< 2 Janův 1 >
1 Starší v Kristu vyvolené paní i synům jejím, kteréž já miluji v pravdě, a ne sám já, ale i všickni, kteříž poznali pravdu,
Daga dattijon zuwa ga uwar gida zababbiya da yayanta, wadanda nake kauna da gaskiya, ba ni kadai ba, amma da dukan wadanda sun san gaskiya -
2 Pro pravdu, kteráž zůstává v nás, a s námiť bude na věky: (aiōn )
domin gaskiya da take cikinmu za ta kuma kasance tare da mu har abada. (aiōn )
3 Budiž s vámi milost, milosrdenství, a pokoj od Boha Otce, i od Pána Jezukrista, Syna Otcova, v pravdě a v lásce.
Alheri da jinkai da salama za su kasance tare da mu, daga Allah Uba da kuma daga Yesu Almasihu Dan Uba, a cikin gaskiya da kauna.
4 Zradoval jsem se velmi, že jsem nalezl některé z synů tvých, an chodí v pravdě, jakož jsme přikázaní vzali od Otce.
Na yi murna sosai sa'anda na sami wadansu yayanki suna tafiya cikin gaskiya, kamar yadda muka karbi wannan umarni daga Uba.
5 A nyní prosím tebe, paní, ne jako nové přikázaní předkládaje tobě, ale to, kteréž jsme měli od počátku, abychom milovali jedni druhé.
Yanzu ina rokon ki, uwar gida, ba kamar ina rubuta maki sabon umarni ba, amma wannan da muka samu tun da can, cewa mu kaunaci junanmu.
6 A totoť jest ta láska, abychom chodili podlé přikázaní jeho. Přikázaní pak toto jest, jakž jste slýchali od počátku, abyste v něm chodili.
Wannan kuma itace kauna, cewa mu yi tafiya bisa ga umarnin sa. Wannan shine umarnin, daidai kamar yadda kuka ji da fari, da cewa ku yi tafiya a cikinsa.
7 Nebo mnozí bludaři vyšli na svět, kteříž nevyznávají Jezukrista přišlého v těle. Takový každý jest bludař a antikrist.
Gama masu yaudara sun fito a duniya, wadanda ba su yarda cewa Yesu ya zo cikin jiki ba. Wannan ne mayaudari da kuma magabcin Almasihu.
8 Hleďtež sebe, abychom neztratili toho, o čemž jsme pracovali, ale odplatu plnou abychom vzali.
Ku dubi kanku, domin kada ku rasa abubuwan da mu duka muka yi aiki a kansu, amma domin ku karba dukan sakamon ku.
9 Každý, kdož přestupuje, a nezůstává v učení Kristovu, nemá Boha; kdož zůstává v učení Kristovu, tenť i Otce i Syna má.
Duk wanda ya ci gaba da tafiya ba cikin koyarwa Almasihu ba, ba shi da Allah. Wanda ya zauna cikin koyarwar kwa yana tare da Uban da kuma Dan.
10 Přichází-li kdo k vám, a tohoto učení nepřináší, nepřijímejte ho do domu, aniž ho pozdravujte.
Duk wanda ya zo wurinku, ba tare da wannan koyarwar ba, kar ku karbe shi cikin gidanku, kada ma ku gaishe shi.
11 Nebo kdož takového pozdravuje, obcuje skutkům jeho zlým.
Domin duk wanda ya gaishe shi ya yi tarayya da shi kenan cikin miyagun ayyukan sa.
12 Mnoho vám psáti měv, nechtěl jsem se svěřiti černidlu a papíru, ale mámť naději, že k vám přijdu, a ústy k ústům mluviti budu, aby radost naše plná byla.
Ina da abubuwa dayawa da nake so in rubuta maki amma al'kalami tawada da takarda baza su iya daukar su duka ba. Amma duk da haka ina begen zuwa gare ki domin mu yi magana fuska da fuska, domin farin cikn mu ya zama cikakke.
13 Pozdravují tě synové sestry tvé v Pánu vyvolené. Amen.
Yayan yar'uwarki zababbiya suna gaishe ki.