< 耶利米書 5 >

1 你們當在耶路撒冷的街上跑來跑去, 在寬闊處尋找, 看看有一人行公義求誠實沒有? 若有,我就赦免這城。
“Ku yi ta kai da kawowa a titunan Urushalima, ku dudduba ko’ina ku kuma lura, ku bincika cikin dandalinta. Ko za ku sami mutum guda wanda yake aikata adalci wanda yake kuma son bin gaskiya, sai in gafarta wa wannan birni.
2 其中的人雖然指着永生的耶和華起誓, 所起的誓實在是假的。
Ko da yake suna cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye,’ duk da haka suna rantsuwar ƙarya.”
3 耶和華啊,你的眼目不是看顧誠實嗎? 你擊打他們,他們卻不傷慟; 你毀滅他們,他們仍不受懲治。 他們使臉剛硬過於磐石, 不肯回頭。
Ya Ubangiji, idanunka ba sa ganin gaskiya? Ka buge su, amma ba su ji zafi ba; ka ragargaza su, amma suka ƙi su gyara. Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse suka ƙi su tuba.
4 我說:這些人實在是貧窮的,是愚昧的, 因為不曉得耶和華的作為 和他們上帝的法則。
Na yi tunani, “Waɗannan ne kawai matalauta; su wawaye ne, gama ba su san hanyar Ubangiji ba, ko abubuwan da Allahnsu yake bukata ba.
5 我要去見尊大的人,對他們說話, 因為他們曉得耶和華的作為 和他們上帝的法則。 哪知,這些人齊心將軛折斷, 掙開繩索。
Saboda haka zan tafi wurin shugabanni in yi musu magana; tabbatacce sun san hanyar Ubangiji, da abubuwan da Allahnsu yake bukata.” Amma da nufi guda su ma suka karye karkiyar suka tsintsinke sarƙoƙin.
6 因此,林中的獅子必害死他們; 晚上的豺狼必滅絕他們; 豹子要在城外窺伺他們。 凡出城的必被撕碎; 因為他們的罪過極多, 背道的事也加增了。
Saboda haka zaki daga kurmi zai fāɗa musu, kyarkeci kuma daga hamada zai cinye su, damisa za tă yi musu ƙawanya kusa da garuruwansu yă yayyage duk wanda ya kuskura ya fita, gama tawayensu da girma yake jan bayansu kuma yana da yawa.
7 我怎能赦免你呢? 你的兒女離棄我, 又指着那不是神的起誓。 我使他們飽足, 他們就行姦淫, 成群地聚集在娼妓家裏。
“Me zai sa in gafarta muku?’Ya’yanku sun yashe ni sun yi rantsuwa da allolin da ba alloli ba ne. Na biya musu dukan bukatunsu, duk da haka suka yi zina suka tattaru a gidajen karuwai.
8 他們像餵飽的馬到處亂跑, 各向他鄰舍的妻發嘶聲。
An ciyar da su sosai, kamar ƙosassun ingarmu, masu jaraba, kowanne yana haniniya, yana neman matar maƙwabcinsa.
9 耶和華說:我豈不因這些事討罪呢? 豈不報復這樣的國民呢?
Ba zan hukunta su saboda wannan ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata in yi ramuwa a kan irin al’ummar nan ba?
10 你們要上她葡萄園的牆施行毀壞, 但不可毀壞淨盡, 只可除掉她的枝子, 因為不屬耶和華。
“Ku ratsa cikin gonakin inabinta ku cinye su, amma kada ku hallaka su gaba ɗaya. Ku kakkaɓe rassanta, gama waɗannan mutane ba na Ubangiji ba ne.
11 原來以色列家和猶大家大行詭詐攻擊我。 這是耶和華說的。
Gidan Isra’ila da gidan Yahuda sun zama marasa aminci gaba ɗaya gare ni” in ji Ubangiji.
12 他們不認耶和華,說: 這並不是他, 災禍必不臨到我們; 刀劍和饑荒,我們也看不見。
Sun yi ƙarya a kan Ubangiji; sun ce, “Ba zai yi kome ba! Ba wata masifar da za tă same mu; ba za mu taɓa ganin takobi ko yunwa ba.
13 先知的話必成為風; 道也不在他們裏面。 這災必臨到他們身上。
Annabawa holoƙo ne kawai maganar kuwa ba ta cikinsu; saboda haka bari abin da suke faɗi ya koma kansu.”
14 所以耶和華-萬軍之上帝如此說: 因為百姓說這話, 我必使我的話在你口中為火,使他們為柴; 這火便將他們燒滅。
Saboda haka ga abin Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa, “Domin mutanen sun yi waɗannan maganganu, zan mai da maganata a bakinku wuta waɗannan mutane kuwa su zama itacen da za tă ci.
15 耶和華說:以色列家啊, 我必使一國的民從遠方來攻擊你, 是強盛的國, 是從古而有的國。 他們的言語你不曉得, 他們的話你不明白。
Ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji, “Ina kawo al’umma daga nesa a kanku al’umma ce ta tun dā mai ƙarfin hali, mutane ne da ba ku san harshensu ba, waɗanda ba za ku fahimci abin da suke faɗa ba.
16 他們的箭袋是敞開的墳墓; 他們都是勇士。
Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabari ne; dukansu jarumawa ne.
17 他們必吃盡你的莊稼和你的糧食, 是你兒女該吃的; 必吃盡你的牛羊, 吃盡你的葡萄和無花果; 又必用刀毀壞你所倚靠的堅固城。
Za su cinye amfanin gonakinku da abincinku, za su cinye’ya’yanku maza da mata; za su cinye garkunan tumakinku da na awakinku, za su cinye’ya’yan inabinku da na ɓaurenku. Da takobi za su hallaka biranenku masu katanga.
18 耶和華說:「就是到那時,我也不將你們毀滅淨盡。
“Amma ko a cikin waɗancan kwanaki,” in ji Ubangiji, “ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba.
19 百姓若說:『耶和華-我們的上帝為甚麼向我們行這一切事呢?』你就對他們說:『你們怎樣離棄耶和華,在你們的地上事奉外邦神,也必照樣在不屬你們的地上事奉外邦人。』」
Sa’ad da kuma mutanen suka yi tambaya, ‘Me ya sa Ubangiji Allahnmu ya yi dukan wannan gare mu?’ Sai ka amsa musu, ‘Yadda kuka yashe ni kuka kuma bauta wa baƙin alloli a ƙasarku, haka yanzu za ku bauta wa baƙi a ƙasar da ba taku ba.’
20 當傳揚在雅各家, 報告在猶大說:
“Ka sanar da wannan ga gidan Yaƙub ka yi shelarsa a Yahuda.
21 愚昧無知的百姓啊, 你們有眼不看, 有耳不聽, 現在當聽這話。
Ku ji wannan, ku wawaye marasa azanci, waɗanda suke da idanu amma ba sa gani, waɗanda suke da kunnuwa amma ba sa ji.
22 耶和華說:你們怎麼不懼怕我呢? 我以永遠的定例, 用沙為海的界限, 水不得越過。 因此,你們在我面前還不戰兢嗎? 波浪雖然翻騰,卻不能逾越; 雖然匉訇,卻不能過去。
Bai kamata ku ji tsorona ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata ku yi rawar jiki a gabana ba? Na sa yashi ya zama iyakar teku, madawwamiyar iyakar da ba zai tsallake ba. Raƙuman ruwa za su iya yin hauka, amma ba za su iya haye ta ba; za su iya yin ruri, amma ba za su iya ƙetare ta ba.
23 但這百姓有背叛忤逆的心; 他們叛我而去,
Amma mutanen nan suna da tauraren zukata, kuma’yan tawaye ne; sun kauce suka kuma rabu da ni.
24 心內也不說: 我們應當敬畏耶和華-我們的上帝; 他按時賜雨,就是秋雨春雨, 又為我們定收割的節令,永存不廢。
Ba sa faɗa wa kansu, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu, wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari na kaka da na bazara, wanda kullum yake tabbatar mana da girbi.’
25 你們的罪孽使這些事轉離你們; 你們的罪惡使你們不能得福。
Laifofinku sun raba ku da waɗannan abubuwa; zunubanku sun hana ku samun alheri.
26 因為在我民中有惡人。 他們埋伏窺探,好像捕鳥的人; 他們設立圈套陷害人。
“A cikin mutanena an sami mugaye waɗanda suke kwanton ɓauna kamar masu sa tarko wa tsuntsaye kamar waɗanda suke kafa tarko don su kama mutane.
27 籠內怎樣滿了雀鳥, 他們的房中也照樣充滿詭詐; 所以他們得成為大,而且富足。
Kamar keji cike da tsuntsaye, gidajensu sun cika da ruɗu; sun yi arziki suka kuma zama masu iko
28 他們肥胖光潤, 作惡過甚,不為人伸冤! 就是不為孤兒伸冤, 不使他亨通, 也不為窮人辨屈。
suka kuma yi ƙiba, suka yi bul-bul. Mugayen ayyukansu ba su da iyaka; ba sa wa marayu shari’ar adalci, ba sa kāre’yancin matalauta.
29 耶和華說:我豈不因這些事討罪呢? 豈不報復這樣的國民呢?
Bai kamata in hukunta su saboda wannan ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata in yi ramuwa a kan irin al’umma kamar wannan ba?
30 國中有可驚駭、可憎惡的事:
“Abin banmamaki da bantsoro ya faru a ƙasar.
31 就是先知說假預言, 祭司藉他們把持權柄; 我的百姓也喜愛這些事, 到了結局你們怎樣行呢?
Annabawa suna annabcin ƙarya, firistoci suna mulki da ikon kansu, mutanena kuma suna son haka. Amma me za ku yi a ƙarshe?

< 耶利米書 5 >