< 詩篇 3 >

1 大衛逃避他兒子押沙龍的時候作的詩。 耶和華啊,我的敵人何其加增; 有許多人起來攻擊我。
Zabura ta Dawuda. Sa’ad da ya gudu daga ɗansa Absalom. Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni!
2 有許多人議論我說: 他得不着上帝的幫助。 (細拉)
Da yawa suna magana a kaina suna cewa, “Allah ba zai cece shi ba.” (Sela)
3 但你-耶和華是我四圍的盾牌, 是我的榮耀,又是叫我抬起頭來的。
Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.
4 我用我的聲音求告耶和華, 他就從他的聖山上應允我。 (細拉)
Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. (Sela)
5 我躺下睡覺,我醒着, 耶和華都保佑我。
Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.
6 雖有成萬的百姓來周圍攻擊我, 我也不怕。
Ba zan ji tsoro ko dubu goma suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.
7 耶和華啊,求你起來! 我的上帝啊,求你救我! 因為你打了我一切仇敵的腮骨, 敲碎了惡人的牙齒。
Ka tashi Ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi; ka kakkarya haƙoran mugaye.
8 救恩屬乎耶和華; 願你賜福給你的百姓。 (細拉)
Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. (Sela)

< 詩篇 3 >