< 耶利米書 40 >
1 耶利米鎖在耶路撒冷和猶大被擄到巴比倫的人中,護衛長尼布撒拉旦將他從拉瑪釋放以後,耶和華的話臨到耶利米。
Sai magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji bayan Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya sake shi a Rama. Ya sami Irmiya a daure da sarƙoƙi a cikin sauran kamammu daga Urushalima da kuma Yahuda waɗanda ake kaiwa zaman bauta a Babilon.
2 護衛長將耶利米叫來,對他說:「耶和華-你的上帝曾說要降這禍與此地。
Sa’ad da shugaban matsaran ya sami Irmiya sai ya ce masa, “Ubangiji Allahnka ya sa wannan masifa saboda wannan wuri.
3 耶和華使這禍臨到,照他所說的行了;因為你們得罪耶和華,沒有聽從他的話,所以這事臨到你們。
Yanzu kuma Ubangiji ya cika shi; ya yi kamar yadda ya faɗa. Dukan wannan ya faru domin kun yi zunubi ga Ubangiji ba ku kuwa yi masa biyayya ba.
4 現在我解開你手上的鍊子,你若看與我同往巴比倫去好,就可以去,我必厚待你;你若看與我同往巴比倫去不好,就不必去。看哪,全地在你面前,你以為哪裏美好,哪裏合宜,只管上那裏去吧!」
Amma yau ina’yantar da kai daga sarƙoƙin da suke a hannuwanka. Zo mu tafi Babilon, in kana so, zan kuwa lura da kai; amma in ba ka so, kada ka zo. Ga shi, dukan ƙasar tana a gabanka; ka tafi duk inda ka so.”
5 耶利米還沒有回去,護衛長說:「你可以回到沙番的孫子亞希甘的兒子基大利那裏去;現在巴比倫王立他作猶大城邑的省長。你可以在他那裏住在民中,不然,你看哪裏合宜就可以上那裏去。」於是護衛長送他糧食和禮物,釋放他去了。
Amma, kafin Irmiya yă juya yă tafi, Nebuzaradan ya ƙara da cewa, “Ka koma wurin Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, wanda sarkin Babilon ya naɗa a kan garuruwan Yahuda, ka zauna da shi a cikin mutane, ko kuwa ka tafi duk inda ka ga dama.” Sa’an nan shugaban ya ba shi abinci da kuma kyauta sai ya bar shi ya tafi.
6 耶利米就到米斯巴見亞希甘的兒子基大利,在他那裏住在境內剩下的民中。
Saboda haka Irmiya ya tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam, a Mizfa ya zauna tare da shi a cikin mutanen da aka bari a ƙasar.
7 在田野的一切軍長和屬他們的人聽見巴比倫王立了亞希甘的兒子基大利作境內的省長,並將沒有擄到巴比倫的男人、婦女、孩童,和境內極窮的人全交給他。
Sa’ad da dukan shugabannin hafsoshin tare da mutanen da suke a karkara suka ji cewa sarkin Babilon ya naɗa Gedaliya ɗan Ahikam gwamna a kan ƙasar ya kuma sa shi ya lura da maza, mata da’ya’yan da suke mafi talauci a ƙasar da waɗanda ba a kwashe zuwa zaman bauta a Babilon ba,
8 於是軍長尼探雅的兒子以實瑪利,加利亞的兩個兒子約哈難和約拿單,單戶篾的兒子西萊雅,並尼陀法人以斐的眾子,瑪迦人的兒子耶撒尼亞和屬他們的人,都到米斯巴見基大利。
sai suka zo wurin Gedaliya a Mizfa, Ishmayel ɗan Netaniya, Yohanan da Yonatan’ya’yan Kareya, da Serahiya ɗan Tanhumet maza,’ya’yan Efai maza, mutumin Netofa, da Yezaniya ɗan mutumin Ma’aka da mutanensu.
9 沙番的孫子亞希甘的兒子基大利向他們和屬他們的人起誓說:「不要怕服事迦勒底人,只管住在這地,服事巴比倫王,就可以得福。
Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, ya yi rantsuwa don yă tabbatar musu da mutanensu. Ya ce, “Kada ku ji tsoron bauta wa Babiloniyawa. Ku zauna a ƙasar ku bauta wa sarkin Babilon, zai kuma yi muku amfani.
10 至於我,我要住在米斯巴,伺候那到我們這裏來的迦勒底人;只是你們當積蓄酒、油,和夏天的果子,收在器皿裏,住在你們所佔的城邑中。」
Ni kaina zan zauna a Mizfa in zama wakilinku a gaban Babiloniyawa waɗanda za su zo wurinmu, amma ku girbe ruwan inabi,’ya’yan itatuwa na kaka, da mai, ku zuba su a tulunan ajiyarku, ku kuma zauna a garuruwan da kuka ci.”
11 在摩押地和亞捫人中,在以東地和各國的一切猶大人,聽見巴比倫王留下些猶大人,並立沙番的孫子亞希甘的兒子基大利管理他們。
Sa’ad da dukan Yahudawan da suke a Mowab, Ammon, Edom da sauran ƙasashe suka ji cewa sarkin Babilon ya bar raguwa a Yahuda ya kuma naɗa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan gwamna a kansu,
12 這一切猶大人就從所趕到的各處回來,到猶大地米斯巴的基大利那裏,又積蓄了許多的酒,並夏天的果子。
sai suka dawo ƙasar Yahuda, wurin Gedaliya a Mizfa, daga dukan ƙasashen da suke a warwatse. Suka girbe ruwan inabi a yalwace da’ya’yan itatuwan kaka.
13 加利亞的兒子約哈難和在田野的一切軍長來到米斯巴見基大利,
Yohanan ɗan Kareya da dukan manyan sojoji da suke a karkara suka zo wurin Gedaliya a Mizfa
14 對他說:「亞捫人的王巴利斯打發尼探雅的兒子以實瑪利來要你的命,你知道嗎?」亞希甘的兒子基大利卻不信他們的話。
suka ce masa, “Ba ka san cewa Ba’alis sarkin Ammonawa ya aiki Ishmayel ɗan Netaniya ya ɗauke ranka ba?” Amma Gedaliya ɗan Ahikam bai gaskata su ba.
15 加利亞的兒子約哈難在米斯巴私下對基大利說:「求你容我去殺尼探雅的兒子以實瑪利,必無人知道。何必讓他要你的命,使聚集到你這裏來的猶大人都分散,以致猶大剩下的人都滅亡呢?」
Sai Yohanan ɗan Kareya ya yi wa Gedaliya a Mizfa magana a asirce ya ce, “Bari in tafi in kashe Ishmayel ɗan Netaniya, ba kuwa wanda zai sani. Me zai sa ya ɗauke ranka ya watsar da dukan Yahudawan da suka taru kewaye da kai har waɗanda suka ragu na Yahuda su hallaka?”
16 亞希甘的兒子基大利對加利亞的兒子約哈難說:「你不可行這事,你所論以實瑪利的話是假的。」
Amma Gedaliya ɗan Ahikam ya ce wa Yohanan ɗan Kareya, “Kada ka yi irin wannan abu! Abin da kake faɗa game da Ishmayel ba gaskiya ba ne.”