< 1 Korinčanima 15 >
1 Dozivljem vam, braćo, u pamet evanđelje koje vam navijestih, koje primiste, u kome stojite,
Yanzu ina tunashshe ku 'yan'uwa, game da bisharar nan da nake shelarwa, wadda kuka karba kuke kuma dogara da ita.
2 po kojem se spasavate, ako držite što sam vam navijestio; osim ako uzalud povjerovaste.
Da wannan bishara aka yi maku ceto, idan kuka rike wa'azi da na yi maku da karfi, sai in dama kun gaskanta a banza.
3 Doista, predadoh vam ponajprije što i primih: Krist umrije za grijehe naše po Pismima;
Domin na baku muhimmin sako kamar na farko da na karba: cewa Almasihu ya mutu domin zunubanmu, bisa ga nassosi,
4 bi pokopan i uskrišen treći dan po Pismima;
cewa kuma an bizne shi, ya kuwa tashi daga matattu a rana ta uku bisa ga nassosi.
5 ukaza se Kefi, zatim dvanaestorici.
Cewa kuma ya bayyana ga Kefas, sa'an nan ga sha biyun.
6 Potom se ukaza braći, kojih bijaše više od pet stotina zajedno; većina ih još i sada živi, a neki usnuše.
Daga nan ya bayyana ga 'yan'uwa sama da dari biyar a lokaci guda. Wadanda mafi yawan su na da rai har yau, amma wasun su sun yi barci.
7 Zatim se ukaza Jakovu, onda svim apostolima.
Daga nan ya bayyana ga Yakubu, da kuma ga manzannin duka.
8 Najposlije, kao nedonoščetu, ukaza se i meni.
A karshe, sai ya bayyana a gare ni, kamar dan da aka haifa bakwaini.
9 Da, ja sam najmanji među apostolima i nisam dostojan zvati se apostolom jer sam progonio Crkvu Božju.
Gama ni ne mafi kankanta a cikin manzanni. Ban cancanci a kira ni manzo ba, domin na tsanantawa ikklisiyar Allah.
10 Ali milošću Božjom jesam što jesam i njegova milost prema meni ne bijaše zaludna; štoviše, trudio sam se više nego svi oni - ali ne ja, nego milost Božja sa mnom.
Amma saboda alherin Ubangiji ina matsayin da nake a yau, kuma alherin sa da ke ciki na ba a banza yake ba. A maimako, nayi aiki tukuru fiye da su duka. Amma duk da haka ba ni bane, amma alherin Allah da ke tare da ni.
11 Ili dakle ja ili oni: tako propovijedamo, tako vjerujete.
Saboda haka ko nine ko Su, haka mukayi wa'azin, haka kuma kuka gaskata.
12 No ako se propovijeda da je Krist od mrtvih uskrsnuo, kako neki među vama govore da nema uskrsnuća mrtvih?
To idan anyi shela a matsayin cewa Yesu ya tashi daga matattu, tayaya wadansunku su ke cewa babu tashin matattu?
13 Ako nema uskrsnuća mrtvih, ni Krist nije uskrsnuo.
Amma idan babu tashin matattu, Almasihu ma ai ba a tashe shi ba kenan.
14 Ako pak Krist nije uskrsnuo, uzalud je doista propovijedanje naše, uzalud i vjera vaša.
idan kuwa ba a tashi Almasihu ba, wa'azin mu ya zama banza kenan, haka kuma bangaskiyar ku ta zama banza.
15 Zatekli bismo se i kao lažni svjedoci Božji što posvjedočismo protiv Boga: da je uskrisio Krista, kojega nije uskrisio, ako doista mrtvi ne uskršavaju.
Mun kuma zama shaidun karya game Allah kenan, muna shaida akan Allah cewa ya tashi Almasihu daga matattu alhali ko bai tashe shi ba.
16 Jer ako mrtvi ne uskršavaju, ni Krist nije uskrsnuo.
Domin idan babu tashin matattu, kai, ko Almasihu ma ba a tashe shi ba kenan.
17 A ako Krist nije uskrsnuo, uzaludna je vjera vaša, još ste u grijesima.
Idan har ba a tashi Almasihu ba, bangaskiyar ku a banza take, har yanzu kuma, kuna cikin zunuban ku.
18 Onda i oni koji usnuše u Kristu, propadoše.
To wadanda suka mutu cikin Almasihu kuma sun hallaka kenan,
19 Ako se samo u ovom životu u Krista ufamo, najbjedniji smo od svih ljudi.
idan a wannan rayuwa ce kadai muke da bege cikin Almasihu, to cikin dukkan mutane munfi kowa zama abin tausayi.
20 Ali sada: Krist uskrsnu od mrtvih, prvina usnulih!
Amma yanzu, Almasihu ya tashi daga matattu, wanda ya sa shi ya zama nunar fari cikin tashi daga matattu.
21 Doista po čovjeku smrt, po Čovjeku i uskrsnuće od mrtvih!
Domin yadda mutuwa ta shigo duniya ta hanyar mutum guda, hakkan nan ma tashi daga matattu.
22 Jer kao što u Adamu svi umiru, tako će i u Kristu svi biti oživljeni.
Gama kamar yadda a cikin Adamu duka suka mutu, haka kuma a cikin Almasihu za a rayar da duka.
23 Ali svatko u svom redu: prvina Krist, a zatim koji su Kristovi, o njegovu Dolasku;
Amma kowanne da tsarinsa: Almasihu, nunan fari, sannan su wadanda ke na Almasihu za a rayar da su lokacin zuwansa.
24 potom - svršetak, kad preda kraljevstvo Bogu i Ocu, pošto obeskrijepi svako Vrhovništvo, svaku Vlast i Silu.
Sa'an nan karshen zai gabato, lokacin da Almasihu zai mika mulkin ga Allah Uba. sa'an nan ne zaya kawar da dukkan mulki, martaba da iko.
25 Doista, on treba da kraljuje dok ne podloži sve neprijatelje pod noge svoje.
Gama mulkinsa zai habaka har sai ya sa dukkan makiyansa a karkashin sawayen sa.
26 Kao posljednji neprijatelj bit će obeskrijepljena Smrt
Mutuwa kuwa, ita ce makiyi na karshe da za'a hallaka.
27 jer sve podloži nogama njegovim. A kad veli: Sve je podloženo, jasno - sve osim Onoga koji mu je sve podložio.
Domin “yasa dukkan komai a karkashin ikonsa,” Amma da aka ce” yasa dukkan komai a karkashin ikonsa,” a sarari yake cewa wannan baya hada da wanda yasa dukan komai a karkashin ikonsa ba.
28 I kad mu sve bude podloženo, tada će se i on sam, Sin, podložiti Onomu koji je njemu sve podložio da Bog bude sve u svemu.
Idan dukan abu na karkashin mulkinsa, to Dan da kansa zaya kasance a karkashin ikon shi wanda yasa komai a karkashin ikonsa. Wannan zaya kasance ne saboda Allah Uba ya zama dukkan komai cikin dukkan komai.
29 Što onda čine oni koji se krste za mrtve? Ako mrtvi uopće ne uskršavaju, što se krste za njih?
ko kuma me zai faru da wadanda ake yi wa baftisma domin matattu? Idan kuwa babu tashin matattu sam sam, ina amfanin yi masu baftisma domin su?
30 Što se onda i mi svaki čas izlažemo pogiblima?
Kuma me yasa muke cikin hadari kowace sa'a?
31 Dan za danom umirem, tako mi slave vaše, braćo, koju imam u Kristu Isusu, Gospodinu našem!
Ina mutuwa kullum. Wannan nake furtawa ta wurin fahariya, 'yan'uwa, wadda nake da ita cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.
32 Ako sam se po ljudsku borio sa zvijerima u Efezu, kakva mi korist? Ako mrtvi ne uskršavaju, jedimo i pijmo jer sutra nam je umrijeti.
Menene ribata, a idanun mutane, idan nayi kokowa da bisashe a Afisa, idan babu tashin matattu? “bari mu ci mu sha, domin gobe zamu mutu.”
33 Ne varajte se: “Zli razgovori kvare dobre običaje.”
Kada fa a yaudare ku, domin “tarayya da mugaye takan bata halayen kirki.”
34 Otrijeznite se kako valja i ne griješite jer neki, na sramotu vam kažem, ne znaju za Boga.
“Ku natsu! kuyi zaman adalci! kada ku cigaba da zunubi. Domin wasunku basu da sanin Allah. Ina fadar wannan domin in baku kunya.
35 Ali reći će netko: Kako uskršavaju mrtvi? I s kakvim li će tijelom doći?
Amma wani zaya ce, “Yaya za'a yi tashin matattu? Wane irin jiki kuma zasu tashi da shi?
36 Bezumniče! Što siješ, ne oživljuje ako ne umre.
Ku jahilai ne sosai! Abinda ka shuka ba zaya fara girma ba sai ya mutu.
37 I što siješ, ne siješ tijelo buduće, već golo zrno, pšenice - recimo - ili čega drugoga.
Abinda ka shuka ba jikin da zaya kasance bane, amma kwayar irin ne kawai. Wanda zaya zama alkama ko wani abu daban.
38 A Bog mu daje tijelo kakvo hoće, i to svakom sjemenu svoje tijelo.
Amma Allah zaya bashi jiki yadda ya zaba, ga kowane kwayar iri da nashi jikin.
39 Nije svako tijelo isto tijelo; drugo je tijelo čovječje, drugo tijelo stoke, drugo tijelo ptičje, a drugo riblje.
Ba duka jiki ne yake iri daya ba. A maimako, akwai jiki irin na mutane, akwai kuma wani irin na dabbobi, kuma wani jikin irin na tsuntsaye, kuma da irin na kifi.
40 Ima tjelesa nebeskih i tjelesa zemaljskih, ali drugi je sjaj nebeskih, a drugi zemaljskih.
Akwai kuma jikina na samaniya da jikina na duniya. Amma daukakar jikin samaniya wata daban ce kuma daukakar jikin duniya daban ce.
41 Drugi je sjaj sunca, drugi sjaj mjeseca i drugi sjaj zvijezda; jer zvijezda se od zvijezde razlikuje u sjaju.
Akwai daukaka irin ta rana, da kuma wata daukakar irin ta wata, da kuma wata daukakar irin ta taurari. Domin wani tauraron ya bambanta da wani wajen daukaka.
42 Tako i uskrsnuće mrtvih: sije se u raspadljivosti, uskršava u neraspadljivosti;
Haka yake a tashin matattu. Abinda aka shuka mai lalacewa ne, wanda aka tayar marar lalacewa ne.
43 sije se u sramoti, uskršava u slavi; sije se u slabosti, uskršava u snazi;
An shuka shi cikin rashin daraja; an tayar da shi cikin daukaka. An shuka shi cikin rauni; an tayar da shi cikin iko.
44 sije se tijelo naravno, uskršava tijelo duhovno. Ako ima tijelo naravno, ima i duhovno.
An shuka shi jiki na zahiri; an tayar da shi jiki na ruhaniya. Idan akwai jiki na zahiri, to akwai jiki na ruhaniya.
45 Tako je i pisano: Prvi čovjek, Adam, postade živa duša, posljednji Adam - duh životvorni.
Haka kuma aka rubuta, “Adamu na farko ya zama rayayyen taliki.” Adamu na karshe ya zama Ruhu mai bayar da rai.
46 Ali ne bi najprije duhovno, nego naravno pa onda duhovno.
Amma na ruhaniyar ba shine ya fara zuwa ba amma na zahirin, daga nan na ruhaniyar.
47 Prvi je čovjek od zemlje, zemljan; drugi čovjek - s neba.
Mutumin farkon ai daga turbaya ya fito, wato na duniya. Amma shi na biyun daga sama yake.
48 Kakav je zemljani takvi su i zemljani, a kakav je nebeski takvi su i nebeski.
kamar yadda mutumin ya fito daga turbaya haka ma wadanda aka halitta da turbaya. kamar yadda mutumin yake daga sama haka ma wadanda ke na sama.
49 I kao što smo nosili sliku zemljanoga, nosit ćemo i sliku nebeskoga.
Kamar yadda muke dauke da jiki mai kamannin turbaya, haka ma zamu kasance da kamannin mutumin sama.
50 A ovo, braćo, tvrdim: tijelo i krv ne mogu baštiniti kraljevstva Božjega i raspadljivost ne baštini neraspadljivosti.
To wannan na fada, 'yan'uwa, cewa nama da jini ba za su gaji mulkin Allah ba. Haka kuma mai lalacewa ba za ya gaji marar lalacewa ba.
51 Evo otajstvo vam kazujem: svi doduše nećemo usnuti, ali svi ćemo se izmijeniti.
Duba! ina gaya maku asirtacciyar gaskiya: Ba dukanmu zamu mutu ba, amma dukanmu za a canza mu.
52 Odjednom, u tren oka, na posljednju trublju - jer zatrubit će - i mrtvi će uskrsnuti neraspadljivi i mi ćemo se izmijeniti.
Za a canza mu nan da nan, cikin keftawar ido, a kaho na karshe. Domin za a busa kaho, kuma za a tada matattu marasa lalacewa, kuma za a canza mu.
53 Jer ovo raspadljivo treba da se obuče u neraspadljivost i ovo smrtno da se obuče u besmrtnost.
Domin wannan jiki mai lalacewa dole ya sanya jiki marar lalacewa, kuma wannan jiki mai mutuwa dole ya sanya marar mutuwa.
54 A kad se ovo raspadljivo obuče u neraspadljivost i ovo smrtno obuče u besmrtnost, tada će se obistiniti riječ napisana: Pobjeda iskapi smrt.
Amma idan wannan jiki mai lalacewa ya sanya marar lalacewa, kuma wannan jiki mai mutuwa ya sanya marar mutuwa, sai abinda aka rubuta ya cika, “An hadiye mutuwa cikin nasara.”
55 Gdje je, smrti, pobjeda tvoja? Gdje je, smrti, žalac tvoj? (Hadēs )
“Mutuwa, ina nasararki? Mutuwa, ina dafinki?” (Hadēs )
56 Žalac je smrti grijeh, snaga je grijeha Zakon.
Gama dafin mutuwa zunubi ne, kuma ikon zunubi shari'a ce.
57 A hvala Bogu koji nam daje pobjedu po Gospodinu našem Isusu Kristu!
Amma godiya ga Allah, wanda ya bamu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu!
58 Tako, braćo moja ljubljena, budite postojani, nepokolebljivi, i obilujte svagda u djelu Gospodnjem znajući da trud vaš nije neplodan u Gospodinu.
Saboda haka, ya ku 'yan'uwana kaunatattu, ku dage kuma kada ku jijjigu. Ko yaushe ku habaka da aikin Ubangiji, domin kun san cewa aikinku cikin Ubangiji ba a banza yake ba.