< 路得記 3 >

1 路得的婆婆拿俄米對她說:「女兒啊,我不當為你找個安身之處,使你享福嗎?
Wata rana Na’omi surukar Rut ta ce mata, “’Yata, bai kamata in nema miki gida, inda za a tanada miki da kyau?
2 你與波阿斯的使女常在一處,波阿斯不是我們的親族嗎?他今夜在場上簸大麥;
Bowaz wanda kike aiki da bayinsa’yan mata ba danginmu ne na kusa ba? Da daren yau zai sussuka sha’ir nasa a masussuka.
3 你要沐浴抹膏,換上衣服,下到場上,卻不要使那人認出你來。你等他吃喝完了,
Ki yi wanka ki fesa turare, ki kuma sa tufafinki mafi kyau. Sa’an nan ki gangara zuwa masussuka, amma kada ki bari yă san cewa kina a can sai ya gama ci da sha.
4 到他睡的時候,你看準他睡的地方,就進去掀開他腳上的被,躺臥在那裏,他必告訴你所當做的事。」
Sa’ad da ya kwanta, ki lura da inda yake kwance. Sa’an nan ki tafi ki buɗe ƙafafunsa ki kwanta. Zai faɗa miki abin da za ki yi.”
5 路得說:「凡你所吩咐的,我必遵行。」
Rut ta amsa ta ce “Zan yi abin da kika faɗa.”
6 路得就下到場上,照她婆婆所吩咐她的而行。
Saboda haka ta gangara zuwa masussuka ta kuma yi dukan abin da surukarta ta ce ta yi.
7 波阿斯吃喝完了,心裏歡暢,就去睡在麥堆旁邊。路得便悄悄地來掀開他腳上的被,躺臥在那裏。
Sa’ad da Bowaz ya gama ci da sha yana kuma cikin farin ciki, sai ya tafi ya kwanta a ƙarshen tarin hatsi. Rut kuwa ta sulalle ta je ta buɗe ƙafafunsa ta kwanta.
8 到了夜半,那人忽然驚醒,翻過身來,不料有女子躺在他的腳下。
Da tsakar dare sai wani abu ya firgitar da mutumin, ya kuwa juya sai ya tarar da mace kwance a ƙafafunsa.
9 他就說:「你是誰?」回答說:「我是你的婢女路得。求你用你的衣襟遮蓋我,因為你是我一個至近的親屬。」
Sai ya yi tambaya ya ce, “Ke wace ce?” Ta amsa ta ce, “Ni ce baranyarka Rut, ka rufe ni ta mayafinka da yake kai dangi, mai fansa ne na kusa.”
10 波阿斯說:「女兒啊,願你蒙耶和華賜福。你末後的恩比先前更大;因為少年人無論貧富,你都沒有跟從。
Sai ya amsa ya ce, “Ubangiji yă albarkace ki’yata. Wannan alheri ya fi wannan da kika nuna da farko. Ba ki gudu kin bi saurayi, mai arziki ko matalauci ba.
11 女兒啊,現在不要懼怕,凡你所說的,我必照着行;我本城的人都知道你是個賢德的女子。
Yanzu kuwa’yata kada ki ji tsoro. Zan yi miki dukan abin da kika roƙa. Dukan’yan’uwana na gari sun san cewa ke mace ce mai halin kirki.
12 我實在是你一個至近的親屬,只是還有一個人比我更近。
Ko da yake gaskiya ne ni dangi ne na kusa, amma akwai dangi mai fansa mafi kusa fiye da ni.
13 你今夜在這裏住宿,明早他若肯為你盡親屬的本分,就由他吧!倘若不肯,我指着永生的耶和華起誓,我必為你盡了本分,你只管躺到天亮。」
Ki kwana a nan, da safe kuwa in yana so yă fansa, to, da kyau, sai yă fansa. Amma in ba ya niyya, tabbatacce, na rantse da Ubangiji mai rai zan yi. Ki kwanta a nan sai da safe.”
14 路得便在他腳下躺到天快亮,人彼此不能辨認的時候就起來了。波阿斯說:「不可使人知道有女子到場上來」;
Saboda haka ta kwanta a ƙafafunsa sai da safe, amma ta tashi kafin a gane wani, sai ya ce, “Kada ki bar wani yă san cewa mace ta zo masussuka.”
15 又對路得說:「打開你所披的外衣。」她打開了,波阿斯就撮了六簸箕大麥,幫她扛在肩上,她便進城去了。
Ya kuma ce, “Ki kawo gyalenki da kika yafa ki shimfiɗa shi a nan.” Sa’ad da ta yi haka, sai ya zuba mudu shida na sha’ir ya sa mata a kai. Sa’an nan ya koma gari.
16 路得回到婆婆那裏,婆婆說:「女兒啊,怎麼樣了?」路得就將那人向她所行的述說了一遍,
Sa’ad da Rut ta koma wurin surukarta Na’omi ta tambaye ta “Yaya aka yi’yata?” Sai ta faɗa mata dukan abin da Bowaz ya yi mata
17 又說:「那人給了我六簸箕大麥,對我說:『你不可空手回去見你的婆婆。』」
ta kuma ƙara da cewa, “Ya ba ni waɗannan mudu shida na sha’ir, yana cewa, ‘Kada ki koma wurin surukarki hannu wofi.’”
18 婆婆說:「女兒啊,你只管安坐等候,看這事怎樣成就,因為那人今日不辦成這事必不休息。」
Sai Na’omi ta ce, “Ki jira,’yata, sai kin ga abin da zai faru. Gama mutumin ba zai huta ba sai an warware batun a yau.”

< 路得記 3 >