< 1 Timoteovi 6 >
1 Kteřížkoli pod jhem jsou služebníci, ať mají pány své za hodné vší poctivosti, aby jméno Boží a učení nebylo rouháno.
Duk waɗanda suke ƙarƙashin bauta, ya kamata su ɗauki iyayengijinsu a kan sun cancanci girmamawa matuƙa, don kada a ɓata sunan Allah da kuma koyarwarmu.
2 Kteříž pak mají pány věřící, nechažť jich sobě nezlehčují, proto že jsou bratřími, ale tím raději slouží, proto že jsou věřící a milí, dobrodiní Božího účastníci. Tomu vyučuj, a napomínej.
Waɗanda suke da iyayengiji masu bi, to, kada su yi musu reni domin su’yan’uwa ne. A maimako, sai ma su fi bauta musu, saboda waɗanda suke cin moriyar hidimarsu masu bi ne, ƙaunatattu ne kuma a gare su. Waɗannan su ne abubuwan da za ka koya musu ka kuma gargaɗe su.
3 Jestližeť kdo jinak učí, a nepovoluje zdravým řečem Pána našeho Jezukrista, a tomu učení, kteréž jest podlé pobožnosti,
In wani yana koyarwar ƙarya bai kuma yarda da sahihiyar koyarwar Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma koyarwa ta tsoron Allah ba,
4 Nadutýť jest, nic neuměje, ale nemoudrost provodí při otázkách a hádkách o slova, z kterýchž pochází závist, svár, rouhání, zlá domnění,
yana cike da girman kai bai kuma san kome ba. Yana da mugun halin son gardama da muhawwara game da kalmomin da suke kawo kishi, rikici, maganar ƙeta, da mugayen zace-zace
5 Marné hádky lidí na mysli porušených a pravdy zbavených, domnívajících se, že by pobožnost byla zisk tělesný. Takových se varuj.
da yawan tankiya tsakanin mutane masu mugun hali, waɗanda aka raba su da gaskiya, suke kuma tsammani cewa bin Allah wata hanya ce ta samun kuɗi.
6 Jestiť pak zisk veliký pobožnost, s takovou myslí, kteráž na tom, což má, přestati umí.
Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa.
7 Nic jsme zajisté nepřinesli na tento svět, bez pochyby že také nic odnesti nemůžeme.
Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba.
8 Ale majíce pokrm a oděv, na tom přestaneme.
In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su.
9 Kteříž pak chtí zbohatnouti, upadají v pokušení, a v osídlo, a v žádosti mnohé nerozumné a škodlivé, kteréž pohřižují lidi v zahynutí a v zatracení.
Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka.
10 Kořen zajisté všeho zlého jestiť milování peněz, kterýchž někteří žádostivi byvše, pobloudili od víry, a sami se naplnili bolestmi mnohými.
Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri.
11 Ale ty, ó člověče Boží, takových věcí utíkej, následuj pak spravedlnosti, pobožnosti, víry, lásky, trpělivosti, tichosti.
Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali.
12 Bojuj ten dobrý boj víry, dosáhni věčného života, k němuž i povolán jsi, a vyznals dobré vyznání před mnohými svědky. (aiōnios )
Ka yi fama, kyakkyawar fama ta bangaskiya. Ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira saboda shi, sa’ad da ka yi kyakkyawar shaida a gaban shaidu masu yawa. (aiōnios )
13 Přikazujiť tobě před Bohem, kterýž všecko obživuje, a před Kristem Ježíšem, kterýž osvědčil před Pontským Pilátem dobré vyznání,
Na umarce ka, a gaban Allah mai ba da rai ga kome, da kuma Kiristi Yesu wanda yayinda yake ba da shaida a gaban Buntus Bilatus ya yi kyakkyawar shaida,
14 Abys ostříhal přikázaní tohoto, jsa bez poškvrny a bez úhony, až do zjevení se Pána našeho Ježíše Krista,
ka kiyaye wannan umarni ba tare da wani aibi ko abin zargi ba har yă bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi,
15 Kteréž časem svým ukáže ten blahoslavený a sám mocný, Král kralujících, a Pán panujících,
wanda Allah zai kawo a daidai lokaci, Allah, mai albarka wanda yake kaɗai Mai Mulki, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji,
16 Kterýž sám má nesmrtelnost, a přebývá v světle nepřistupitelném, jehož žádný z lidí neviděl, aniž viděti může, kterémužto čest a síla věčná. Amen. (aiōnios )
wanda shi kaɗai ne marar mutuwa wanda kuma yake zaune cikin hasken da ba ya kusatuwa, wanda babu wanda ya taɓa gani ko zai iya gani. A gare shi girma da iko su tabbata har abada. Amin. (aiōnios )
17 Bohatým tohoto světa přikazuj, ať nejsou vysokomyslní, a ať nedoufají v nejistém zboží, ale v Bohu živém, kterýž dává nám hojnost všeho ku požívání. (aiōn )
Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. (aiōn )
18 A ať dobře činí, a bohatnou v dobrých skutcích, a snadní ať jsou k udílení, i přívětiví,
Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako.
19 Skládajíce sobě základ dobrý k času budoucímu, aby dosáhli věčného života.
Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.
20 Ó Timotee, cožť jest svěřeno, ostříhej, utíkaje nepobožných daremních křiků, a odporů falešně nazvaného umění.
Timoti, ka lura da abin da aka danƙa maka amana. Ka yi nesa da masu maganganun rashin tsoron Allah da kuma yawan mūsu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi,
21 Kterýmž někteří chlubíce se, z strany víry pobloudili od cíle. Milost Boží s tebou. Amen.
wanda waɗansu suka furta kuma ta yin haka suka bauɗe daga bangaskiya. Alheri yă kasance tare da ku.