< 雅歌 8 >

1 巴不得你像我的兄弟, 像吃我母親奶的兄弟; 我在外頭遇見你就與你親嘴, 誰也不輕看我。
Da a ce kai ɗan’uwa ne gare ni, wanda nonon mahaifiyata sun shayar! Da in na same ka a waje, na sumbace ka, babu wanda zai rena ni.
2 我必引導你, 領你進我母親的家; 我可以領受教訓, 也就使你喝石榴汁釀的香酒。
Da sai in bi da kai in kawo ka gidan mahaifiyata, ita da ta koyar da ni. Da na ba ka ruwan inabi gaurayayye da kayan yaji ka sha, zaƙin rumman nawa.
3 他的左手必在我頭下; 他的右手必將我抱住。
Hannunsa na hagu yana a ƙarƙashin kaina, hannunsa na dama kuma ya rungume ni.
4 耶路撒冷的眾女子啊, 我囑咐你們: 不要驚動、不要叫醒我所親愛的, 等他自己情願。
’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari. Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba sai haka ya zama lalle.
5 那靠着良人從曠野上來的是誰呢? 〔新娘〕 我在蘋果樹下叫醒你。 你母親在那裏為你劬勞; 生養你的在那裏為你劬勞。
Wace ce wannan da take haurawa daga hamada tana dogara a kan ƙaunataccenta? Ƙaunatacciya A ƙarƙashin itacen gawasa na farkar da ke, a wurin da aka haife ki, wurin da mahaifiyarki ta haife ki.
6 求你將我放在你心上如印記, 帶在你臂上如戳記。 因為愛情如死之堅強, 嫉恨如陰間之殘忍; 所發的電光是火焰的電光, 是耶和華的烈焰。 (Sheol h7585)
Ka sa ni kamar hatimi a zuciyarka, kamar hatimi a hannunka; gama ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa, kishinta yana kamar muguntar kabari, yana ƙuna kamar wuta mai ci, kamar gagarumar wuta. (Sheol h7585)
7 愛情,眾水不能熄滅, 大水也不能淹沒。 若有人拿家中所有的財寶要換愛情, 就全被藐視。
Ruwa da yawa ba zai iya kashe ƙauna ba, koguna ba za su iya kwashe ta ba. In wani zai bayar da dukan dukiyar gidansa don ƙauna, za a yi masa dariya ne kawai.
8 我們有一小妹; 她的兩乳尚未長成, 人來提親的日子, 我們當為她怎樣辦理?
Muna da ƙanuwa, nonanta ba su riga sun yi girma ba. Me za mu yi da ƙanuwarmu a ranar da za a yi maganar sonta?
9 她若是牆, 我們要在其上建造銀塔; 她若是門, 我們要用香柏木板圍護她。
Da a ce ita katanga ce, da sai mu gina hasumiyar azurfa a kanta. Da a ce ita ƙofa ce, da sai mun yi mata ƙyauren itacen al’ul.
10 我是牆; 我兩乳像其上的樓。 那時,我在他眼中像得平安的人。
Ni katanga ce kuma nonaina sun yi kamar hasumiya. Ta haka na zama idanunsa kamar wanda yake kawo gamsuwa.
11 所羅門在巴力‧哈們有一葡萄園; 他將這葡萄園交給看守的人, 為其中的果子必交一千舍客勒銀子。
Solomon ya kasance da gonar inabi a Ba’al-Hamon; ya ba da hayar gonar inabi ga’yan haya. Kowanne zai biya shekel dubu na azurfa don’ya’yan inabin.
12 我自己的葡萄園在我面前。 所羅門哪,一千舍客勒歸你, 二百舍客勒歸看守果子的人。
Amma gonar inabina nawa ne da zan bayar; shekel dubu naka ne, ya Solomon, kuma ɗari biyu na waɗanda suke lura da’ya’yan itatuwansa ne.
13 你這住在園中的, 同伴都要聽你的聲音, 求你使我也得聽見。
Ke da kike zaune a cikin lambu da ƙawaye suna lura da ke, bari in ji muryarki!
14 我的良人哪,求你快來! 如羚羊或小鹿在香草山上。
Ka zo, ƙaunataccena, ka zama kamar barewa ko kuwa kamar’yar batsiya a kan dutsen da kayan yaji suke a shimfiɗe.

< 雅歌 8 >