohany dar Ducha svatého jest vylit.
Mutanen da ke kungiyar masu bi da suka yarda da kaciya, dukan wadanda suka zo tare da Bitrus suka yi mamaki, domin baiwar Ruhu Mai Tsarki ya sauko a kan al'ummai.
46 Nebo slyšeli je, ani mluví jazyky rozličnými, a velebí Boha. Tehdy odpověděl Petr:
Domin sun ji al'umman nan suna magana da wasu harsuna suna yabon Allah. Sai Bitrus ya amsa,
47 Zdali může kdo zabrániti vody, aby tito nebyli pokřtěni, kteříž Ducha svatého přijali jako i my?
“Ko akwai wanda zai hana wa wadannan baftisma ta ruwa, da shike suma sun karbi Ruhu Mai Tsarki kamar mu?”
48 A rozkázal je pokřtiti ve jménu Páně. I prosili ho, aby u nich pobyl za některý den.
Sai ya ba da umarni a yi masu baftisma cikin sunan Yesu Kristi. Sai suka roke shi ya kasance da su na wasu kwanaki.