< Ivan 15 >

1 “Ja sam istinski trs, a Otac moj - vinogradar.
“Nine itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomin.
2 Svaku lozu na meni koja ne donosi roda on siječe, a svaku koja rod donosi čisti da više roda donese.
Yakan cire duk wani rashe a cikina da ba ya bada 'ya'ya, mai bada 'ya'ya kuwa ya kan gyara shi domin ya kara bada 'ya'ya.
3 Vi ste već očišćeni po riječi koju sam vam zborio.
Kun rigaya kun tsarkaka saboda maganar da na yi muku.
4 Ostanite u meni i ja u vama. Kao što loza ne može donijeti roda sama od sebe, ako ne ostane na trsu, tako ni vi ako ne ostanete u meni.
Ku zauna ciki na, Ni kuma cikin ku. Kamar yadda reshe ba ya iya bada 'ya'ya shi kadai sai ya zauna cikin itacen, haka kuma ba za ku iya ba, sai kun zauna ciki na.
5 Ja sam trs, vi loze. Tko ostaje u meni i ja u njemu, taj donosi mnogo roda. Uistinu, bez mene ne možete učiniti ništa.
Ni ne itacen inabi, ku ne rassan. Wanda ya zauna ciki na, ni kuma cikin sa, yana bada 'ya'ya dayawa, gama in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba.
6 Ako tko ne ostane u meni, izbace ga kao lozu i usahne. Takve onda skupe i bace u oganj te gore.
Wanda kuma bai zauna a ciki na ba, akan jefar da shi kamar reshe, ya bushe, kuma sukan tattara rassan su jefa a wuta, su kone.
7 Ako ostanete u meni i riječi moje ako ostanu u vama, što god hoćete, ištite i bit će vam.
In kun zauna a ciki na, maganata kuma ta zauna a cikin ku, sai ku roki duk abinda kuke so, za a kuwa yi maku.
8 Ovim se proslavlja Otac moj: da donosite mnogo roda i da budete moji učenici.
Ta haka ake daukaka Ubana: cewa ku bada 'ya'ya dayawa, kuma cewa ku almajiraina ne.
9 Kao što je Otac ljubio mene tako sam i ja ljubio vas; ostanite u mojoj ljubavi.
Kamar yadda Ubana ya kaunace ni, haka Ni ma na kaunace ku; Ku zauna cikin kaunata.
10 Budete li čuvali moje zapovijedi, ostat ćete u mojoj ljubavi; kao što sam i ja čuvao zapovijedi Oca svoga te ostajem u ljubavi njegovoj.
Idan kun kiyaye dokokina, za ku zauna cikin kaunata kamar yadda Na kiyaye dokokin Ubana, na kuma zauna cikin kaunarsa.
11 To sam vam govorio da moja radost bude u vama i da vaša radost bude potpuna.
Ina gaya maku wadannan al'amura domin farincikina ya kasance a cikin ku, kuma domin farincikinku ya zama cikakke.
12 Ovo je moja zapovijed: ljubite jedni druge kao što sam ja vas ljubio!
“Wannan shine umarnina, cewa ku kaunaci juna kamar yadda na kaunace ku.
13 Veće ljubavi nitko nema od ove: da tko život svoj položi za svoje prijatelje.
Babu wanda ke da kaunar da tafi haka, wato ya bada ransa domin abokansa.
14 Vi ste prijatelji moji ako činite što vam zapovijedam.
Ku abokaina ne idan kuna yin abubuwan da na umarce ku.
15 Više vas ne zovem slugama jer sluga ne zna što radi njegov gospodar; vas sam nazvao prijateljima jer vam priopćih sve što sam čuo od Oca svoga.
Nan gaba ba zan kara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abinda Ubangijinsa ke yi ba. Na kira ku abokaina, domin na sanar da ku duk abinda na ji daga wurin Ubana.
16 Ne izabraste vi mene, nego ja izabrah vas i postavih vas da idete i rod donosite i rod vaš da ostane te vam Otac dadne što ga god zaištete u moje ime.
Ba ku kuka zabe ni ba, amma Ni ne na zabe ku, na aike ku don ku je ku bada 'ya'ya, 'ya'yanku kuma su tabbata. Wannan ya zama domin duk abinda kuka roki Uba a cikin sunana, zai baku.
17 Ovo vam zapovijedam: da ljubite jedni druge.”
Na baku wannan umarni: domin ku kaunaci juna.
18 “Ako vas svijet mrzi, znajte da je mene mrzio prije nego vas.
In duniya ta ki ku, ku sani cewa ta kini kafin ta ki ku.
19 Kad biste bili od svijeta, svijet bi svoje ljubio; no budući da niste od svijeta, nego sam vas ja izabrao iz svijeta, zbog toga vas svijet mrzi.
Da ku na duniya ne, da duniya ta kaunace ku kamar nata. Amma saboda ku ba na duniya bane, na kuma zabe ku daga duniya, don haka duniya take kin ku.
20 Sjećajte se riječi koju vam rekoh: 'Nije sluga veći od svoga gospodara.' Ako su mene progonili, i vas će progoniti; ako su moju riječ čuvali, da vašu će čuvati.
Ku tuna da maganar da na yi muku, 'Bawa ba ya fi Ubangijinsa girma ba.' Idan sun tsananta mani, ku ma za su tsananta maku; Idan sun kiyaye maganata, za su kuma kiyaye maganarku.
21 A sve će to poduzimati protiv vas poradi imena moga jer ne znaju onoga koji mene posla.
Za su yi maku duk wadannan abubuwa saboda sunana, don basu san wanda ya aiko ni ba.
22 Da nisam došao i da im nisam govorio, ne bi imali grijeha; no sada nemaju izgovora za svoj grijeh.
Da ban zo na yi masu magana ba, da basu da zunubi, amma yanzu, basu da wata hujja don zunubinsu.
23 Tko mene mrzi, mrzi i Oca mojega.
Duk wanda ya ki ni ya ki Ubana.
24 Da nisam učinio među njima djela kojih nitko drugi ne čini, ne bi imali grijeha; a sada vidješe pa ipak zamrziše i mene i Oca mojega.
Da ban yi ayyukan da babu wanda ya taba yinsu a cikin su ba, da basu da zunubi, amma yanzu sun gani, sun kuma ki ni da Ubana duka.
25 No neka se ispuni riječ napisana u njihovu Zakonu: Mrze me nizašto.
An yi wannan kuwa domin a cika maganar da ke rubuce a cikin shari'arsu, ' Sun ki ni ba dalili.'
26 A kada dođe Branitelj koga ću vam poslati od Oca - Duh Istine koji od Oca izlazi - on će svjedočiti za mene.
Sa'adda Mai Ta'aziya- wanda zan aiko maku daga wurin Uban, wato, Ruhun gaskiya, wanda ke fita daga wurin Uban-ya zo, zai bada shaida a kai na.
27 I vi ćete svjedočiti jer ste od početka sa mnom.
Ku ma kuna bada shaida saboda kuna tare da ni tun daga farko.

< Ivan 15 >