< 2 Korintským 9 >
1 Nebo o pomoci, kteráž se děje svatým, jest zbytečné psáti vám.
Babu wata bukata in rubuta muku game da hidiman nan ga tsarkaka.
2 Vím zajisté o vaší hotovosti, pro kterouž chlubím se vámi Macedonským, že Achaia hotova jest od předešlého léta. A ta vaše horlivost mnohými pohnula.
Gama na san aniyarku na yin taimako, ina kuma taƙama a kan wannan ga Makidoniyawa, ina faɗin musu cewa tun bara, ku da kuke a Akayya a shirye kuke ku bayar. Ƙoƙarinku kuwa ya zuga yawancinsu ga aiki.
3 I poslal jsem tyto bratří, aby chlouba naše vámi nebyla marná v té stránce, ale abyste, (jakž jsem řekl, ) byli hotovi,
Amma ina aika’yan’uwan nan don kada taƙamar da muke yi da ku, a kan wannan al’amari ta zama a banza, sai dai domin yă zama kuna nan a shirye, kamar yadda na faɗa za ku kasance.
4 Abychom snad, přišli-li by se mnou Macedonští, a nalezli vás nehotové, nemusili se styděti, (ať nedím vy, ) za tak podstatnou chloubu.
Gama in waɗansu mutanen Makidoniya sun zo tare da ni, suka tarar ba a shirye kuke ba, kunya ta ishe mu, balle fa ku, saboda amincewa da muke yi da ku.
5 Protož vidělo se mi za potřebné těchto bratří napomenouti, aby napřed šli k vám, a připravili prvé opověděnou zbírku vaši, aby byla hotová jako dobrovolná zbírka, a ne jako bezděčná.
Saboda haka, na ga ya dace in roƙi’yan’uwan nan su ziyarce ku kafin lokacin, su kuma gama shirye-shirye saboda bayarwa ta yardar ran da kuka yi alkawari. Ta haka bayarwar za tă zama a shirye, ta yardar rai ba ta dole ba.
6 Ale totoť pravím: Kdo skoupě rozsívá, skoupě i žíti bude; a kdož rozsívá ochotně, ochotně i žíti bude.
Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace.
7 Jeden každý jakž uložil v srdci, ne s neochotnou myslí aneb z mušení. Neboť ochotného dárce miluje Bůh.
Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.
8 Mocenť jest pak Bůh všelikou milost rozhojniti v vás, abyste ve všem všudy všeliký dostatek majíce, hojní byli ke všelikému skutku dobrému,
Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki.
9 Jakož psáno jest: Rozsypal a dal chudým, spravedlnost jeho zůstává na věky. (aiōn )
Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ya ba gajiyayyu hannu sake, ayyukansa na alheri madawwama ne.” (aiōn )
10 Ten pak, kterýž dává símě rozsívajícímu, dejž i vám chléb k jedení, a rozmnožiž símě vaše, a přispořiž úrody spravedlnosti vaší,
To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa.
11 Abyste všelijak zbohaceni byli ke všeliké sprostnosti, kteráž působí skrze nás, aby díky činěny byly Bohu.
Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah.
12 Nebo služba oběti této netoliko doplňuje nedostatky svatých, ale také rozhojňuje se v mnohé díků činění Bohu, příčinou schválení služby této,
Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah.
13 Když chválí Boha z jednomyslné poddanosti vaší k evangelium Kristovu, a z upřímé té zdílnosti k sobě i ke všechněm,
Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na’am da bisharar Kiristi, saboda kuma gudummawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake.
14 A modlí se za vás ti, kteříž vás převelice milují pro vyvýšenou milost Boží v vás.
A cikin addu’arsu dominku kuwa, zukatansu za su koma gare ku, saboda mafificin alherin da Allah ya ba ku.
15 Díka pak Bohu z nevymluvného daru jeho.
Godiya ga Allah, saboda kyautarsa da ta wuce misali!