< 詩篇 14 >
1 大衛的詩,交與伶長。 愚頑人心裏說:沒有上帝。 他們都是邪惡,行了可憎惡的事; 沒有一個人行善。
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Wawaye sukan ce a ransu, “Ba Allah.” Sun lalace, ayyukansu kuwa mugaye ne; babu wani da yake yi abu mai kyau.
2 耶和華從天上垂看世人, 要看有明白的沒有, 有尋求上帝的沒有。
Ubangiji ya duba daga sama a kan’yan adam don yă ga ko akwai wani da ya gane, wani wanda yake neman Allah.
3 他們都偏離正路, 一同變為污穢; 並沒有行善的, 連一個也沒有。
Duka sun kauce, duka gaba ɗaya sun zama lalatattu; babu ɗaya wanda yake yin abu mai kyau, ba ko ɗaya.
4 作孽的都沒有知識嗎? 他們吞吃我的百姓,如同吃飯一樣, 並不求告耶和華。
Masu aikata mugunta za su taɓa koyo. Suna cin mutane yadda mutane ke cin gurasa kuma waɗanda ba sa kira bisa Ubangiji?
5 他們在那裏大大地害怕, 因為上帝在義人的族類中。
Ga su, tsoro ya sha kansu, gama Allah yana cikin ƙungiyar adalai.
6 你們叫困苦人的謀算變為羞辱; 然而耶和華是他的避難所。
Ku masu mugunta kuna sa ƙoƙarin matalauta yă zama banza, amma Ubangiji ne mafakansu.
7 但願以色列的救恩從錫安而出。 耶和華救回他被擄的子民那時, 雅各要快樂,以色列要歡喜。
Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana! Sa’ad da Ubangiji zai maido da sa’ar mutanensa, bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna!