< 馬可福音 9 >
1 耶穌又對他們說:「我實在告訴你們,站在這裏的,有人在沒嘗死味以前,必要看見上帝的國大有能力臨到。」
Sai ya ce masu, “Hakika, ina gaya maku, akwai wasun ku anan da ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.”
2 過了六天,耶穌帶着彼得、雅各、約翰暗暗地上了高山,就在他們面前變了形像,
Bayan kwana shida Yesu ya dauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kadai. Sai kamaninsa ya sake a gabansu.
3 衣服放光,極其潔白,地上漂布的,沒有一個能漂得那樣白。
Sai tufafinsa ya zama fari fat, yadda ba mai rinin da zai iya rininsa haka a duniya.
4 忽然,有以利亞同摩西向他們顯現,並且和耶穌說話。
Sai Iliya da Musa suka bayyana gare su, suna magana da Yesu.
5 彼得對耶穌說:「拉比,我們在這裏真好!可以搭三座棚,一座為你,一座為摩西,一座為以利亞。」
Sai Bitrus ya amsa ya ce, malam, bari mu da muke anan mu kafa bukka uku, daya ta ka, daya ta Musa, da ta Iliya,
Ya rasa abin da zai fada ne, don sun tsorota kwarai.)
7 有一朵雲彩來遮蓋他們;也有聲音從雲彩裏出來,說:「這是我的愛子,你們要聽他。」
Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga gajimaren, “ta ce Wannan shine kaunataccen Dana, Ku saurare shi.
8 門徒忽然周圍一看,不再見一人,只見耶穌同他們在那裏。
Nan take da suka duba, ba su ga kowa ba, sai Yesu shi kadai.
9 下山的時候,耶穌囑咐他們說:「人子還沒有從死裏復活,你們不要將所看見的告訴人。」
Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai ya kwabe su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan da Dan Mutum ya tashi daga mattatu.
10 門徒將這話存記在心,彼此議論「從死裏復活」是甚麼意思。
Sai suka bar zancen a tsakaninsu, amma suka tamabayi junansu “mene ne tashin matattu” ke nufi.
11 他們就問耶穌說:「文士為甚麼說以利亞必須先來?」
Suka tambaye shi yaya malaman attaura suka ce Iliya zai fara zuwa?”
12 耶穌說:「以利亞固然先來復興萬事;經上不是指着人子說,他要受許多的苦被人輕慢呢?
Ya ce masu, laile ne Iliya ya fara zuwa ya raya dukan abubuwan. Don me a ka rubuta cewa Dan Mutum, zai sha wuya iri iri a kuma ki shi?
13 我告訴你們,以利亞已經來了,他們也任意待他,正如經上所指着他的話。」
Amma ina gaya muku Iliya ya riga, ya zo, amma sun yi masa abin da suke so su yi kamar yadda littatafai suka yi magana a kansa.”
14 耶穌到了門徒那裏,看見有許多人圍着他們,又有文士和他們辯論。
Sa'adda suka dawo wurin sauran almajiran, suka ga taron jama'a masu yawa suna ta muhawara tare da manyan malaman attaura.
Da ganin sa, sai dukan taron yayi mamaki kwarai da gaske, suka dungumo wurinsa a guje, suna gaishe shi.
Ya tambayi almajiransa, “Wacce muhawara ce kuke yi da su?”
17 眾人中間有一個人回答說:「夫子,我帶了我的兒子到你這裏來,他被啞巴鬼附着。
Daya daga cikin taron ya amsa masa”malam, ga shi na kawo maka dana don yana da beben aljani.
18 無論在哪裏,鬼捉弄他,把他摔倒,他就口中流沫,咬牙切齒,身體枯乾。我請過你的門徒把鬼趕出去,他們卻是不能。」
Duk lokacin da ya tasar masa yakan buga shi har kasa, na kuma yi wa almajiranka magana su fitar sun kasa.
19 耶穌說:「噯!不信的世代啊,我在你們這裏要到幾時呢?我忍耐你們要到幾時呢?把他帶到我這裏來吧。」
Ya amsa masu ya ce ya ku mutanen zamaninnan marasa bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku ina jimrewa? ku dai kawo mini shi.
20 他們就帶了他來。他一見耶穌,鬼便叫他重重地抽瘋,倒在地上,翻來覆去,口中流沫。
Sai suka kawo masa yaron. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan ya buge yaron jikinsa na rawa. Sai yaron ya fadi yana ta birgima, bakinsa yana kumfa.
21 耶穌問他父親說:「他得這病有多少日子呢?」回答說:「從小的時候。
Yesu ya tambayi mahaifin yaron, Tun yaushe wannan abu ya same shi? Mahaifin yaron ya ce tun yana karami.
22 鬼屢次把他扔在火裏、水裏,要滅他。你若能做甚麼,求你憐憫我們,幫助我們。」
Ya kuwa sha jefa shi a ruwa da wuta, don ya halakar da shi. Idan zaka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimakemu.
23 耶穌對他說:「你若能信,在信的人,凡事都能。」
Yesu ya ce masa, “In zan iya? Ai dukan abu mai yiwuwa ne, ga duk wanda ya gaskata.
24 孩子的父親立時喊着說:「我信!但我信不足,求主幫助。」
Nan da nan mahaifin yaron ya daga murya ya ce, Na ba da gaskiya. A kore mini rashin bangaskiyata.
25 耶穌看見眾人都跑上來, 就斥責那污鬼,說:「你這聾啞的鬼,我吩咐你從他裏頭出來,再不要進去!」
Da Yesu ya ga taron na dungumowa a guje, sai ya tsawata wa bakin aljanin ya ce masa, “kai, beben aljani na umarce ka, ka fita daga wannan yaron kar ka sake shigar sa.
26 那鬼喊叫,使孩子大大地抽了一陣瘋,就出來了。孩子好像死了一般,以致眾人多半說:「他是死了。」
Sai wannan aljanin ya daga murya ya fita ya rabu da wannan yaron. Sai yaro ya zama kamar mattacce, sai sauran mutanen suka ce, “Ai, yaron ya mutu.
Yesu ya kama hannunsa, ya daga shi, sai yaron ya mike tsaye.
28 耶穌進了屋子,門徒就暗暗地問他說:「我們為甚麼不能趕出他去呢?」
Da Yesu ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi a kadaice, me ya sa muka kasa fitar da shi?”
29 耶穌說:「非用禱告,這一類的鬼總不能出來。」
Ya ce masu, “Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a.”
30 他們離開那地方,經過加利利;耶穌不願意人知道。
Sai suka ratsa cikin Galili, amma ba ya son kowa ya san inda suke.
31 於是教訓門徒,說:「人子將要被交在人手裏,他們要殺害他;被殺以後,過三天他要復活。」
Da yake koyar da almajiransa, ya ce masu lokaci na zuwa da za'a ba da Dan mutum a hannun mutane, za su kuwa kashe shi, sa'adda aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi.
Amma fa ba su fahimci maganar ba, suna kuma jin tsoron tambayarsa.
33 他們來到迦百農。耶穌在屋裏問門徒說:「你們在路上議論的是甚麼?」
Sai suka zo kafarnahum. A lokacin da ya ke cikin gida, ya tambayi Al'majiransa, Menene ku ke magana a kansa a hanya?
Amma suka yi shiru. don suna gardama da junansu akan hanya, a kan wane ne mafi girma.
35 耶穌坐下,叫十二個門徒來,說:「若有人願意作首先的,他必作眾人末後的,作眾人的用人。」
Sai ya zauna, ya kira al'majiransa goma sha biyu, yace masu duk wanda ya ke so ya zama na fari, dole ya kankantar da kansa, sa'annan ya bautawa sauran duka.
36 於是領過一個小孩子來,叫他站在門徒中間,又抱起他來,對他們說:
Sai ya dauko karamin yaro a hannunsa ya sa shi a tsakiyarsu. Ya rumgome shi a kafadarsa ya ce masu.
37 「凡為我名接待一個像這小孩子的,就是接待我;凡接待我的,不是接待我,乃是接待那差我來的。」
Dukan wanda ya karbi dan karamin yaron nan a cikin sunana ni ya karba, kuma dukan wanda ya karbi wani, ni ya karba, bai kuma karbeni ni kadai ba, duk da wanda ya aiko ni.”
38 約翰對耶穌說:「夫子,我們看見一個人奉你的名趕鬼,我們就禁止他,因為他不跟從我們。」
Sai Yahaya ya ce masa, Malam mun ga wani yana fitar da aljanu da sunanka mun yi kokari mu hana shi domin ba ya tare da mu.
39 耶穌說:「不要禁止他;因為沒有人奉我名行異能,反倒輕易毀謗我。
Sai Yesu ya ce masu ku kyale shi domin babu wanda zai yi irin wannan babban aikin, sa'annan ya fadi wasu maganganu mara sa kyau a kanmu.
Duk wanda ba ya gaba da mu, na mu ne.
41 凡因你們是屬基督,給你們一杯水喝的,我實在告訴你們,他不能不得賞賜。」
Duk wanda ya ba ku ruwa ku sha domin kuna na Almasihu, gaskiya nake fada maku ba za ya rasa ladansa ba.
42 「凡使這信我的一個小子跌倒的,倒不如把大磨石拴在這人的頸項上,扔在海裏。
Amma duk wanda ya sa kananan nan tuntube, ya fi kyau a rataya masa dutsen nika a jefa shi a cikin teku.
43 倘若你一隻手叫你跌倒,就把它砍下來; 你缺了肢體進入永生,強如有兩隻手落到地獄,入那不滅的火裏去。 (Geenna )
Idan har hannun ka zai sa ka yi tuntube, zai fi kyau ka yanke shi. Domin zai fi kyau ka shiga aljanna da hannu daya da ka shiga jahannama da hannu biyu. (Geenna )
(Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa).
45 倘若你一隻腳叫你跌倒,就把它 砍下來; 你瘸腿進入永生,強如有兩隻腳被丟在地獄裏。 (Geenna )
Idan kafarka za ta sa ka yi tuntube, ka yanke ta ka yar. Zai fi kyau ka shiga aljanna da kafa daya da ka shiga jahannama da kafa biyu. (Geenna )
(Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa).
47 倘若你一隻眼叫你跌倒,就去掉它;你只有一隻眼進入上帝的國,強如有兩隻眼被丟在地獄裏。 (Geenna )
Idan idonka zai sa ka yi tuntube, ka kwakule shi ka yar, domin gwamma ka shiga mulkin Allah da ido daya, da a jefa ka cikin wuta da idanu biyu. (Geenna )
Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa.
Domin da wuta za a tsarkake kowa.
50 鹽本是好的,若失了味,可用甚麼叫它再鹹呢?你們裏頭應當有鹽,彼此和睦。」
Gishiri yana da kyau, amma idan ya rasa zakinsa, ta ya ya za ka sa shi yayi zaki kuma? Ku kasance da zaki, kuma ku yi zaman lafiya da kowa.