< Rimljanima 2 >
1 Zato nemaš isprike, čovječe koji sudiš, tko god ti bio. Jer time što drugoga sudiš, sebe osuđuješ: ta to isto činiš ti što sudiš.
Saboda da haka baka da hujja, kai mutum, kai mai shara'antawa, domin kuwa abinda kake shara'antawa akan wasu kana kada kanka da kanka. Domin kuwa kai mai shar'antaawa kana aikata wadannan abubuwa.
2 Znamo pak: Bog po istini sudi one koji takvo što čine.
Amma mun san cewa shari'ar Allah ta gaskiya ce sa'adda zata fado wa masu aikata wadannan irin abubuwa.
3 Misliš li da ćeš izbjeći sudu Božjemu, ti čovječe što sudiš one koji takvo što čine, a sam to isto činiš?
Amma ka lura da wannan, ya kai mutum, mai shara'anta masu aikata wadannan ababuwa. Duk da shike kaima kana aikatawa. Kana jin zaka kubucewa hukuncin Allah?
4 Ili prezireš bogatstvo dobrote, strpljivosti i velikodušnosti njegove ne shvaćajući da te dobrota Božja k obraćenju privodi?
Ko kana raina falalar alheransa da yake yi ta wajen jinkirin hukuncinsa, da hakurinsa? Baka san cewa alheransa musanman domin su kai ka ga tuba bane?
5 Tvrdokornošću svojom i srcem koje neće obraćenja zgrćeš na se gnjev za Dan gnjeva i objavljenja pravedna suda Boga
Amma saboda taurin kanka da zuciyarka marar tuba, kana tanadarwa kanka fushi, a ranar fushi, wato ranar bayyanuwar shari'ar adalci ta Allah.
6 koji će uzvratiti svakom po djelima:
Zai baiwa kowanne mutum daidai sakamakon ayyukansa:
7 onima koji postojanošću u dobrim djelima ištu slavu, čast i neraspadljivost - život vječni; (aiōnios )
Ga wadanda kuma suka nace da yin ayyukan alheri ba fasawa, sun samarwa kansu, yabo da daraja, da rai na har'abada. (aiōnios )
8 buntovnicima pak i nepokornima istini, a pokornima nepravdi - gnjev i srdžba!
Amma ga masu son kai, wadanda suka ki yin biyayya ga gaskiya, suka yiwa rashin adalci biyayya, fushi da hasala mai zafi zai afko masu.
9 Nevolja i tjeskoba na svaku dušu čovječju koja čini zlo, na Židova najprije, pa na Grka;
Allah kuma zai sauko da bala'i da bakin ciki ga dukkan rayukan da suka aikata mugunta, ga Yahudawa da fari, sannan kuma Hellinawa.
10 a slava, čast i mir svakomu koji čini dobro, Židovu najprije, pa Grku!
Amma yabo daraja da salama zasu kasance ga dukkan wadanda suka aikata ayukan alheri, ga Yahudawa da fari sannan Hellanawa.
11 Ta u Boga nema pristranosti.
Domin kuwa Allah ba mai tara bane.
12 Uistinu koji bez Zakona sagriješiše, bez Zakona će i propasti; i koji pod Zakonom sagriješiše, po Zakonu će biti suđeni.
Ga wadanda suka yi zunubi batare da shari'aba, zasu hallaka ba tare da shari'a ba, ga wadanda suka yi zunubi cikin shari'a kuma za'a hukunta su bisa ga shari'a.
13 Ne, pred Bogom nisu pravedni slušatelji Zakona, nego - izvršitelji će Zakona biti opravdani.
Domin kuwa ba masu jin shari'ar ne masu adalci agaban Allah ba, amma masu aikatawa ne zasu samu barata.
14 Ta kad se god pogani, koji nemaju Zakona, po naravi drže Zakona, i nemajući Zakona, oni su sami sebi Zakon:
Gama al'umai da basu san shari'a ba, bisa ga dabi'a sun yi abinda ke na shari'a, sun kuma zame wa kansu shari'a, koda shike basu da shari'ar.
15 pokazuju da je ono što Zakon nalaže upisano u srcima njihovim. O tom svjedoči i njihova savjest, a i prosuđivanja kojima se među sobom optužuju ili brane.
Dalilin haka kuwa sun nuna cewa ayukan da shari'a take bukata na nan a rubuce a zuciyarsu. lamirinsu kuma na yi masu shaida, tunanainsu kuma, ko dai yana kashe su, ko kuma yana karesu.
16 To će se očitovati na Dan u koji će, po mojem evanđelju, Bog po Isusu Kristu suditi ono što je skriveno u ljudima.
hakanan kuma ga Allah. Wannan zai faru ranar da Allah zai shara'anta asiran boye na dukkan mutane, bisa ga bishara ta cikin Yesu Almasihu.
17 Ako pak ti koji se Židovom nazivaš, koji mirno počivaš na Zakonu i dičiš se Bogom,
Da shike kana kiran kanka Bayahude, kana zaune akan shari'a, kana alfahari cikin Allah,
18 koji poznaješ Volju i iz Zakona poučen razlučuješ što je bolje
ka san nufinsa, ka kuma san abubuwan da suka bambanta da hakan, ka kuma sami koyarwa cikin shari'ar.
19 te si uvjeren da si vođa slijepih, svjetlo onih u tami,
Da shike kana da gabagadi akan cewa kai jagora ne ga makafi, haske ga wadanda suke cikin duhu,
20 odgojitelj nerazumnih, učitelj nejačadi jer u Zakonu imaš oličenje znanja i istine;
mai horo ga marasa hikima, mai koyar da jarirai, kuma a cikin shari'ar kana da abin da ya shafi sani da kuma gaskiya.
21 ti, dakle, koji drugoga učiš, sam sebe ne učiš! Ti koji propovijedaš da se ne krade, kradeš!
ku da kuke koyar da wadansu, ba ku koyar da kanku? ku da kuke wa'azi kada ayi sata, ba ku yin sata?
22 Ti koji zabranjuješ preljub, preljub počinjaš! Ti komu su odvratni kumiri, pljačkaš hramove!
Ku da ke wa'azi kada ayi zina, ba ku yin zina? ku da ke hana bautar gumaka, ba ku yin sata a haikali?
23 Ti koji se Zakonom dičiš, kršenjem toga Zakona Boga obeščašćuješ!
ku masu murna da tinkaho cikin shari'ar, ba kwa wulakanta Allah cikin kurakuranku na rashin bin shari'a?
24 Doista, kako je pisano, ime se Božje zbog vas huli među narodima.
''Domin kuwa an wulakanta sunan Allah cikin Al'umai sabili da ku,'' kamar yadda aka riga aka rubuta.
25 Da, obrezanje koristi ako vršiš Zakon; ako pak kršiš Zakon, obrezanje tvoje postalo je neobrezanje.
Lallai kuwa kaciya tana da riba a gare ku, idan kuka kiyaye doka, amma idan ku marasa bin doka ne kaciyarku ta zama rashin kaciya.
26 Ako dakle neobrezani opslužuje propise Zakona, neće li se njegovo neobrezanje smatrati obrezanjem?
domin kuwa idan mutum marar kaciya zai kiyaye dukkan bukatun doka, baza'a iya daukan rashin kaciyarsa a matsayin mai kaciya ba?
27 I onaj koji je podrijetlom neobrezanik, a ispunja Zakon, sudit će tebi koji si, uza sve slovo i obrezanje, prijestupnik Zakona.
Sannan idan mutum marar kaciya ta jini zai kiyaye dukkan dokoki, ba zai iya shara'anta ku masu kaciya ta shari'a ba? Haka kuma ya kasance ne domin kuna da shari'a a rubuce da kuma kaciya amma ba kwa bin doka!
28 Ta nije Židov tko je Židov naizvana i nije obrezanje ono izvana,
Domin shi kuwa ba Bayahude bane a waje; ba kuwa mai kaciyar da aka tsaga fata ba.
29 na tijelu, nego pravi je Židov u nutrini i pravo je obrezanje u srcu, po duhu, ne po slovu. Pohvala mu nije od ljudi, nego od Boga.
Amma Bayahude ne ta ciki, sanna kuma mai kaciyar zuciya da kuma ruhu ba wasika ba, irin wanna mutumin yabonsa ba daga wurin mutane yake zuwa ba, amma daga Allah.