< 尼希米記 12 >

1 同着撒拉鐵的兒子所羅巴伯和耶書亞回來的祭司與利未人記在下面:祭司是西萊雅、耶利米、以斯拉、
Waɗannan su ne firistoci da Lawiyawa waɗanda suka komo tare da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da kuma Yeshuwa. Serahiya, Irmiya, Ezra,
2 亞瑪利雅、瑪鹿、哈突、
Amariya, Malluk, Hattush
3 示迦尼、利宏、米利末、
Shekaniya, Rehum, Meremot,
4 易多、近頓、亞比雅、
Iddo, Ginneton, Abiya,
5 米雅民、瑪底雅、璧迦、
Miyamin, Mowadiya, Bilga,
6 示瑪雅、約雅立、耶大雅、
Shemahiya, Yohiyarib, Yedahiya,
7 撒路、亞木、希勒家、耶大雅。這些人在耶書亞的時候作祭司和他們弟兄的首領。
Sallu, Amok, Hilkiya da Yedahiya. Waɗannan su ne shugabannin firistoci da’yan’uwansu a kwanakin Yeshuwa.
8 利未人是耶書亞、賓內、甲篾、示利比、猶大、瑪他尼。這瑪他尼和他的弟兄管理稱謝的事。
Lawiyawan su ne Yeshuwa, Binnuyi, Kadmiyel, Sherebiya, Yahuda, da kuma Mattaniya, wanda tare da’yan’uwansa yake lura da waƙoƙin godiya.
9 他們的弟兄八布迦和烏尼照自己的班次與他們相對。
Bakbukiya da Unni,’yan’uwansu sun tsaya ɗaura da su a hidimomi.
10 耶書亞生約雅金;約雅金生以利亞實;以利亞實生耶何耶大;
Yeshuwa ne mahaifin Yohiyakim, Yohiyakim shi ne mahaifin Eliyashib, Eliyashib shi ne mahaifin Yohiyada,
11 耶何耶大生約拿單;約拿單生押杜亞。
Yohiyada shi ne mahaifin Yonatan, Yonatan kuma mahaifin Yadduwa.
12 在約雅金的時候,祭司作族長的西萊雅族有米拉雅;耶利米族有哈拿尼雅;
A kwanakin Yohiyakim, waɗannan su ne shugabannin iyalan firistoci, na iyalin Serahiya, Merahiya; na iyalin Irmiya, Hananiya;
13 以斯拉族有米書蘭;亞瑪利雅族有約哈難;
na iyalin Ezra, Meshullam; na iyalin Amariya, Yehohanan;
14 米利古族有約拿單;示巴尼族有約瑟;
na iyalin Malluk, Yonatan; na iyalin Shebaniya, Yusuf;
15 哈琳族有押拿;米拉約族有希勒愷;
na iyalin Harim, Adna; na iyalin Merahiyot, Helkai;
16 易多族有撒迦利亞;近頓族有米書蘭;
na iyalin Iddo, Zakariya; na iyalin Ginneton, Meshullam;
17 亞比雅族有細基利;米拿民族某;摩亞底族有毗勒太;
na iyalin Abiya, Zikri; na iyalin Miniyamin da na Mowadiya, Filtai;
18 璧迦族有沙母亞;示瑪雅族有約拿單;
na iyalin Bilga, Shammuwa; na iyalin Shemahiya, Yehonatan;
19 約雅立族有瑪特乃;耶大雅族有烏西;
na iyalin Yohiyarib, Mattenai; na iyalin Yedahiya, Uzzi;
20 撒來族有加萊;亞木族有希伯;
na iyalin Sallu, Kallai; na iyalin Amok, Eber;
21 希勒家族有哈沙比雅;耶大雅族有拿坦業。
na iyalin Hilkiya, Hashabiya; na iyalin Yedahiya, Netanel.
22 至於利未人,當以利亞實、耶何耶大、約哈難、押杜亞的時候,他們的族長記在冊上。波斯王大流士在位的時候,作族長的祭司也記在冊上。
Shugabannin iyalin Lawiyawa a kwanakin Eliyashib, Yohiyada, Yohanan da Yadduwa, da kuma na firistoci, an rubuta su a zamanin mulkin Dariyus mutumin Farisa.
23 利未人作族長的記在歷史上,直到以利亞實的兒子約哈難的時候。
Shugabannin iyali cikin zuriyar Lawi har zuwa lokacin Yohanan ɗan Eliyashib, an rubuta su a cikin littafin tarihi.
24 利未人的族長是哈沙比雅、示利比、甲篾的兒子耶書亞,與他們弟兄的班次相對,照着神人大衛的命令一班一班地讚美稱謝。
Shugabannin Lawiyawa kuwa su ne Hashabiya, Sherebiya, Yeshuwa ɗan Kadmiyel, da’yan’uwansu, waɗanda suka tsaya ɗaura da su don su yi yabo da kuma godiya, sashe ɗaya kan ba da amsa ga ɗaya sashen, kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta.
25 瑪他尼、八布迦、俄巴底亞、米書蘭、達們、亞谷是守門的,就是在庫房那裏守門。
Mattaniya, Bakbukiya, Obadiya, Meshullam, Talmon da Akkub su ne matsaran ƙofofi waɗanda suka yi tsaron ɗaukan ajiya a ƙofofi.
26 這都是在約撒達的孫子、耶書亞的兒子約雅金和省長尼希米,並祭司文士以斯拉的時候,有職任的。
Sun yi hidima a kwanakin Yohiyakim ɗan Yeshuwa, ɗan Yozadak, kuma a kwanakin Nehemiya gwamna da kuma na Ezra firist da kuma marubuci.
27 耶路撒冷城牆告成的時候,眾民就把各處的利未人招到耶路撒冷,要稱謝、歌唱、敲鈸、鼓瑟、彈琴,歡歡喜喜地行告成之禮。
A keɓewar katangar Urushalima, an nemi Lawiyawa daga inda suke zama aka kawo su Urushalima don su yi bikin miƙawa da farin ciki da waƙoƙin godiya da kuma kiɗin kuge, garaya da molo.
28 歌唱的人從耶路撒冷的周圍和尼陀法的村莊與伯‧吉甲,又從迦巴和押瑪弗的田地聚集,因為歌唱的人在耶路撒冷四圍為自己立了村莊。
Aka kuma tattara mawaƙa su ma daga yankin kewayen Urushalima, daga ƙauyukan Netofawa,
daga Bet-Gilgal, da kuma daga wuraren Geba da Azmawet, gama mawaƙan sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Urushalima.
30 祭司和利未人就潔淨自己,也潔淨百姓和城門,並城牆。
Sa’ad da firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu da tsarki, sai suka tsarkake mutane, ƙofofi da kuma katanga.
31 我帶猶大的首領上城,使稱謝的人分為兩大隊,排列而行:第一隊在城上往右邊向糞廠門行走,
Sai na sa shugabannin Yahuda suka haura zuwa bisan katangar. Na kuma sa manyan ƙungiyoyi biyu na mawaƙa su miƙa godiya. Ɗaya ya haura zuwa bisan katangar zuwa dama, wajen Ƙofar Juji.
32 在他們後頭的有何沙雅與猶大首領的一半,
Hoshahiya da rabin shugabannin Yahuda kuwa suka bi su,
33 又有亞撒利雅、以斯拉、米書蘭、
tare da Azariya, Ezra, Meshullam,
34 猶大、便雅憫、示瑪雅、耶利米。
Yahuda, Benyamin, Shemahiya, Irmiya,
35 還有些吹號之祭司的子孫,約拿單的兒子撒迦利亞。約拿單是示瑪雅的兒子;示瑪雅是瑪他尼的兒子;瑪他尼是米該亞的兒子;米該亞是撒刻的兒子;撒刻是亞薩的兒子;
da waɗansu firistoci kuma da ƙahoni, da kuma Zakariya ɗan Yonatan, ɗan Shemahiya, ɗan Mattaniya, ɗan Mikahiya, ɗan Zakkur, ɗan Asaf,
36 又有撒迦利亞的弟兄示瑪雅、亞撒利、米拉萊、基拉萊、瑪艾、拿坦業、猶大、哈拿尼,都拿着神人大衛的樂器,文士以斯拉引領他們。
da’yan’uwansa, Shemahiya, Azarel, Milalai, Gilalai, Ma’ai, Netanel, Yahuda da Hanani, tare da kayan kiɗi da Dawuda mutumin Allah ya umarta. Ezra malamin Doka ya jagoranci jerin gwanon.
37 他們經過泉門往前,從大衛城的臺階隨地勢而上,在大衛宮殿以上,直行到朝東的水門。
A Ƙofar Maɓuɓɓuga suka ci gaba kai tsaye suka haura matakalan Birnin Dawuda a kan hawa zuwa katangar suka wuce a bisa gidan Dawuda zuwa Ƙofar Ruwa wajen gabas.
38 第二隊稱謝的人要與那一隊相迎而行。我和民的一半跟隨他們,在城牆上過了爐樓,直到寬牆;
Ƙungiyar mawaƙa ta biyu suka yi jerin gwano a ɗaya gefen. Na bi su a bisan katangar, tare da rabin mutanen, muka wuce Hasumiya Tanderu zuwa Katanga Mai Faɗi,
39 又過了以法蓮門、古門、魚門、哈楠業樓、哈米亞樓,直到羊門,就在護衛門站住。
bisa Ƙofar Efraim, Ƙofar Yeshana, Ƙofar Kifi, Hasumiyar Hananel da kuma Hasumiya ɗari, har zuwa Ƙofar Tumaki. A Ƙofar Matsara suka tsaya.
40 於是,這兩隊稱謝的人連我和官長的一半,站在上帝的殿裏。
Ƙungiyoyin mawaƙa biyu da suka yi godiya suka ɗauki wurarensu a gidan Allah, haka ma ni, tare da rabin shugabanni,
41 還有祭司以利亞金、瑪西雅、米拿民、米該亞、以利約乃、撒迦利亞、哈楠尼亞吹號;
da kuma firistoci, Eliyakim, Ma’asehiya, Miniyamin, Mikahiya, Eliyohenai, Zakariya da Hananiya tare da ƙahoninsu,
42 又有瑪西雅、示瑪雅、以利亞撒、烏西、約哈難、瑪基雅、以攔,和以謝奏樂。歌唱的就大聲歌唱,伊斯拉希雅管理他們。
haka ma Ma’asehiya, Shemahiya, Eleyazar, Uzzi, Yehohanan, Malkiya, Elam da Ezer. Mawaƙan suka rera waƙoƙi a ƙarƙashin kulawar Yezrahiya.
43 那日,眾人獻大祭而歡樂;因為上帝使他們大大歡樂,連婦女帶孩童也都歡樂,甚至耶路撒冷中的歡聲聽到遠處。
A rana ta uku kuma suka miƙa manyan hadayu, suna farin ciki domin Allah ya ba su farin ciki mai girma. Mata da yara suka yi farin ciki su ma. An ji ƙarar farin ciki da ake yi a Urushalima daga nesa.
44 當日,派人管理庫房,將舉祭、初熟之物和所取的十分之一,就是按各城田地,照律法所定歸給祭司和利未人的分,都收在裏頭。猶大人因祭司和利未人供職,就歡樂了。
A lokacin an naɗa mutane su lura da ɗakunan ajiya don sadakoki, nunan fari da kuma zakka. Daga gonakin garuruwan da suke kewaye za su kawo sassan da Dokar ta umarta zuwa ɗakunan ajiya domin firistoci da Lawiyawa, gama Yahuda ya ji daɗin aikin firistoci da Lawiyawa.
45 祭司利未人遵守上帝所吩咐的,並守潔淨的禮。歌唱的、守門的,照着大衛和他兒子所羅門的命令也如此行。
Sun yi hidimar Allahnsu da kuma hidimar tsarkakewa, kamar yadda mawaƙa da matsaran ƙofofi suka yi, bisa ga umarnin Dawuda da ɗansa Solomon.
46 古時,在大衛和亞薩的日子,有歌唱的伶長,並有讚美稱謝上帝的詩歌。
Gama tun dā, a kwanakin Dawuda da Asaf, akwai masu bi da mawaƙa da kuma na waƙoƙin yabo da na godiya ga Allah.
47 當所羅巴伯和尼希米的時候,以色列眾人將歌唱的、守門的,每日所當得的分供給他們,又給利未人當得的分;利未人又給亞倫的子孫當得的分。
Saboda haka a kwanakin Zerubbabel da Nehemiya, dukan Isra’ila suka ba da sashe na kowace rana domin mawaƙa da matsaran ƙofofi. Suka kuma keɓe sashe don sauran Lawiyawa, Lawiyawan kuma suka keɓe sashe don zuriyar Haruna.

< 尼希米記 12 >