< Luka 5 >

1 Dok se jednom oko njega gurao narod da čuje riječ Božju, stajaše on pokraj Genezaretskog jezera.
Ya zama sa'adda mutane sun taru a wurin Yesu suna sauraron maganar Allah, yana kuma yana tsaye a bakin tabkin Janisarata.
2 Spazi dvije lađe gdje stoje uz obalu; ribari bili izašli iz njih i ispirali mreže.
Ya ga jiragen ruwa biyu tsaye a bakin tabkin. Masu kamun kifin kuwa sun fita daga cikin jiragen suna wanke tarunsu.
3 Uđe u jednu od tih lađa; bila je Šimunova pa zamoli Šimuna da malo otisne od kraja. Sjedne te iz lađe poučavaše mnoštvo.
Yesu ya shiga daya daga cikn jiragen wanda shike na Bitrus ne, sai ya umarce shi ya dan zakuda da jirgin daga bakin tabkin kadan zuwa cikin ruwa. Sai ya zauna ya kuma koya wa mutane daga cikin jirgin.
4 Kada dovrši pouku, reče Šimunu: “Izvezi na pučinu i bacite mreže za lov.”
Da ya gama magana, ya ce wa Siman, “Zakuda jirgin zuwa wuri mai zurfi sa'annan ka zuba tarunka domin kamu.”
5 Odgovori Šimun: “Učitelju, svu smo se noć trudili i ništa ne ulovismo, ali na tvoju riječ bacit ću mreže.”
Siman ya amsa ya ce, “Ubangiji, mun yi aiki dukan dare bamu kama komai ba, amma bisa ga maganarka, zan jefa tarun.”
6 Učiniše tako te uhvatiše veoma mnogo riba; mreže im se gotovo razdirale.
Da sun yi haka, suka kama kifaye da yawan gaske, har tarunsu suna yagewa.
7 Mahnuše drugovima na drugoj lađi da im dođu pomoći. Oni dođoše i napuniše obje lađe, umalo im ne potonuše.
Sai suka roki abokan aikinsu da ke a dayan jirgin su zo su taimake su. Suka zo sun cika jiragen biyu da kifaye, har suka fara nutsewa.
8 Vidjevši to, Šimun Petar pade do nogu Isusovih govoreći: “Idi od mene! Grešan sam čovjek, Gospodine!”
Amma Siman Bitrus, da ya ga haka, ya russuna a gaban Yesu, yana cewa, “Ka rabu da ni Ubangiji, gama ni mai zunubi ne.”
9 Zbog lovine riba što ih uloviše bijaše se zapanjio on i svi koji bijahu s njime,
Domin ya yi mamaki, da dukan wadanda suke tare da shi, sabili da yawan kifaye da suka kama.
10 a tako i Jakov i Ivan, Zebedejevi sinovi, drugovi Šimunovi. Isus reče Šimunu: “Ne boj se! Odsada ćeš loviti ljude!”
Wannan ya hada da Yakubu da Yahaya 'ya'yan Zabadi abokan aikin Siman. Sai Yesu ya ce wa Siman, “Kada ka ji tsoro, domin daga yanzu, za ka kama mutane.”
11 Oni izvukoše lađe na kopno, ostaviše sve i pođoše za njim.
Da sun kawo jiragensu waje kan kasa, suka bar komai suka kuma bi shi.
12 I dok bijaše u jednom gradu, gle čovjeka puna gube! Ugledavši Isusa, padne ničice i zamoli ga: “Gospodine, ako hoćeš, možeš me očistiti.”
Sa'adda yana daya daga cikin biranen, wani mutum dauke da kuturta yana nan wurin. Da ya ga Yesu, ya fadi bisa fuskarsa kasa yana rokansa, yana cewa, “Ubangji, idan ka yarda, za ka iya tsarkake ni.”
13 Isus pruži ruku i dotakne ga se govoreći: “Hoću, očisti se!” I odmah nesta gube s njega.
Yesu ya mika hanunsa ya taba shi, yana cewa, “Na yarda. Ka tsarkaka.” Sai nan da nan, kuturtar ta rabu da shi.
14 I zapovjedi mu: “Nikome ni riječi, nego otiđi, pokaži se svećeniku i prinesi za svoje očišćenje kako propisa Mojsije, njima za svjedočanstvo.”
Ya umarce shi kada ya gaya wa kowa, amma ya ce ma sa, “Tafi ka nuna kanka ga firist sa'annan ka mika hadaya domin tsarkakewarka, kamar yadda Musa ya umarta, a matsayin shaida a garesu.”
15 Glas se o njemu sve više širio i silan svijet grnuo k njemu da ga sluša i da ozdravi od svojih bolesti.
Amma labarinsa ya bazu nesa, taron mutane da yawa kuma suka zo wurinsa domin su ji shi, su kuma samu warkarwa daga cututtukansu.
16 A on se sklanjao na samotna mjesta da moli.
Amma ya kan janye zuwa wuraren da babu kowa ya yi addu'a.
17 I jednog je dana on naučavao. A sjeđahu ondje farizeji i učitelji Zakona koji bijahu došli iz svih galilejskih i judejskih sela i Jeruzalema. A sila ga je Gospodnja nukala da liječi.
Ya zama daya a cikin kwanakin da yake koyarwa, akwai Farisawa da malaman attaura da ke zaune a wurin wandanda suka zo daga kauyukan da suke kewaye da Galili da Yahudiya da kuma birnin Urushalima. Ikon Ubangiji yana tare da shi domin warkarwa.
18 I gle, ljudi doniješe na nosiljci čovjeka koji bijaše uzet. Tražili su da ga unesu i stave preda nj.
A lokacin nan, wasu mutane suka zo dauke da wani mutum shanyayye a kan tabarma, suka kuma nemi yadda za su shigar da shi ciki, su kwantar da shi a gaban Yesu.
19 Budući da zbog mnoštva nisu našli kuda bi ga unijeli, popnu se na krov te ga između crepova s nosiljkom spuste u sredinu pred Isusa.
Ba su iya samun hanyar da za su shigar da shi ba saboda taron, sai suka hau saman gidan, suka saukar da shi daga rufin, a kan tabarman sa, zuwa tsakiyar mutanen, dai dai a gaban Yesu.
20 Vidjevši njihovu vjeru reče on: “Čovječe, otpušteni su ti grijesi!”
Da ya ga bangaskiyarsu, Yesu ya ce, “Maigida, an gafarta zunubanka.”
21 Pismoznanci i farizeji počeše mudrovati: “Tko je ovaj što huli? Tko može grijehe otpuštati doli Bog jedini?”
Marubuta da Farisawa suka fara sukar wannan, suna cewa, “Wanene wannan da ke sabo? Wa zai iya gafarta zunubi, idan ba Allah kadai ba?”
22 Proniknuvši njihovo mudrovanje, upita ih Isus: “Što mudrujete u sebi?
Amma da Yesu ya fahimci abin da suke tunani, sai ya amsa ya ce masu, “Don me kuke sukar wannan a zuciyarku?
23 Što je lakše? Reći: 'Otpušteni su ti grijesi' ili reći: 'Ustani i hodi?'
Wanne ne ya fi sauki a ce, 'An yafe zunubanka' ko kuwa a ce, 'Tashi ka yi tafiya?”
24 Ali da znate: Vlastan je Sin Čovječji na zemlji otpuštati grijehe!” I reče uzetomu: “Tebi zapovijedam: ustani, uzmi nosiljku i idi kući!”
Amma domin ku sani cewa Dan Mutum yana da yancin gafarta zunubai a duniya, na ce maka, 'Tashi, dauki tabarmanka, ka tafi gidanka.'”
25 I on odmah usta pred njima, uze na čemu ležaše i ode kući slaveći Boga.
Nan take, ya tashi a gabansu ya dauki tabarma da yake kwance; sai ya koma gidansa, yana daukaka Allah.
26 A sve obuze zanos te su slavili Boga i puni straha govorili: “Danas vidjesmo nešto neviđeno!”
Kowa yana ta mamaki kuma suka daukaka Allah. Suna cike da tsoro, suna cewa, “Yau mun ga abubuwan al'ajibi.”
27 Nakon toga iziđe i ugleda carinika imenom Levija gdje sjedi u carinarnici. I reče mu: “Pođi za mnom!”
Bayan wadannan abubuwa sun faru, Yesu ya fito daga can sai ya ga wani mai karban haraji mai suna Lawi yana zama a wurin karban haraji. Ya ce masa, “Ka biyo ni.”
28 On sve ostavi, usta i pođe za njim.
Sai Lawi ya bar komai, ya tashi, ya bi shi.
29 I Levi mu u svojoj kući priredi veliku gozbu. A s njime bijaše za stolom veliko mnoštvo carinika i drugih.
Lawi kuma ya shirya gagarumar liyafa a gidansa, kuma akwai masu karban haraji da yawa a nan, da wasu mutane da ke zama a gaban teburin liyafar suna cin abinci tare da su.
30 Farizeji i pismoznanci njihovi negodovahu i govorahu njegovim učenicima: “Zašto s carinicima i grešnicima jedete i pijete?”
Amma Farisawa da Marubuta suka fara korafi ga almajiransa, suna cewa, “Don menene kuna ci da sha tare da masu karban haraji da mutane masu zunubi?”
31 Isus im odgovori: “Ne treba zdravima liječnika, nego bolesnima.
Yesu ya amsa masu, “Masu lafiya basu bukatar likita, wadanda ke marasa lafiya kadai ke bukatar likita.
32 Nisam došao zvati pravedne, nego grešnike na obraćenje.”
Ban zo domin kiran masu adalci ba, amma na zo ne domin kiran masu zunubi zuwa ga tuba.”
33 A oni mu rekoše: “Učenici Ivanovi, a tako i farizejski, počesto poste i obavljaju molitve, tvoji pak jedu i piju.”
Sun ce masa, “Almajiran Yahaya sukan yi azumi da addu'a, kuma almajiran Farisawa ma sukan yi haka. Amma almajiranka suna ci suna sha?”
34 Reče im Isus: “Ne možete svatove prisiliti da poste dok je zaručnik s njima.
Yesu ya ce masu, “Akwai wanda zai sa abokan ango su yi azumi, a lokacin da shi ango yana tare da su?
35 Doći će već dani: kad im se ugrabi zaručnik, tada će postiti, u one dane!”
Amma kwanaki na zuwa wadanda za a dauke ango daga wurinsu, a kwanakin za su yi azumi.”
36 A kazivao im je i prispodobu: “Nitko neće otparati krpe s novog odijela da je stavi na staro odijelo. Inače će i novo rasparati, a starom neće pristajati krpa s novoga.”
Sai Yesu ya sake fada masu wani misali. “Babu wanda zai yage kyalle daga sabuwar tufa, ya kuma yi amfani da ita ya dinka tsohuwar tufa. Idan ya yi hakannan, zai yage sabuwar tufar, kuma kyallen daga sabuwar tufar ba zai dace da kyallen tsohuwar tufar ba.
37 “I nitko ne ulijeva novo vino u stare mješine. Inače će novo vino proderati mješine pa će se i ono proliti i mješine će propasti.
Kuma, babu mutum da zai sa sabon ruwan inabi a cikin tsofafin salkuna. Idan ya yi haka, sabon ruwan inabin zai fasa salkunan, kuma ruwan inabin din zai zube, salkunan kuma za su lallace.
38 Nego, novo vino neka se ulijeva u nove mješine!”
Amma dole ne a sa sabon ruwan inabi a sabobin salkuna.
39 “I nitko pijuć staro, ne zaželi novoga. Ta veli se: 'Valja staro!'”
Babu wanda zai yi marmarin sabon ruwan inabi bayan da ya sha tsohon, gama zai ce, “Tsohon ya fi sabon.”

< Luka 5 >