< 詩篇 140 >
1 大衛的詩,交與伶長。 耶和華啊,求你拯救我脫離凶惡的人, 保護我脫離強暴的人!
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ka cece ni, ya Ubangiji, daga mugaye; ka tsare ni daga mutane masu rikici,
masu shirya maƙarƙashiya a zukatansu suna kuma kawo yaƙi kullum.
3 他們使舌頭尖利如蛇, 嘴裏有虺蛇的毒氣。 (細拉)
Suna sa harsunansu su yi kaifi kamar na maciji; dafin gamsheƙa yana a leɓunansu. (Sela)
4 耶和華啊,求你拯救我脫離惡人的手, 保護我脫離強暴的人! 他們圖謀推我跌倒。
Ka kiyaye ni, ya Ubangiji, daga hannuwan mugaye; ka tsare ni daga mutane masu rikici waɗanda suke shirin kwashe ni a ƙafafu.
5 驕傲人為我暗設網羅和繩索; 他們在路旁鋪下網,設下圈套。 (細拉)
Masu girman kai sun sa mini tarko; sun shimfiɗa igiyoyin ragarsu sun kuma shirya mini tarko a hanyata. (Sela)
6 我曾對耶和華說:你是我的上帝。 耶和華啊,求你留心聽我懇求的聲音!
Ya Ubangiji, na ce maka, “Kai ne Allahna.” Ka ji kukata ta neman jinƙai, ya Ubangiji.
7 主-耶和華、我救恩的力量啊, 在爭戰的日子,你遮蔽了我的頭。
Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mai fansana mai ƙarfi, wanda yake garkuwoyin kaina a ranar yaƙi.
8 耶和華啊,求你不要遂惡人的心願; 不要成就他們的計謀,恐怕他們自高。 (細拉)
Kada ka biya wa mugaye bukatunsu, ya Ubangiji; kada ka bar shirinsu su yi nasara, in ba haka ba za su yi fariya. (Sela)
9 至於那些昂首圍困我的人, 願他們嘴唇的奸惡陷害自己!
Bari kawunan waɗanda suka kewaye ni su rufu da masifun da leɓunansu suka jawo.
10 願火炭落在他們身上! 願他們被丟在火中, 拋在深坑裏,不能再起來。
Bari garwashin wuta yă zubo a kansu; bari a jefar da su cikin wuta, cikin rami mai zurfi, kada su sāke tashi.
11 說惡言的人在地上必堅立不住; 禍患必獵取強暴的人,將他打倒。
Kada masu ɓata suna su taɓa kahu a ƙasar; bari masifa ta farauci mutane masu rikici.
12 我知道耶和華必為困苦人伸冤, 必為窮乏人辨屈。
Na san cewa Ubangiji ya shirya wa matalauta adalci yana kuma yi wa mabukata adalci.
Tabbatacce masu adalci za su yabi sunanka masu aikata gaskiya kuma za su zauna a gabanka.