< Efežanima 1 >
1 Pavao, po volji Božjoj apostol Krista Isusa: svetima koji su u Efezu i vjernima u Isusu Kristu.
Bulus, manzon Yesu Almasihu ta wurin nufin Allah, zuwa ga kebabbu na Allah da ke a Afisa wanda suke aminci cikin Yesu.
2 Milost vam i mir od Boga, Oca našega, i Gospodina Isusa Krista!
Bari alheri ya kasance da ku, da salama daga wurin Allah Ubanmu da Ubangijinmu Yesu Almasihu.
3 Blagoslovljen Bog i Otac Gospodina našega Isusa Krista, on koji nas blagoslovi svakim blagoslovom duhovnim u nebesima, u Kristu.
Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu. Shine ya albarkace mu da kowanne albarku na ruhaniya da ke cikin sammai cikin Almasihu.
4 Tako: u njemu nas sebi izabra prije postanka svijeta da budemo sveti i bez mane pred njim;
Kafin halitar duniya, Allah ya zabe mu da muka ba da gaskiya cikin Yesu. Ya zabe mu domin mu yi zaman tsarki da rayuwar da babu aibu a gabansa.
5 u ljubavi nas predodredi za posinstvo, za sebe, po Isusu Kristu, dobrohotnošću svoje volje,
Cikin kauna Allah ya kaddara ya dauke mu mu zama yayansa ta wurin Yesu almasihu. Ya yi wannan domin ya gamshe shi ya yi abin da ya ke so.
6 na hvalu Slave svoje milosti. Njome nas zamilova u Ljubljenome
Sakamakon shine Allah ya karbi yabo domin daukakan alherinsa. Wannan shine abinda ya ba mu hannu sake ta wurin kaunataccensa.
7 u kome, njegovom krvlju, imamo otkupljenje, otpuštenje prijestupa po bogatstvu njegove milosti.
Gama cikin kaunataccensa aka fanshe mu ta wurin jininsa, da gafarar zunubai ta wurin wadataccen alherinsa.
8 Nju preobilno u nas uli zajedno sa svom mudrošću i razumijevanjem
Ya ba da wannan alherin a yalwace cikin dukan hikima da fahimta.
9 obznanivši nam otajstvo svoje volje po dobrohotnom naumu svojem što ga prije u njemu zasnova
Allah ya bayyana mana gaskiyar al'amarin da aka boye na shirinsa, ta wurin abin da yake so ya nuna cikin Almasihu.
10 da se provede punina vremena: uglaviti u Kristu sve - na nebesima i na zemlji.
Idan lokaci ya yi na kammala shirinsa, Allah zai kawo dukan abubuwan da ke sama da kasa cikin Yesu.
11 U njemu, u kome i nama - predodređenima po naumu Onoga koji sve izvodi po odluci svoje volje - u dio pade
An zabe mu cikin Almasihu mu zama abin gado na Allah. Ya yi mana wannan shirin tun da cikin shirin sa, shi mai yin dukan abu ta dalilin nufinsa.
12 da budemo na hvalu Slave njegove - mi koji smo se već prije nadali u Kristu.
Allah ya yi haka saboda mu rayu domin yabon daukakarsa. Mune na farko da muka sami bege cikin Almasihu.
13 U njemu ste i vi, pošto ste čuli Riječ istine - evanđelje spasenja svoga - u njemu ste, prigrlivši vjeru, opečaćeni Duhom obećanim, Svetim,
A cikin Almasihu ne kuma kuka samu jin maganar gaskiya, bisharan cetonku ta wurin Yesu. A cikinsa ne kuka bada gaskiya aka hatimce ku da Ruhu Mai Tsarki wanda aka alkawarta.
14 koji je zalog naše baštine: otkupljenja, posvojenja - na hvalu Slave njegove.
Ruhun shine tabbacin gadonmu kafin mu kai ga samunsa. Wannan don yabon daukakarsa ne.
15 Zato i ja, otkad sam čuo za vašu vjeru u Gospodinu Isusu i za ljubav prema svima svetima,
Sabo da haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kaunar ku zuwa dukan wadanda aka kebe dominsa.
16 ne prestajem zahvaljivati za vas i sjećati vas se u svojim molitvama:
Ban fasa tunawa da ku ba ina addu'a saboda ku cikin addu'o'ina.
17 Bog Gospodina našega Isusa Krista, Otac Slave, dao vam Duha mudrosti i objave kojom ćete ga spoznati;
Ina addu'a da cewa Allah Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uban daraja, ya ba ku ruhun basira da wahayin saninsa.
18 prosvijetlio vam oči srca da upoznate koje li nade u pozivu njegovu, koje li bogate slave u baštini njegovoj među svetima
Ina addu'a idanun zuciyarku su bude domin ku san tabacin kiranku. Ina addu'a dominku san arzikin mulkin gadonsa cikin wadanda aka kebe dominsa.
19 i koje li prekomjerne veličine u moći njegovoj prema nama koji vjerujemo: ona je primjerena djelotvornosti sile i snage njegove
Ina addu'a ku san ikon nan nasa mai girma mara iyaka da ke cikin mu da muka ba da gaskiya. Wannan girman yana ta wurin aikin karfin ikonsa ne.
20 koju na djelu pokaza u Kristu, kad ga uskrisi od mrtvih i posjede sebi zdesna na nebesima
Wannan shine ikon da ya yi aiki cikin Almasihu lokacin da Allah ya tashe shi daga matattu ya sa shi a hannun damansa cikin sammai.
21 iznad svakog Vrhovništva i Vlasti i Moći i Gospodstva i svakog imena imenovana ne samo na ovom svijetu nego i u budućemu. (aiōn )
Ya sanya shi bisa birbishin dukan sarauta, iko, mulki, karfi, da kowanne irin suna. Ya sanya Almasihu ba a wannan zamanin kadai ba, amma da zamani mai zuwa. (aiōn )
22 Sve mu podloži pod noge, a njega postavi - nad svime - Glavom Crkvi,
Allah ya saka dukan abubuwa a karkashin kafafun Almasihu. Ya sa shi shugaban dukan abubuwa a cikin ikilisiya.
23 koja je Tijelo njegovo, punina Onoga koji sve u svima ispunja.
Ikilisiya jikinsa ne, cikarsa wanda ya cika dukan abubuwa cikin kowacce hanya.