< 耶利米書 29 >

1 先知耶利米從耶路撒冷寄信與被擄的祭司、先知,和眾民,並生存的長老,就是尼布甲尼撒從耶路撒冷擄到巴比倫去的。(
Ga abin da yake cikin wasiƙar annabi Irmiya da ya aika daga Urushalima zuwa ga sauran dattawan da suka ragu a cikin masu zaman bauta da kuma zuwa ga firistoci, annabawa da kuma dukan sauran mutanen da Nebukadnezzar ya kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon.
2 這在耶哥尼雅王和太后、太監,並猶大、耶路撒冷的首領,以及工匠、鐵匠都離了耶路撒冷以後。)
(Wannan ya faru bayan Sarki Yekoniya da mahaifiyar sarauniya, shugabannin fada da kuma dukan shugabannin Yahuda da Urushalima, gwanayen sana’a da masu sassaƙa suka tafi zaman bauta daga Urushalima.)
3 他藉沙番的兒子以利亞薩和希勒家的兒子基瑪利的手寄去。他們二人是猶大王西底家打發往巴比倫去見尼布甲尼撒王的。
Ya ba da wasiƙar ta hannun Eleyasa ɗan Shafan da Gemariya ɗan Hilkiya, waɗanda Zedekiya sarkin Yahuda ya aika wurin Sarki Nebukadnezzar a Babilon. Wasiƙar ta ce,
4 信上說:「萬軍之耶和華-以色列的上帝對一切被擄去的(就是我使他們從耶路撒冷被擄到巴比倫的人)如此說:
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ga dukan waɗanda aka kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon.
5 你們要蓋造房屋,住在其中;栽種田園,吃其中所產的;
“Ku gina gidaje ku zauna; ku dasa gonaki ku kuma ci abin da suka haifar.
6 娶妻生兒女,為你們的兒子娶妻,使你們的女兒嫁人,生兒養女。在那裏生養眾多,不致減少。
Ku yi aure ku kuma haifi’ya’ya maza da mata; ku nemi mata wa’ya’yanku maza, ku kuma ba da’ya’yanku mata ga aure, saboda su ma za su haifi’ya’ya maza da mata. Ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu.
7 我所使你們被擄到的那城,你們要為那城求平安,為那城禱告耶和華;因為那城得平安,你們也隨着得平安。
Haka kuma, ku nemi zaman salama da cin gaba a birnin da aka kai ku zaman bauta. Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda birnin, domin in ya ci gaba, ku ma za ku ci gaba.”
8 萬軍之耶和華-以色列的上帝如此說:不要被你們中間的先知和占卜的誘惑,也不要聽信自己所做的夢;
I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Kada ku bar annabawa da masu sihiri a cikinku su ruɗe ku. Kada ku saurari mafarkan da dā kuke ƙarfafa su su yi.
9 因為他們託我的名對你們說假預言,我並沒有差遣他們。這是耶和華說的。
Suna muku annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba,” in ji Ubangiji.
10 「耶和華如此說:為巴比倫所定的七十年滿了以後,我要眷顧你們,向你們成就我的恩言,使你們仍回此地。
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sa’ad da shekaru saba’in suka cika a Babilon, zan zo muku in cika alkawarin alherina don in komo da ku zuwa wannan wuri.
11 耶和華說:我知道我向你們所懷的意念是賜平安的意念,不是降災禍的意念,要叫你們末後有指望。
Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.
12 你們要呼求我,禱告我,我就應允你們。
Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku.
13 你們尋求我,若專心尋求我,就必尋見。
Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku.
14 耶和華說:我必被你們尋見,我也必使你們被擄的人歸回,將你們從各國中和我所趕你們到的各處招聚了來,又將你們帶回我使你們被擄掠離開的地方。這是耶和華說的。
Za ku same ni,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku daga bauta. Zan tattaro ku daga dukan al’ummai in sa ku inda na kore ku,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku zuwa wurin da na kwashe ku zuwa zaman bauta.”
15 「你們說:『耶和華在巴比倫為我們興起先知』;
Za ku iya ce, “Ubangiji ya tā da annabawa saboda mu a Babilon.”
16 所以耶和華論到坐大衛寶座的王和住在這城裏的一切百姓,就是未曾與你們一同被擄的弟兄,
Amma ga abin da Ubangiji yana cewa game da sarki, wanda yake zaune a kursiyin Dawuda da kuma dukan mutanen da suka ragu a wannan birni,’yan’uwanku waɗanda ba su tafi tare da ku zuwa zaman bauta ba.
17 萬軍之耶和華如此說:『看哪,我必使刀劍、饑荒、瘟疫臨到他們,使他們像極壞的無花果,壞得不可吃。
I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Zan aika da takobi, yunwa da annoba a kansu zan kuma sa su zama kamar ɓaure marar amfani da suka yi munin da ba a iya ci.
18 我必用刀劍、饑荒、瘟疫追趕他們,使他們在天下萬國拋來拋去,在我所趕他們到的各國中,令人咒詛、驚駭、嗤笑、羞辱。
Zan fafare su da takobi, yunwa da annoba zan kuma sa su zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya da kuma abin la’ana da abin bantsoro, abin dariya da abin reni, a cikin dukan al’umman da aka kore su zuwa.
19 耶和華說:這是因為他們沒有聽從我的話,就是我從早起來差遣我僕人眾先知去說的,無奈他們不聽。這是耶和華說的。
Gama ba su saurari maganata ba,” in ji Ubangiji, “maganar da na aika gare su sau da sau ta bayina annabawa. Ku kuma masu zaman bauta ba ku saurara ba,” in ji Ubangiji.
20 所以你們一切被擄去的,就是我從耶路撒冷打發到巴比倫去的,當聽耶和華的話。』」
Saboda haka, ku ji maganar Ubangiji, dukanku masu zaman bauta waɗanda na aika daga Urushalima zuwa Babilon.
21 萬軍之耶和華-以色列的上帝論到哥賴雅的兒子亞哈,並瑪西雅的兒子西底家,如此說:「他們是託我名向你們說假預言的,我必將他們交在巴比倫王尼布甲尼撒的手中;他要在你們眼前殺害他們。
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa game da Ahab ɗan Kolahiya da Zedekiya ɗan Ma’asehiya, waɗanda suke muku annabcin ƙarya da sunana. “Zan ba da su ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, zai kuwa kashe su a gaban idanunku.
22 住巴比倫一切被擄的猶大人必藉這二人賭咒說:『願耶和華使你像巴比倫王在火中燒的西底家和亞哈一樣。』
Saboda su, dukan masu zaman bauta daga Yahuda waɗanda suke a Babilon za su yi amfani da wannan la’ana cewa, ‘Ubangiji ka yi da mu kamar Zedekiya da Ahab waɗanda sarkin Babilon ya ƙone da wuta.’
23 這二人是在以色列中行了醜事,與鄰舍的妻行淫,又假託我名說我未曾吩咐他們的話。知道的是我,作見證的也是我。這是耶和華說的。」
Gama sun aikata munanan abubuwa a Isra’ila; sun yi zina da matan maƙwabtansu kuma da sunana suka yi ƙarya, waɗanda ban faɗa musu su yi ba. Na san wannan kuma ni shaida ne ga haka,” in ji Ubangiji.
24 「論到尼希蘭人示瑪雅,你當說,
Faɗa wa Shemahiya mutumin Nehelam,
25 萬軍之耶和華-以色列的上帝如此說:你曾用自己的名寄信給耶路撒冷的眾民和祭司瑪西雅的兒子西番雅,並眾祭司,說:
“Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ka aika da wasiƙu da sunanka ga dukan mutane a Urushalima, zuwa ga Zefaniya ɗan Ma’asehiya firist da kuma ga sauran firistoci. Ka ce wa Zefaniya,
26 『耶和華已經立你西番雅為祭司,代替祭司耶何耶大,使耶和華殿中有官長,好將一切狂妄自稱為先知的人用枷枷住,用鎖鎖住。
‘Ubangiji ya naɗa ka firist a wurin Yehohiyada don ka lura da gidan Ubangiji; ya kamata ka sa kowane mahaukaci wanda yake yi kamar annabi cikin turu da kuma a kangi.
27 現在亞拿突人耶利米向你們自稱為先知,你們為何沒有責備他呢?
To, me ya sa ba ka tsawata wa Irmiya daga Anatot, wanda yana ɗauka kansa annabi a cikinku ba?
28 因為他寄信給我們在巴比倫的人說:被擄的事必長久。你們要蓋造房屋,住在其中;栽種田園,吃其中所產的。』」
Ya aiko mana da saƙonsa a Babilon cewa zai ɗauki lokaci ƙwarai. Saboda haka ku gina gidaje ku zauna; ku dasa gonaki ku kuma ci abin da suka haifar.’”
29 祭司西番雅就把這信念給先知耶利米聽。
Zefaniya firist kuwa, ya karanta wasiƙar annabi Irmiya.
30 於是耶和華的話臨到耶利米說:
Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,
31 「你當寄信給一切被擄的人說:『耶和華論到尼希蘭人示瑪雅說:因為示瑪雅向你們說預言,我並沒有差遣他,他使你們倚靠謊言;
“Ka aika da wannan saƙo zuwa ga dukan masu zaman bauta cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa game da Shemahiya, mutumin Nehelam. Domin Shemahiya ya yi muku annabci, ko da yake ban aike shi ba, ya kuma sa kuka gaskata ƙarya,
32 所以耶和華如此說:我必刑罰尼希蘭人示瑪雅和他的後裔,他必無一人存留住在這民中,也不得見我所要賜與我百姓的福樂,因為他向耶和華說了叛逆的話。這是耶和華說的。』」
ga abin da Ubangiji yana cewa, tabbatacce zan hukunta Shemahiya mutumin Nehelam da zuriyarsa. Ba zai kasance da wani da ya rage a cikin wannan mutane ba, ba kuwa zai ga abubuwa alherin da zan yi wa mutanena ba, in ji Ubangiji, domin ya yi wa’azin tawaye a kaina.’”

< 耶利米書 29 >