< Titu 1 >

1 Pavao, sluga Božji i apostol Isusa Krista poradi vjere izabranika Božjih i spoznanja istine usmjerene k pobožnosti
Bulus, bawan Allah, kuma manzon Yesu Almasihu, ta wurin bangaskiyar zababbun mutanen Allah da sanin gaskiya da ta yadda da allahntaka.
2 u nadi života vječnoga što ga, prije vremena vjekovječnih, obeća Bog, On koji ne laže, (aiōnios g166)
Wadannan na cikin begen rai marar matuka wanda Allah, wanda babu karya a cikinsa, ya alkawarta kafin dukkan lokatan zamanai. (aiōnios g166)
3 a u svoje doba očitova riječ svoju u propovijedanju koje je meni povjereno po odredbi Spasitelja našega, Boga:
A daidai lokaci, ya bayyana maganarsa ta wurin sakonsa da ya damka mani in shelar. Zan yi wannan ta wurin umarnin Allah mai ceton mu.
4 Titu, pravomu sinu po zajedničkoj vjeri, milost i mir od Boga i Krista Isusa, Spasitelja našega!
Zuwa ga Titus, da' na gaske a cikin bangaskiyarmu. Alheri, jinkai da salama daga wurin Allah Uba da Almasihu Yesu mai ceton mu.
5 Poradi toga ostavih te na Kreti da urediš preostalo te po gradovima postaviš starješine kako sam ti ja odredio:
Sabili da wannan ne na bar ka a Karita domin ka daidaita abubuwan da basu cika ba, ka kuma nada dattibai a dukan birane kamar yadda na umarceka.
6 je li tko besprigovoran, jedne žene muž, jesu li mu djeca vjernici i ne pod optužbom raskalašenosti ili nepokorna...
Dole ne dattijo ya zama marar abin zargi, mijin mace daya, da amintattun 'ya'ya wadanda babu wani zargi na mugunta ko rashin kamun kai a kansu.
7 Jer nadstojnik kao Božji upravitelj treba da bude besprigovoran: ne samoživ, ne jedljiv, ne vinu sklon, ni nasilju, ni prljavu dobitku,
Wajibi ne shugaban Ikklisiya, a matsayin sa na mai kulla da haikalin Allah, ya zama marar aibi. Kada ya zama mai surutu ko rashin hakuri. Kada ya zama mai saurin fushi, ko mashayi, ko mai hayaniya, ko mai handama.
8 nego gostoljubiv, ljubitelj dobra, razuman, pravedan, svet, uzdržljiv,
Maimakon haka, ya zama mai karbar baki, abokin abinda ke mai kyau. Dole ne ya zama mai hankali, adali, cike da allahntaka, da kuma kamun kai.
9 priljubljen uz vjerodostojnu riječ nauka da može i hrabriti u zdravom nauku i uvjeravati protivnike.
Ya zama mai rike amintaccen sakon da aka koyar da karfi, yadda zai iya karfafa wasu da koyarwa mai kyau ya kuma yi wa wadanda suke hamayya da shi gyara.
10 Jer mnogi su nepokorni, praznorječni i zavodnici, ponajpače oni iz obrezanja.
Domin akwai kangararrun mutane dayawa, musamman masu kaciya. Maganganunsu na banza ne. Suna yaudara kuma suna badda mutane.
11 Njima treba začepiti usta jer cijele domove prevraćaju naučavajući što ne bi smjeli, i to poradi prljava dobitka.
Wajibi ne mu hana su. Suna koyar da abinda bai kamata su koyar ba saboda makunyaciyar riba suna kuma rusar da iyalai dungum.
12 Reče netko od njih, njihov vlastiti prorok: “Krećani uvijek lašci, opake zvijeri, trbusi dangubni.”
Daya daga cikinsu, kuma mai hikima ne daga cikinsu, yace, “Kirawa manyan makaryata ne, lalatattu kuma miyagun dabbobi, masu kyiuya da zarin cin abinci.”
13 Svjedočanstvo je to istinito. Zato ih karaj oštro da budu zdravi u vjeri,
Wannan magana gaskiya ne, ka yi masu gyara da tsanani yadda zasu kafu a cikin bangaskiya.
14 da ne prianjaju uza židovske bajke i propise ljudi koji se odvraćaju od istine.
Kada ka mai da hankalin ka ga tatsunniyoyi na Yahudawa ko dokokin mutane wadanda sun sauya gaskiya.
15 Sve je čisto čistima; okaljanima pak i nevjernima ništa čisto, nego su im okaljani i razum i savjest.
Ga wadanda suke da tsarki, komai mai tsarki ne. Amma wadanda suke marasa tsarki da rashin bangaskiya, komai marar tsarki ne. Domin zuciyarsu da lamirinsu sun gurbata.
16 Ispovijedaju da Boga poznaju, ali djelima ga niječu - odvratni, neposlušni i za koje god dobro djelo nepodesni.
Suna cewa sun san Allah, amma sun musanta shi ta wurin ayyukansu. Sun zama abin kyama da marasa biyayya. Ba za a iya tabbaatar dasu ba akan wani aiki maikyau.

< Titu 1 >