< 2 Korinčanima 9 >

1 A o posluživanju svetih suvišno je da vam pišem.
Game da hidima domin tsarkaka, ya dace in rubuta maku.
2 Ta poznajem vašu spremnost s koje se vama ponosim pred Makedoncima: “Ahaja je spremna od prošle godine.” I vaša gorljivost potaknu mnoge.
Na san marmarinku, wanda na yi fahariya da shi a gaban mutanen Makidoniya. Na gaya masu Akaya sun riga sun shirya tun bara. Kwazon ku ya sa yawancin su sun shiga aiki.
3 Ipak šaljem braću da se u tome pogledu ne opovrgne što se vama ponosimo; da budete spremni kao što sam tvrdio te se -
To na aiko maku da 'yan'uwa saboda kada fahariyarmu akanku ta zama a banza, domin kuma ku zauna a shirye, kamar yadda na ce za ku yi.
4 ako sa mnom dođu Makedonci i nađu vas nespremne - ne osramotimo s preuzetnosti mi, da ne kažemo vi.
Idan kuwa ba haka ba, idan wani cikin makidoniyawa ya biyoni kuma ya tarar da baku shirya ba, za mu ji kunya-ba ni cewa komai game da ku-domin ina da gabagadi a kan ku.
5 Smatrao sam dakle potrebnim zamoliti braću da unaprijed pođu k vama i da pripreme vaš još prije obećani dar te bude pripravan - kao dar darežljivosti, a ne škrtosti.
Sai na ga ya dace in turo 'yan'uwa su zo wurin ku kafin lokaci yayi suyi shirye shirye game da gudummuwar da kuka yi alkawari. Wannan ya zama haka ne domin a shirya shi a matsayin bayarwar albarka, ba wani abin kwace ba.
6 Ta eno: tko sije oskudno, oskudno će i žeti; a tko sije obilato, obilato će i žeti.
Batun shine: wanda ya shuka kadan zai girbi kadan, wanda kuma ya shuka da manufar albarka zai girbi albarka
7 Svatko neka dade kako je srcem odlučio; ne sa žalošću ili na silu jer Bog ljubi vesela darivatelja.
Bari kowa ya bayar bisa ga yadda ya yi niyya a zuciyarsa. Kada ya bayar da bacin rai ko kamar dole. Gama Allah yana kaunar mai bayarwa da dadin rai.
8 A Bog vas može obilato obdariti svakovrsnim darom da u svemu svagda imate svega dovoljno za se i izobilno za svako dobro djelo -
Allah na da ikon ya sa kowace albarka ta ribanbanya domin ku, domin, a koyaushe, a cikin dukan abubuwa, ku sami duk abinda kuke bukata. Hakan zai kasance domin ku ribabbanya kowanne kyakkyawan aiki.
9 kao što je pisano: Rasipno dijeli, daje sirotinji, pravednost njegova ostaje dovijeka. (aiōn g165)
Kamar yadda aka rubuta, ''Ya rarraba arzikinsa, ya bada shi ga matalauta. Adalcinsa ya dawwama har abada.'' (aiōn g165)
10 A onaj koji pribavlja sjeme sijaču i kruh za jelo, pribavit će i umnožiti sjeme vaše i povećati plodove pravednosti vaše.
Shi wanda ke bayar da iri ga mai shuka da gurasa domin abinci, zai bayar ya kuma ribabbanya maku iri domin shuka. Zai sa girbin adalcinku ya karu.
11 Tako ćete se u svemu obogatiti za svakovrsnu darežljivost koja se, našim posredovanjem, izvija u zahvalnicu Bogu.
Za ku wadata ta kowace hanya domin ku zama masu bayarwa, wannan kuwa zai sa a yi wa Allah godiya ta wurin mu.
12 Jer ovo bogoslužno posluživanje ne samo da podmiruje oskudicu svetih nego se i obilno prelijeva u mnoge zahvalnice Bogu.
Aiwatar da wannan hidima ba biyan bukatun tsarkaka kawai take yi ba. Tana kuma ribanbanya zuwa ayyuka masu yawa na bada godiya ga Allah.
13 Osvjedočeni ovim posluživanjem, slave Boga zbog vašega pokornog ispovijedanja evanđelja Kristova i zbog velikodušnog zajedništva prema njima i prema svima.
Domin an gwada ku an tabbatar da ku akan wannan hidima, za ku kuma daukaka Allah ta wurin biyayyar ku ga shaidar bisharar Almasihu. Za ku kuma daukaka Allah ta wurin yalwar bayarwarku gare su da kowa duka.
14 A moleći se za vas, čeznu za vama zbog preobilne milosti Božje na vama.
Suna marmarin ganin ku, suna kuma yi maku addu'a. Suna yin haka saboda alherin Allah mai girma da ke bisan ku.
15 Hvala Bogu na njegovu neizrecivom daru!
Godiya ga Allah domin kyautarsa wadda ta fi gaban bayyanawa.

< 2 Korinčanima 9 >